Ana səhifə

Gyara kayanka yi hattara da


Yüklə 401 Kb.
səhifə2/12
tarix26.06.2016
ölçüsü401 Kb.
1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12

Yanka Don Wanin Allah


Xaya daga cikin yanke – yanken da mushrikai kan yi tun zamanin Jahiliyyar Larabawa, wanda kuma ya zama wata al’ada da ta watsu a cikin duniya shi ne yanka wata dabba don aljannu su sha jini.

Mushrikan Larabawa kan yi wannan al’ada ne, kamar idan xayan su ya gina ko ya sayi gida, ko ya haqa wata rijiya. Sai a sami wata dabba a yanka a bai wa aljannun da ake da imanin suna cikin gidan ko rijiyar jini a matsayin cin hanci, don su bar abin. Wanda idan ba haka aka yi ba, a tunaninsu, mai gidan ko rijiyar zai haxu da wata cuta.

Irin wannan Shirka ta haxa nau’in haramiya biyu: Na farko, Sadaukar da wani abu da sunan bauta ga wanin Allah. Na biyu kuma, yanka abin da za a yi ba da sunan Allah ba.

Da zuwan addinin Musulunci sai wannan al’ada ta haramta. Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya musanya wa musulmi ita da bauta masa inda Ya ce:

ﭽ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﭼ الكوثر: ٢

Ma’ana:

Saboda haka, ka yi sallah ga Ubangijika, ka kuma yi yanka (don Shi) (108:2).

Bayan wannan kuma sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya qara daddale wannan haramci tare da qara fitowa da shi fili, ya ce: “Allah Ya la’anci duk wanda ya yanka wani abu don wanin Allah (Muslim: 1978).

Nau’in Shirka na gaba kuma shi ne:


Halsta Abin Da Allah Ya Haramta


Haka nan kuma yin imani da cewa akwai wani mahaluki a bayan qasa, wanda ke da lasisin halasta wani abu da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta, Shirka ne.

Irin wannan Shirka ta haxa har da kai qara a kotunan da ba na musulunci ba. Musamman idan haka ta kasance tare da yin imani da cewa yin haka halas ne. Kuma an tafi can ne bisa zavin kai; babu wanda ya tilasta hakan.

Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ambaci irin wannan Shirka a cikin Alqur’ani, a matsayin Babbar Shirka, in da Ya ce:

ﭽ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜ ﯝ ﯞ ﭼ التوبة: ٣١



Ma’ana:

Sun riqi malamansu (Yahudawa) da ruhubanawansu (Nasara) Ubannangiji, baicin Allah (Saboda Suna yi masu xa’a a cikin abubuwan da suka halasta masu ko haramta masu, bisa ra’ayin kansu; ba umunin Allah ba) (9:31).

A lokacin da Adiyyu xan Hatimu ya ji Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya karanta wannan aya sai ya ce: Ya Manzon Allah! Ai ba bauta masu suke yi ba. “Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya karva masa da cewa: “Na ji. Amma ai suna halasta masu abubuwan da Allah Ya haramta, su kuma haramta masu abubuwan da Ya halasta, su kuma amince da haka ko? To, ai wannan ita ce bautar da suke yi masu. (Baihaqi: 10/116).

Bayan wannan ma, irin wannan tavargaza, na daga cikin siffofin mushrikai, kamar yadda Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya bayyana a wata aya da ke cewa:

ﭽ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﭼ التوبة: ٢٩

Ma’ana:

Ba su haramta abin da Allah da Manzonsa ya haramta, kuma ba su bin addinin gaskiya (9:29).

A wata ayar kuma Ya ce:

ﭽ ﮜ ﮝ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ ﮱ ﭼ يونس: ٥٩



Ma’ana:

Ka ce, “Shin, kun ga abin da Allah Ya saukar saboda ku na arziki, sai kuka halalta wasu kuka haramta wasu?”. “Ka ce, “Shin, Allah ne Ya yi maku izini, ko Allan ne kuke wa qazafi? (10:59).

Nau’in Shirka na gaba kuma shi ne:

Sihiri, Bayar Da Sa’a Da Faxin Gaibi


Sihiri wani na’ui ne na kafirci, kuma Shirka ne. Yana kuma daga cikin zunubai guda bakwai da ke durmuyar da mutun a cikin wuta. Kuma babu wani amfani da ake samu a cikinsa. Hasali ma ba abin da yake haifarwa ga wanda aka yi wa shi illa hasara da ci baya.

Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya gaya mana matsayin masu koyon sa. Ya ce:

ﭽ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﭼ البقرة: ١٠٢

Ma’ana:

Kuma suna neman ilimin abin da yake cutar da su, kuma ba ya amfaninsu (2:102).

A wata ayar kuma Ya ce:

ﭽ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﭼ طه: ٦٩



Ma’ana:

Kuma masihirci ba ya cin nasara a duk inda ya je (20:69).

A wata ayar kuma Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya tabbatar da cewa duk wanda ke sihiri da tsafi kafiri ne. Ya ce:

ﭽ ﭙ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣ ﭤ ﭥ ﭦ ﭧ ﭨﭩ ﭪ ﭫ ﭬ ﭭ ﭮ ﭯ ﭰ ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭼ البقرة: ١٠٢



Ma’ana:

Kuma sulaimanu bai yi kafirci ba, kuma shaixanun su ne suka yi kafirci, (Saboda) suna karantar da mutane sihiri da abin da aka saukar da shi a kan mala’iku biyu a Babila; Haruta da Maruta. Kuma babu wanda suka sanar sai sun ce: “Mu fa fitina ne, saboda haka kada ka kafirta”. (2:102).

Bayan wannan kuma hukuncin mai sihiri a duniya shi ne kisa, kuma duk abin da ya samu daga wannan sana’a tasa qazantatta, shi ma haram ne.

Amma kuma duk da irin wannan mugun matsayi na mai sihiri, sai ka taras da wasu musulmi, saboda kantar jahilci da tsatsarsa, da raunin imani da ke tattare da su, suna ziyarar masu wannan mugunyar sana’a don neman su taimake su, su xauki fansa a kan wani ko kuma don su karya wani makaru da wani ya yi masu. Alhali kuwa kamata ya yi su fuskanci Allah Subhanahu Wa Ta’ala su nemi taimakonsa a kan waxannan al’amurra da makamantansu. Ta hanyar karanta wasu surori na Alqur’ani kamar Falaqi da Nasi.

Haka su ma masu bayar da sa’a, ta hanyar bayar da labarin abin da zai faru. Su ma kafirai ne. Domin suna raya cewa sun san gaibi. Alhali kuwa babu wanda ya san gaibi sai Allah.

Mafi yawan masu irin wannan sana’a sukan yi amfani ne da qarancin ilimi da wayewar wasu mutane, su karve masu kuxaxe. Sai ka ga suna ‘yan zane –zane ga qasa, suna jefa xiyan wuri suna karanta wasu surkulle. Wasu kuma a qasashen Turai suna wasa da kofunan Gahawa da wasu ‘yan kwalayen qarau da madubbai, da makamantansu. Amma kuma a mafi yawan lokuta, sau xaya ne sukan yi nasara daga cikin sihiri xari da suke yi, sauran xari ba xayan kuma, sun sha kunya a cikinsu. Duk da haka, irin waxancan jahilan mutane sai su mayar da hankali a kan sihirin nan guda da qaddara ta riga fata a cikin sa, su manta da Tasa’in da tarar.

Take Sai ka ga suna ta yin tururuwa a garaken masihirtan, suna neman su gaya masu ko akwai sa’a a cikin wani aure ko kasuwanci da suke shirin qullawa. Ko su taimaka masu su gane wani abu nasu da ya vata da wasu abubuwa masu kama da wannan.

A qa’idar shari’ar musulunci kuwa gaskata mai sihiri kafirci ne. Kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya je wurin wani boka ko mai sihiri, ya kuma gaskata shi, to, ya kafirce wa abin da aka saukar ga Muhammadu Sallallahu Alaihi Wasallama (Ahmad: 2/429).

Idan kuwa har zuwa wurinsu kawai mutun ya yi, ba don ya yi imani da abin da suke yi ba, ba kuma don ya yi amanna cewa sun san gaibi ba. A’a ya dai tafi ne don tantancewa da ganarwa idonsa, ko don wani abu mai kama da wannan, to bai zama kafiri ba. Amma dai ya yi babbar hasara. Don Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Duk wanda ya je wurin wani mai sihiri ya kuma tambaye shi wani abu to, ba za a karvi Sallarsa ba har kwana arba’in (Muslim: 4/1751). Amma duk da haka wajibi ne ya ci gaba da Sallar, yana kuma neman gafarar Allah a kan laifin.

Bayan wannan na’ui na Shirka sai kuma:


1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət