Ana səhifə

Gyara kayanka yi hattara da


Yüklə 401 Kb.
səhifə6/12
tarix26.06.2016
ölçüsü401 Kb.
1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12

LIWAXI


Wani abu kuma da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta amma mutane suka yi biris da shi, shi ne liwaxi. Wato saduwar namiji da xan uwansa namiji. Irin wannan baqar xabi’a ce dai ta haxa Allah Subhanahu Wa Ta’ala da mutanen annabi Luxu Alaihis Salamu har Sarkin Ya labarta wa duniya abin da ya faru, inda ya ce:

ﭽ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰ ﭼ العنكبوت: ٢٨ - ٢٩



Ma’ana:

Kuma ka faxi labarin Luxu a lokacin da, ya ce wa mutanensa: “Haqiqa ku, kuna je ma alfasha wadda ba wanda ya riga ku yin ta a cikin talikai?” “Haqiqa ku, kuna je wa maza, kuma ku yi fashin hanya, kuma ku aikata abin da ba shi da kyau a wuraren zaman ku? Ba wata amsar da mutanensa suka bayar sai dai suka ce: “Ka zo mana da azabar Allah in har da gaske ka ke yi?” (29:28-28).

Saboda qazantar wannan xabi’a ta liwaxi da kasancewar ta wani nau’i na dabbantaka ne, Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya saukar da wasu azabobi guda huxu, da bai tava saukarwa a game ba a kan waxannan mutane na annabi Luxu Alaihis Salamu. Da farko sai da Allah Ya makantar da su. Sannan ya yi wa garinsu juyin masa. Ya kuma bi shi da ruwan duwatsun wuta da balbalin azaba, da tsawa mai tsanani.

A musulunci kuma duk wanda aka kama da aikata laifin liwaxi hukuncinsa shi ne kisa da takobi. Wannan shi ne ra’ayin da ya fi amo a tsakanin malamai. Shi ne kuma hukuncin da zai hau kan wanda aka yi liwaxin da shi matuqar ba tilasta shi aka yi ba. Xan Abbas ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda kuka kama yana aikata irin aikin mutanen Luxu, to ku kashe shi, ku kuma kashe wanda yake yi da shi (Ahmad: 1/300).

Ko shakka babu miyagun ciwarwata masu wuyar magani da suka zama ruwan dare a wannan zamani namu musamman “qanjamau” sun yaxu ne sanadiyyar wannan yamutsa hazo a duniyar halittu. Kuma wannan na daxa fitowa fili da gwanintar shari’a da ta zartar da hukuncin kisa ga wanda ya qazanta kansa da wannan bala’i don kada ya yaxa shi.

QIYO


(Hana Wa Miji Kai)

Qiyo; hana wa miji kai don biyan buqatar aure, sava wa Allah ne. Amma kuma tattare da sanin haka, wasu mata sun sa qafa sun take haramcin.

Abu Hurairata Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “idan mutum ya gayyaci matarsa zuwa ga shimfixarsa ta qi, ya kwana cikin hushi da ita, Allah zai ci gaba da la’antar ta har a wayi gari (Bukhari: 6/314).

Duk da irin wannan mummunan tanadi da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi wa mace mai yi wa mijinta qiyo, wasu matan kan qaurace wa mazajensu, idan wata ‘yar tankiya ta shiga tsakaninsu. Wataqila har mazan sun xan yi masu wani horo koda na so-kanki ne. Alhali kuwa irin wannan mataki, kan iya haifar da aukawar miji cikin wata babbar haramiya ko qarshe ma ya yi tunanin ya auri wata.

Don gudun faruwar xaya daga cikin waxannan abubuwa ko dukansu wajibi ne mace ta yi gaggawar karva gayyatar mijinta idan ya nemi wannan buqata, a matsayin biyayya ga umurnin Allah da Manzonsa. Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Idan mutum ya gayyaci matarsa zuwa ga shimfixarsa, to ta karva masa, koda kuwa tana kan raqumi ne (wato komai aikin da take yi) (Majma’uz Zawaidi: 2/181).

Shi kuwa miji wajibi ne ya yi matuqar kula da matarsa, ta hanyar lelenta, musamman a lokacin da take fama da wata rashin lafiya ko take da juna biyu. Haka zai qara yauqi da danqon soyayyar da ke tsakaninsu, ta gane lalle yana ji da ita. Sadoba haka ba zata rena shi ba, balle ya ce ta yi, ta ce ta qi.


NEMAN SAKI

Wata haramtacciyar xabi’a kuma a shari’a ita ce, mace ta nemi miji ya sake ta, ba da wani qwaqqwaran dalili ba. Kamar idan mijin ya hana mata wasu kuxi da ta nema daga gare shi.

Wasu matan sukan tayar da irin wannan fitina ne ta neman saki, bayan wasu vata- gari daga cikin danginsu sun yi masu fanfo, ko wasu miyagun maqwauta sun harzuqa su a kan lalle su qalubalanci mazan nasu. Ai dole ne idan masara ta ji wuta ta yi daxo. A wasu lokutan ma har naqalta masu ake yi abin da za su faxa sukan yi; ki ce masa; “In ka haihu ka sake ni” Da zarar hakan ta faru, idan an yi rashin sa’a da wa’adin auren ya qare sai ka ji an raba gari, Gida ya watse, yara su rinqa ragaita rariya- rariya. Wanda kuma a mafi yawan lokuta ma’aurata kan sami kansu cikin nadama idan haka ta faru bayan bakin alqalami ya riga ya bushe. Saboda haka ne shari’a ta haramta irin wannan aiki.

Saubanu Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Duk matar da ta nemi saki daga mijinta ba tare da wani qwaqqwaran dalili ba, ko qanshin aljanna kam ba zata ji ba. (Ahmad: 5/277).

Haka kuma Uqbatu xan Amiru Raliyallahu Anhu ya riwaito Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa; “Duk matar da ke neman mijinta ya sake ta da wadda har abada bata gode wa miji, munafukai ne (Xabarani: 17/339).

Amma idan akwai wani qwaqqwaran dalili kamar mijin ya kasance baya sallah ko yana shan giya ko miyagun qwayoyi ko yana tilasta mata aikata waxansu abubuwa na haramun. Ko yana musguna mata da zaluntar ta, ta hanyar hana mata wasu haqqoqin nata na shariah. Kuma ya qi jin shawarwarin, balle ya sassafta mata. A irin wannan hali babu laifi ga matar don ta nemi a sake ta. Don ta tsira da mutuncinta da addininta.



ZIHARI

Zihari wata xabi’a ce da Larabawa kan yi tun zamanin Jahiliyyarsu ta farko, don su cutar da matansu. Da zarar xayansu ya gaji da mace, sai ya dube ta ya ce “Kin haramta gare ni yadda gadon bayan mahaifiyata ya haramta gare ni”. Ko ya ce mata: “Kin haramta gare ni yadda ‘yar uwata ta haramta gare ni”.

Wannan mugunyar al’ada na xaya daga cikin al’adun jahiliyyar Larabawa da suka wanzu a cikin wannan al’umma har ila yaumina haza.

Shari’ah ta haramta wannan al’ada da duk wani abu mai kama da ita, da ke cutar da mata ta ko wane hali. Allah Subhanahu Wa Ta’ala na cewa a cikin Alqur’ani:

ﭽ ﭥ ﭦ ﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭬﭭ ﭮ ﭯ ﭰ ﭱ ﭲﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﭼ المجادلة: ٢

Ma’ana:

Waxanda ke yin Zihari daga cikinsu game da matansu, su matan nan ba uwayensu ba ne, uwayensu kam su ne waxanda suka haife su. Suna faxar abin qyama na magana da qarya. Kuma haqiqa Allah Mai yafewa ne, Mai gafara (58:27).

Hukuncin duk wanda ya aikata irin wannan laifi a matsayin kaffara, a shari’ar musulunci, shi ne irin kaffarar da wanda ya kashe wani a kan kuskure, ko ya taki matarsa a cikin watan azumi da rana zai yi. Kuma haramun ne ya kusanci matar sai bayan ya yi kaffara Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa:

ﭽ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍﮎ ﮏ ﮐ ﮑﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭﮮ ﮯ ﮰ ﮱﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﭼ المجادلة: ٣ - ٤



Ma’ana:

Waxanda ke yin Zihari game da matansu, sa’annan su koma wa abin da suka faxa, to akwai ‘yanta wuya a gabanin su shafi juna. Wannan ana yi maku wa’azi da shi. Kuma Allah mai qididdigewa ne ga abin da kuke aikatawa. To, wanda bai samu (Abin da zai ‘yanta wuyan da shi) ba, sai (ya yi) azumin wata biyu jere a gabanin su shafi juna, sa’annan wanda bai sami ikon yi ba, to, sai ya ciyar da miskinai sittin. Wannan domin ku yi imani da Allah da Manzonsa. Kuma waxannan hukunce-hukunce iyakokin Allah ne. Kuma kafirai suna da azaba mai raxaxi (58:3-4).


1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət