Ana səhifə

Gyara kayanka yi hattara da


Yüklə 401 Kb.
səhifə5/12
tarix26.06.2016
ölçüsü401 Kb.
1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12

Karauniya A Cikin Salllah


Wani abun kuma da shari’a ta haramta mai kama da rashin natsuwa a cikin sallah shi ne karauniya. Wato haxa gudu da susar katara. Wannan kuwa ita ma wata matsala ce da ta zama ruwan dare ga musulmi masallata kuma tabbas abin da ke kawo haka shi ne, rashin biyar umurnin Allah sau da qafa, kamar inda ya ce:

ﭽ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭼ البقرة: ٢٣٨



Ma’ana:

Kuma ku tsayu kuna masu qanqan da kai ga Allah (2:238).

Ga kuma cewar da Allah ya yi

ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭼ المؤمنون: ١ - ٢



Ma’ana:

Haqiqa, Muminai sun samu babban rabo. Waxanda suke a cikin sallarsu masu qanqan da kai ne (23:1-2).

Babu wani aiki da ke halasta a cikin sallah, koda na taimakon sallar ne, matuqar shari’a bata aminta a yi shi ba. An tambayi Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama a kan matsayin share wurin sanya goshi domin yin sujuda a lokacin da aka sunkuyo, sai ya ce, kada ayi haka matuqar dai an riga an fara sallah. Idan kuwa har yin hakan ya zama tilas to, kar a wuce ture tsakuwa kawai (Abu Dawuda: 1/581).

A kan haka ne malamai suka tafi a kan cewa, duk wani motsi nan da can a cikin sallah, wanda ya wuce wuri, to yana vata sallah.

To, tunda kuwa har haka ne, me zai sa wasu mutane su yi biris da wannan matsala? Har a same su suna tsaye gaban Allah kuma a lokaci xaya suna duba agogo ko gyaran riga ko wasa da hanci ko su riqa waiwaye wawaiye, suna rabon ido kamar maye ya yi baqo? Ba su gudun Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya makantar da su, ko shexan ya vata masu sallah?

Shiga Gaban Liman A Cikin Sallah Da Gangan


Wani abin kuma da shari’a ta haramta shi ne, shiga a gaban liman a wajen aikata ayyukan sallah. Xan Adam akwai gaggawa. Shi ya sa Maxaukakin Sarki ya ce:

ﭽ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﭼ الإسراء: ١١

Kuma mutum ya kasance mai gaggawa (17:11)

Gaggawa a idon shari’a abu ce maras kyau. Kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Tsanaki abu ne daga Allah. Amma gaggawa aikin shexan ce (Baihaqi: 10/104). Sau da yawa idan mutum na sallah cikin jama’a zai lura da wasu mutane a hagunsa da damansa suna rigan liman wajen ruku’i ko sujuda ko kabbara, saboda tsananin gaggawa da wutar ciki. Wasu mutane ma har sallama suke rigan liman.

Kuma ga dukkan alamu mutane ba su xauki wannan xabi’a a bakin komai ba. Alhali kuwa saboda nauyinta ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi garagaxi yana mai cewa: “Waxanda ke xaukakowa da kansu kafin liman ba su gudun kada Allah Ya mayar da kanunsu irin na jakai? (Muslim: 1/320-321).

Babu shakka irin tsanakin da ake nema ga wanda ke sallah yana da yawa. Domin tun daga zuwa wurin sallar an neme shi da natsuwa da tsanaki, to ina kuma bayan ya shiga cikin ta?

A vangare xaya kuma sai ka tsinkayi wasu masallatan suna jinkiri sosai bayan liman ya yi wani aiki kafin su, su yi. A nasu tunani wannan shi ne irin tsanakin da ake nema. Ba ko haka abin yake ba.

Malaman fiqihu sun faxi yadda ake koyi da liman a cikin sallah, yadda ba za a shige makaxi da rawa ba, ba kuma za a zama kurar baya ba. Suka ce Mamu zai fara abin da zai yi ne bayan liman ya gama furta gavar qarshe ta kabbara. A lokacin ne aka halasta wa mamu motsawa. Ba kafin haka ba, ko bayan haka da nisa. Haka sahabban Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama suka kasance, suna matuqar qoqarin ganin ba su riga shi yin komai a sallah ba.

Wani sahabi da ake kira Bara’u xan Azibu Raliyallahu Anhu ya ce: “A duk lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya xaukako kansa daga ruku’i babu xaya daga cikinmu da zai karya qashin bayansa don sujuda sai in Manzon Allah ya xora goshinsa a qasa. A lokacin ne kowa zai sunkuya ya yo tasa sujudar (Muslim: 474).

Saboda irin tsananin muhimmancin da biyar liman sau da qafa a cikin ayyukan sallah gaba xaya ke da shi. Ko bayan da Manzon Allah ya samu jikinsa da nauyi saboda gabacin shekaru bai yi izni ga sahabbai da su riga shi wajen aiwatar da kome a cikin sallah ba. Kai! Har ma jan kunne ya yi masu a kan haka, da cewa: “Ina maku kashedi kada ganin jikina ya fara nauyi, ya sa ku riga ni yin ruku’i ko sujada” (Baihaqi: 2/93).

Shi kuwa liman, shari’ah ta xora masa yin kabbarorinsa na sallah kamar yadda sunnah ta tanada. Abu Hurairata Raliyallahu Anhu ya riwaito a wani hadisi cewa: “Duk lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tashi yin sallah, ya kan yi kabbarar harama ne bayan ya gama tsayuwa cik, ko duqawa. Idan kuma zai tafi sujuda yakan sunkuya ne tare da furta kabbara. Haka zai yi wajen xaukakowa da kansa. Haka kuma zai yi idan zai tafi sujuda ta biyu, da kuma xaukakowa daga gare ta. Haka zai yi ta yi har ya qare sallar. Kuma yakan yi kabbara bayan qare tahiya ta farko don miqewa tsaye (Bukhari, 785).

Wato a taqaice liman zai yi kabbara ne tare da aiki a cikin mafi yawan ayyukan sallah su kuma mamu suna biye da shi kamar yadda qa’ida ta tanada. Kuma ta haka ne kawai sallar jama’a zata karva sunanta.


Zuwa Masallaci Da Warin Albasa Ko Tafarnuwa

Wani abu kuma da shari’a ta haramta shi ne, zuwa masallaci bayan mutum ya qare kalaci da albasa ko tafarnuwa. Wanda hakan za ta sa warin jikinsa ya dami mutane. Alhali kuwa shari’a ta yi umurni da tabbatar da cikakkiyar tsafta ga musulmi kafin ya tinkari masallaci, kamar yadda Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce:

ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘﭼ الأعراف: ٣١

Ma’ana:

Ya ku xiyan Adamu! Ku riqi qawarku a wurin ko wane masallaci (7:31).

Kuma Jabir Raliyallahu Anhu na cewa: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya ci tafarnuwa ko albasa kada ya matso mu, kada kuma ya zo masallacinmu. Ya tsayawarsa a gida (Bukhari: 2/339).

A wata riwaya ta Muslimu kuma ya ce: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce:Duk wanda ya ci albasa ko tafarnuwa ko Kurrasi kada ya matso kusa da masallacinmu. Domin kuwa mala’iku na qyamar duk abin da ‘yan Adam ke qyama (Muslim: 1/395).

Watarana kuma Halifa Umar xan khaxxabi ya yi wa mutane huxubar juma’a, har yake cewa:Ya ku mutane! Haqiqa kukan ci wasu abubuwa biyu, da nake zaton tsirrai ne qazantacci, wato albasa da tafarnuwa. Na lura a duk lokacin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ji mutum na warin xaya daga cikinsu a cikin masallaci yakan umurce shi da ya fita waje, ya koma Baqi’a. Saboda haka daga yau duk wanda ke son ya ci waxannan abubuwam to ya dafa su sosai har warinsu ya vace (Muslimu: 1/396).

Wannan hukunci a wannan zamani namu ya haxa har da mutanen da ke da xabi’ar wucewa masallaci daga wurin ayyukansu. Musamman zaka tarar hamutansu da safar da ke qafarsu suna aman wani irin wari. To, mafi munin su ma, ga tayar da hankali da takura masallata su ne mashaya taba sigani, wadda ma ita a karan kanta haram ce. Su kuma sha ta, sannan su nufato masallaci suna warinta, suna xaga hankalin mala’iku da mutane.


ZINA

Kiyaye alfarmar yaxuwar xan Adamu a bayan qasa ta hanyar samar da zuri’a mai nagartaccen asali, na xaya daga cikin manufofin shari’ar musulunci. Saboda haka ne Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta zina, da duk wani abu da ke iya kai mutum ga faxawa cikinta. Ya ce:

ﭽ ﮊ ﮋ ﮌﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﭼ الإسراء: ٣٢

Ma’ana:

Kuma kada ku (ko) kusanci zina. Haqiqa, ta kasance alfasha ce, kuma ta munana ga zama hanya (17:32).

Da wannan aya ne, da ire- irenta shari’ar musulunci ta haramta tare da rufe ko wace irin kafa wadda ke iya zama sanadin aikata zina. Shari’ar ta kuwa yi haka ne ta hanyar kwaxaitarwa ga sa hijabi da kau da kai daga xiyan jinsin da bai halatta ba. Da kuma haramta kaxaita tsakanin jinsunan biyu, da sauransu.

Saboda daqushe kaifin wannan mummunar xabi’a ne, da hana ta ci gaba da yaxuwa shari’a ta tanadi hukuncin kisa ga mutumin da ya aikata ta alhali yana da aure. Don ya xanxani azaba sakamakon abin da ya aikata, kuma gaba xayan jikinsa ya ji xacin abun kamar yadda annashawar da ake samu a sakamakon saduwa, ta game shi irin gamewar da jini ke yi ga jiki. Shi kuwa wanda bai yi aure ba, shari’ar ta yanke masa hukuncin bulala xari (100), a bainar jama’a ba tare da rufa- rufa ba. Bayan haka kuma za’a yi masa xaurin shekara xaya ko ya bar garinsu na tsawon wannan lokaci.

Wannan a duniya kenan. Idan kuma aka zo barzahu; cikin qabari, mazinata na da wata uquba ta quntata masu makwanci, da gasa jikinsu da wata wuta da za a hura a qarqashinsu bayan an yi ko sama ko qasa da likkafaninsu. Haka za a yi ta dafa su, suna narkewa suna kumfa gwargwadon zafin wutar, har sai kumfan ya yi kamar zai yi ambaliya ya tunbutso zuwa waje, sai kuma wutar ta faxa. A kuma sake juyawa. Haka za a yi ta jujjuya su har ranar tashin mutane zuwa farfajiyar alqiyama.

To babbar matsala ma duk ba ta fi mutum ya mayar da zina sana’a ba. Ba shi da aiki sai yin ta har tsufa ya kama shi, mutuwa ta fara barbaxa masa gishiri, amma ya kasa tuba, ya bari. Alhali kuma Allah Ya ba shi ikon yin haka. Matsalar ita ce, da zarar mutuwa ta rutsa da shi a cikin irin wannan hali, to, ba shi fa ba rahama da gafarar Allah. Saboda Abu Hurairata ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce:Akwai wasu mutane uku da Allah ba zai haxa baki da su ba ranar qiyama, ko kallonsu kuma ba zai yi ba, balle, ko sanyi su ji. Matsananciyar azaba ita ce sakamakon su. Na farkon su shi ne: Tsoho Mazinaci. Na biyu: Maqaryacin shugaba. Na uku: Talaka mai girman kai (Muslim: 1/102-103).

Wannan ke nan, Sannan kuma wani mugun abun kama shi ne, a idon shari’ar musulunci, mafi sharri da rashin albarkar kuxi su ne waxanda mace ta samu ta zina. Allah Subhanahu Wa Ta’ala ba zai karvi addu’o’in su ba a lokacin da yake buxe qofofin sama don karvar addu’o’in bayinsa a tsakkiyar dare. Wannan garavasar ba da karuwai ba a ciki, ba kuma da kwartayensu ba.

Talauci da fatara da wasu karuwai ke kafa hujja da shi, a matsayin dalilinsu na wannan mugunyar sana’a ba hujja ba ne a wurin Maiduka. Balle hakan ya zama wani lasisi na yi wa wata dokar Allah karan tsaye. Bari ma batun ta Zina. Magabata cewa suka yi: “Da mace marar miji ta shayar da wani jinjiri nono, gara an soke ta da wuqa”. To, ina ga ta kasa al’aurarta a faifai a kasuwa?

Amma kuma tattare da haka, sai ga shi, abin takaici, abin kuka, abin kuma tayar da tuta da sa riga da koda babu cuna, an wayi gari shexan da ‘yan barandarsa sun buxe gaba xayan qofofin fitsara da batsa da rashin arziqi a faxin duniya. Wanda hakan ta sawwaqe wa mutane aikata ko wane irin savo, duk inda ka jefa idonka mata ne ke yawo kamar tsirara akan tituna. Su kuwa maza sai zuba idonsu suke yi akansu. Inna Lillahi Wa Inna Ilaihi Raji’una.

A yau ne zaka ga cuxanya tsakanin maza da mata bata zama abin qyama ba. Mujallun batsa da fayafan Talabijin na tsiraici kuwa babu kama hannun yaro. Hakan kuwa ta haxa har da masu sha’awar ziyartar qasashen qetare. Saboda tsananin kai wa matuqa ma har kasuwanni ake buxawa a yau, da ba su da wata safara sai karuwanci.

Irin waxannan abubuwa ne suka haifar da hauhawar keta mutunci da alfarmar ‘yan Adamtaka ta hanyar yawaita haihuwar shegu da zubar da cikkunan banza.

Ya Ubangiji! Muna roqonka ka zubo rahamarka gare mu, ka kare mu daga faxawa cikin miyagun xabi’u. Muna roqon ka tsarkake zukatanmu da al’aurunmu, ka yi katangar qarfe tsakaninmu da haramiyya baki xaya.


1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət