Ana səhifə

Gyara kayanka yi hattara da


Yüklə 401 Kb.
səhifə3/12
tarix26.06.2016
ölçüsü401 Kb.
1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12

Imani Da Taurari


Zaidu xan khalidu al-juhani ya riwaito cewa: “Wata rana a Hudabiyya, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba mu sallar safe, bayan an xauke ruwan sama, da aka kwana ana yi. Da ya qare sallar ya juyo ya fuskance mu. Sai ya ce: ko kun ji abin da Unbangijinku ke faxa? Muka ce: Allah da Manzonsa kaxai ke da sani. Daga nan sai ya ce:Allah Ya ce ne: Wayewar garin nan wani bawa nawa ya yi imani da ni, wani kuma ya kafirce mani. Duk wanda ya ce: “Ruwan nan Allah ne Ya shayar da mu a cikin ikonsa da rahamarsa”. To shi ne wanda ya yi imani da ni, ya kafirce ma taurari. Shi kuwa wanda ya kafirce mani ya kuma yi imani da taurari shi ne wanda ya ce: “Tauraruwa kaza da kaza ne suka shayar da mu wannan ruwa (Buhari: 2/333).

Haka kuma duk wanda ya karanta jadawalin abubuwan da za su faru na gaibi wanda ake kirdado dabra da kaiwa da komowar taurari, a cikin wata jarida ko mujalla, ya kuma yi imani da abin to, babu shakka shi ma mushriki ne. Savanin wanda karantawa kawai ya yi don nishaxi. Shi mai laifi ne kawai. Dalili kuwa shi ne, ba abu ne yardadde a shari’a ba, mutum ya nemi samun wani nishaxi ta hanyar karanta wasu abubuwa da suka qunshi Shirka. Domin shexan na iya amfani da wannan dama ya tuqa masa tuwon tulu, a wayi gari ya faxa cikin mushrikai.

Abu na gaba kuma a layin nau’o’an Shirka shi ne:

Imani da Tasirin wani Abu


Wani nau’i na Shirka kuma shi ne imani da cewa, wani abu na da wani tasiri na amfani zuwa ga mutum. Alhali Allah Mahalicci bai tanadi haka ba.

Wasu mutane sun yi imani da cewa, abubuwa irin su: Karho, Laya, Guru da Dagumma na da wani amfani da zasu iya yi masu. Wannan kuwa wata tsohuwar al’ada ce da suka gada tun kaka da kakanni. Wasu kuwa yanzu ne da rana tsaka bokaye da malamansu na tsibbu ke xora su a kan wannan aqida. A sakamakon haka sai ka tarar da su rataye da waxannan abubuwa ga wuyansu ko sun xaura ga kunkuransu, ko sanye ga kunnuwansu ko ga damatsansu ko na’ya’yansu. Imanin da suka yi shi ne abubuwan na taimakonsu ga kuranye masu hatsarin mayu da masu kandun baka.

Wasu kuma zaka ga rataya irin waxannan abubuwa suke yiga motocinsu ko a bangayen gidajensu. Wasu kuma wasu zobba zaka gani ga yatsunsu, waxanda aka saka wa wasu duwatsu na musamman waxanda suka yi imani cewa, suna ba su kariya ne daga wasu matsaloli. Alhali kuwa a haqiqanin gaskiya, waxannan abubuwa na kawai nisantar da waxanda suka yi imani da su ne, daga kasancewa masu imani da Allah Subhanahu Wa Ta’ala, masu dogara gare shi. A qarshe kuma ba abin da za su qaru da shi, illa rauni da hasara da tavewa. Domin yin hakan neman waraka ne ta hanyoyi haramtacci.

Eh! Ko shakka babu hanyoyi ne haramtacci. Domin a cikinsu akwai Shirka, wadda ke tabbata ta hanyar neman agaji daga shexanu ko wasu aljannu. Ko ka taras a cikin su da surkulle, na wasu zane-zane da rubuce- rubuce. A wasu lokuta kuma zaka ga an rubuta wasu ayoyin na Alqur’ani, an sassaqa su da wasu kalmomi na Shirka. Wani lokaci ma akan yi waxannan rubuce-rubuce da zane- zane ne, da qazamtattun abubuwa kamar jinin haila da makamantan sa.

Ko shakka babu, xaura irin waxannan abubuwa da amfani da su a jikin mutum ta ko wace hanya haramun ne. Saboda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya xaura laya ya yi Shirka (Ahmad: 4/156).

Qarin bayani game da wannan hadisi shi ne: Idan wanda ya xaura layar ga misali ya qudurce cewa, tana da wani tasiri na kai tsaye, a cikin samar da wani amfani ko wata cuta wadda Allah bai nufa ba, to, ya aikata babbar Shirka. A yayin da wanda kuma ya xaura layar yana mai qudurce cewa, tana zama sanadi ne kawai na amfanin ko cutar amma tantagaryar aikin na hannun Allah. To, irin wannan ya aikata qaramar Shirka.

Wani nau’i na Shirka kuma shi ne:

RIYA


Yana daga cikin qa’idojin da shari’a ta gindaya, ga ko wane kyakkyawan aiki, kafin ya zama karvavve a wurin Allah, dole ne ya kasance an yi shi ba don a nuna wa duniya ba. Kuma dole ne ya kasance daidai da yadda sunnah ta tanada a yi shi.

A kan haka, duk wanda ya aikata wani aiki na ibada kamar Sallah don ya nuna wa mutane cewa yana sallah, to ya yi Shirka. Kuma Allah ba zai karvi aikinsa ba.

Allah Subhanahu Wa Ta’ala ne cewa a kan haka:

ﭽ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﭼ النساء: ١٤٢



Ma’ana:

Haqiqa, munafukai suna yaudarar Allah (a zatonsu) alhali kuwa Shi ke yaudarar su ga haqiqani. Kuma idan sun tashi zuwa sallah, sai su tashi a raggwance. Suna nuna wa mutane (wai suna sallah!), kuma ba su ambatar Allah sai kaxan (4:142).

A idon shariar musulunci duk wanda ya yi wani aiki na ibada don labari ya kai ga kunnuwan mutane, ya faxa tarkon Shirka, kuma sakamakonsa shi ne Allah zai taqaita ladar aikin nasa a kan haka. Kamar yadda xan Abbas Raliyallahu Anhu ya riwaito a wani hadisi cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Duk wanda ya aikata wani abu don mutane su ji ko su gani Allah zai sa su jin kuma su gani (Shi ke nan. Ba lada). (Muslim: 4/2289) .

Haka kuma yau da mutum zai yi irin wannan aiki na ibada amma bai yi shi don mutane su gani ko so ji ba kawai. A’a har ma don Allah Ya ji kuma Ya gani, To, shi ma irin wannan bai tsira ba. Kenan ya yi aikin don Allah da mutane. Aikin nasa kuwa ya zama ba karvavve ba a wurin Allah. Kamar yadda wani hadisi qudusi yake cewa, Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce: “Na wadaci kaina, ta yadda ba na buqatar yin tarayya da kowa a cikin komai. Saboda haka duk wanda ya aikata wani aiki, ya ce ya yi shi don mutane da kuma Ni, to na bar wa wanda ya haxa Ni da shi aikin. Ni ba na so (Muslim: 2485).

Tana yiwuwa kuma, wani lokaci, mutum ya fara wani aiki, ba ya nufin kowa da shi sai Allah. Amma kuma kafin ya qare sai shexan ya kaxa masa tambari sai ya ji yana buqatar a gani. To, idan ya qi sauraren wannan huxuba ta shexan Allah zai karvi aikin nasa. Amma idan ya saurare shi har ya yi masa kari, to, mafi yawan malamai sun tafi a kan cewa Allah Subhanahu Wa Ta’ala ba zai karvi aikin nasa ba.

Nau’i na gaba kuma daga cikin waxannan nau’o’i na Shirka shi ne;



CAMFI

Camfi wata tsohuwar al’ada ce ta maguzanci, da akan yi amfani da ita don gano abin da zai faru nan gaba na alheri ko sharri, ko kuma don yanke hukuncin dalilin faruwar wani abu da mafarinsa. Allah Subhanahu Wa Ta’ala na cewa:

ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞﭟ ﭩﭼ الأعراف: ١٣١

Ma’ana:

Sai idan wani abu mai kyau ya je masu, sai su ce: “Wannan namu ne”. Kuma idan masifa ta same su sai su ce, shu’umcin Musa ne da waxanda ke tare da shi (7:131).

Kafin zuwan musulunci idan Balarabe ya shirya tafiya sai ya kama wani xan tsuntsu sannan ya sake shi a sarari har tsuntsun ya yi tafiyar sa. Idan ya fiffika ta dama, sai ya ce, akwai sa’a ga wannan tafiya. Idan kuwa har ya fiffika ta hagu, to, shikenan, ba batun tafiya domin babu sa’a a cikinta.

Da bayyanar musulunci, sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yanke wa irin wannan camfi hukunci da cewa: “Camfi Shirka ne” (Ahmad: 1/389).

Irin wannan haramtacciyar aqida ta camfi wadda ke takin saqa da aqidar Tauhidi ta haxa da, qudure cewa akwai waxansu lokuta ko ranakku ko watanni da makamantan su da babu sa’a a cikinsu faufau. Kamar yadda wasu suka camfa watan Rajab da cewa watan rashin sa’a ne. Saboda haka ba sa yin aure a cikinsa. Wasu kuma sun camfa ranar larabar qarshen ko wane wata da cewa ita ma rana ce ta rashin sa’a, da saukar miyagun qaddarori. Wasu kuma sun camfa wasu sunaye da wasu lambobi, kamar 13 da wasu mutane suka camfa da cewa ba sa’a a tare da ita.

Haka kuma camfa musakai da wasu mutane suka yi da cewa suna tare da rashin sa’a. Shi ma wannan haramun ne. Akwai mutanen da yau da zasu nufi kasuwa su don su buxe shagunansu. Da zarar sun ci karo da mai- ido- xaya a hanya sai su dawo gida. Wai, ba sa’a a ranar kenan. Duk waxannan camfe-camfe haramun ne, kuma nau’i ne na Shirka. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, ba shi ba mai yin su. Kamar yadda Imrana xan Husaini ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce:Duk wanda ke amfani da tsuntsu don neman sa’a, ko yake da wani mai yi masa haka, ko ya ke gaya masa abin da gobe zata haifar, ko yake haka da kansa, ba ya tare da mu”. Mai riwayar ya kuma ce: Kuma kamar na ji ya ce haka: “Ko wanda ke tsafi, ko yake da wani mai yi masa”. (Tabarani: 18/162).

Kaffarar da wanda ya yi irin wannan aika-aika zai yi na cikin hadisin da Abdulahi xan Ausu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya fasa yin wani abu saboda wani camfi, ya yi Shirka. Sai sahabbai suka tambaye shi, mene ne kaffararsa? Sai ya ce: kaffararsa ita ce, ya ce: Ya Allah! babu wani alheri sai alherinka, babu kuma wani sharri sai wanda ka hukunta, kuma babu wani Ubangiji sai kai kaxai. (Ahmad: 2/220).

To amma kuma a haqiqa, yin imani cewa, wani abu na iya zama alheri ko sharri wani abu ne da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya halitta cikin jinin xan Adamu, kai tsaye ko kaikaice. Amma kuma babban maganinsa shi ne dogara ga Allah. Kamar yadda xan Ma’sudu Raliyallahu Anhu ya ce: “Babu wanda ba ya irin wancan hasashe daga cikinmu a wasu lokuta. Amma da zarar mun mayar da kome ga Allah sai mu sami sukuni (Abu Dawud: 3910).

Nau’i na qarshe daga cikin waxannan nau’o’i na Shirka shi ne:

1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət