Ana səhifə

Gyara kayanka yi hattara da


Yüklə 401 Kb.
səhifə7/12
tarix26.06.2016
ölçüsü401 Kb.
1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12

JIMA’I A LOKACIN HAILA


Haramun ne a shari’ar musulunci mutum ya je wa matarsa a lokacin da take al’ada. Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce:

ﭽ ﮠ ﮡ ﮢﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪﮫ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﭼ البقرة: ٢٢٢



Ma’ana:

Kuma suna tambayar ka game da haila. Ka ce: Ita cuta ce. Saboda haka ku nisanci mata a lokacin da suke haila; Kuma kada ku ku sance su sai sun yi tsarki” (2:222)

Kenab ba ya halatta namiji ya sadu da matarsa sai ta sami xaukewar wannan jini, ta kuma yi wanka. Kamar yadda Allah Subhanahu Wa Ta’ala ke cewa:

ﭽ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﭼ البقرة: ٢٢٢



Ma’ana:

To, idan sun yi wanka sai ku je musu ta inda Allah Ya umurce ku” (2:222).

Qazanta da haxarin da ke cikin sava wa wannan umurni na Allah Subhanahu Wa Ta’ala na daxa fitowa fili idan muka dubi cewar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: “Duk wanda ya sadu da mace tana haila, ko ta baya gare ta, ko ya tafi wurin wani boka, to ya kafirce wa abin da aka saukar wa Muhammadu” Sallallahu Alaihi Wasallama (Tirmidhi: 1/243).

Da qaddara zata sa mutum ya afka wa iyalinsa cikin wannan hali; ba da gangan ba cikin rashin sani babu wata kaffara da zai yi (sai dai ya yi ta istigfari). Amma idan aikin da gangan ne ya yi, tare da ya san hakan haramun ne, to, manyan malamai sun ce, kaffararsa ita ce yin sadaqa da dinari xaya, ko rabinsa. Wasu kuma suka ce: a’a, zai yi dai sadaqa ne da dinari xaya a yayin da ya sadu da iyalin nasa a farkon al’adar. Wato lokacin da suka fi tsiyaya. Amma idan qarshen al’adar ne abin ya faru; lokacin da zubar jinin ta sassafta, to sai ya yi sadaqa da rabin dinari.

A wannan zamani namu dinari xaya na daidai da gwal mai nauyin 25.4 gram. Saboda haka shi ne abin da za a bayar sadaqar, ko kwatankwacinsa.

ZO WA MACE TA BAYA

An samu wasu mutane da qarancin imaninsu ya sa basu damuwa da zo wa matansu ta baya. Wannan kuwa babban zunubi ne. Kuma abu ne da shari'ah ta haramta. Sannan Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya la'anci mai yin sa. Abu Hurairata Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: "Allah Ya la'anci duk wanda ke zo wa mace ta baya" (Ahmad: 2/479) Haka kuma Manzon Allah ya ce: "Duk wanda ya sadu da mace tana haila, ko ta bayanta, ko ya tafi wurin boka, to ya kafirce wa abin da aka saukar wa Muhammadu" (Tirmidhi: 1/243)

Sai dai kuma Alhamdu lillahi, akwai waxansu nagartattun mata masu hankali, da ke qin yarda da mazansu idan sun nemi su zo masu ta baya.

Wani abu kuma kishiyar wannan shi ne, akwai wasu maza da kan yiwa irin waxannan mata barazamar sakin su, a sakamakon haka. Wasu kuma sukan yi iyakar qoqarinsu su gamsar da matan akan cewa, ai babu wani laifi a cikin yin haka. Haka za su rinqa yi yau da gobe, har su ci qarfin mata su yaudare su. Musamman idan aka yin rashin sa’a, matan suka yi nauyi bakin yin fatawa ga malaman sunnah, kafin su bayar da kai bori ya hau.

A qoqarin irin waxannan mazaje na gamsar da matansu a kan wannan mugunyar tagara har kafa masu hujja sukan yi da ayar da ke cewa:

ﭽ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﯧ ﭼ البقرة: ٢٢٣

Ma’ana:

Matanku gonaki ne a gare ku, saboda haka ku je wa gonakinku yadda kuka so" (2:223).

A tunanin waxannan mazaje, da na wasu vatattu irinsu, kalmar "Anna shi’itun" a cikin wannan aya na nufin: "Ta inda duk kuka so”, alhali kuwa ingantattar ma'anarta ita ce: "Yadda kuka so" kamar yadda ya gabata.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama shi ya tabbatar da haka, cewa, halas ne mutum ya zo wa matarsa ta yadda duk ya so; ma’ana su yi gaba-da-gaba, ko ta ba shi baya, matuqar dai zai shiga ta ne, ta inda ake haihuwa.

Wannan mugunyar xabi'a, qazantatta, ta shigo cikin al'ummar musulumi ne, ta wasu da suka musulunta alhali ba su yi bankwana da miyagun al’adunsu na jahiliyya ba, da suka gada daga iyaye da kakanni, waxanda kuma a musulunci haramun ne. Kamata kuwa ya yi a ce sun watsar da su, sun tuba ga Allah, tun shigowarsu a cikin musulunci.

Wani abin da ya kamata a lura da shi kuma shi ne, ba yadda za a yi wannan baqar xabi'a ta halast, koda kuwa mtar da dmijin sun aminta da ita. Domin babu wata yarjejeniya ko haxin baki da suka isa su mayar da haram ta koma halas.


RASHIN ADALCI TSAKANIN MATAN AURE

Tabbatar da adalci tsakanin matan aure na xaya daga cikin abubuwan da Allah Subhanahu Wa Ta’alaYa yi umurni da su a cikin littafinsa Mai tsarki (Alqur’ani) inda Ya ce:

ﭽ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀﮁ ﮂ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﭼ النساء: ١٢٩

Ma’ana:

Kuma ba za ku iya yin adalci (wajen so) a tsakanin mata ba, ko da kun yi kwaxayin yin haka. Saboda haka kada ku karkata, dukan karkata (ga wata a zahiri) har ku bar wata kamar wadda aka rataye. Kuma idan kun yi sulhu, kuma kuka yi taqawa, to lalle ne Allah Ya kasance mai gafara, Mai jinqai” (4:129).

Adalcin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala ke umurnin ko wane miji da tabbatarwa tsakanin matansa, shi ne na daidaitawa a tsakaninsu a wajen kwana da tufafi da xan abin vatarwa. Amma ba so da qauna ba. Wannan kam xan Adamu ba ya da wani iko a cikin sa.

Tattare da wannan umurni da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi, zaka taras wasu mazajen da ke auren mata da dama sun fi matuqar mayar da hankali da kulawa da wata daga cikin su ta hanyar bata mafi yawan lokaci, da abin aljihu, xayar kuma ko sauran sai abinda hali ya yi, su da banza duk xaya. Wani lokacin ma har ta fi su. Irin wannan xabi’a kuwa haramun ce a shari’ar musulunci kuma sakamakon duk mutumin da ke haka shi ne abin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya faxa, in ji Abu Hurairata cewa: “Duk wanda ke da mata biyu, ya kuma fi karkata ga xaya zai zo ranar qiyama sashen jikinsa yana shanyayye” (Abu Dawuda: 2/601).


KAXAITA DA MATAR DA BA MUHARRAMA BA

Har ko wane lokaci shexan, qoqarin yake ta ko wace hanya ya sa mutum ya sava wa Ubangijinsa, ta hanyar sa shi aikata wani abin da sarkin Ya haramta. Saboda wannan dalili ne Allah Subhanahu Wa Ta’ala ke jan kunnen bayinsa tare da yi masu kashedi, inda yake cewa:

ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘﭙ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡﭢ ﭼ النور: ٢١

Ma’ana:

Ya ku waxanda suka yi imani, kada ku bi hanyoyin shaixan. Kuma wanda ke bin hanyoyin shaixan, to haqiqa shi yana umurni da yin alfasha, da abin qi” (24:21)

Wannan gargaxi da jan kunne da maxaukakin Sarki Ya yi wa mutane musulmi, ko shakka babu abun kula da yin hattara ne, tare da kaffa-kaffa. Domin kuwa Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ba shaixan dama da ikon shiga cikin jikin mutum ya yawata kamar yadda jinni ke yawo a cikin jikin.

Wannan dama ce shexan kan yi amfani da ita ya qawata masa wata mata da ba halaliyar sa ba, har a qarshe ya kaxaita da ita, sai ya kai shi ya baro.

Don kaucewa da tsere wa wannan matsala da haxari ne, shari’ar musulunci ta xaukar wa al’amarin mataki tun da wuri. Ta kuwa yi haka ne ta hanyar haramta wa mace da namiji kaxaita in babu igiyar aure da ta haxa su. A kan haka kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke cewa: “Babu wani mutum da zai kaxaita da matar da bata halatta gare shi ba, face shaixan ne na ukunsu” (Turmizi: 3/474).

Haka kuma xan Umar Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa wata rana Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gaya masu cewa: “Daga yau kada wani daga cikinku ya sake shiga gidan wata mata da mijinta ba ya nan sai fa idan yana tare da wani ko wasu” (Muslim: 4/1711).

A kan haka, haramun ne mutum ya kaxaita da matar da ba muharramarsa ba, a cikin wani gida ko xaki ko mota. Matan xan uwansa da na baransa duk sun shiga cikin wannan haramci. Haka kuma bai kamata ba likita namiji ya kaxaita da mace maras lafiya, da sunan duba ta. Wannan idan babu likitoci mata ke nan. Idan ko har akwai su, kuma suka wadatar to, haramun ne likita namiji ya duba wata macein ba muharramarsa ba.

Duk da irin haxarin da ke tattare da wannan matsala, mutane da yawa a yau, sun yi ko-oho da wannan. Wasu na jin sun fi qarfin shexan ne. Ko kuma suna da wasu dalilai na yin haka. Amma kuma a qarshe, mafi yawansu na faxawa cikin abin da ake gudu. Wanda kan haifar da gurvacewar nasabobin mutane, tare da haihuwar baqin haure.


GAMA HANNU DA MATA

Gaisuwa tsakanin maza da mata, ta hanyar yin musabaha hannu da hannu, na xaya daga cikin mIyagun al’adun da mutane suka fifita a kan dokokin Allah Subhanahu Wa Ta’ala a yau. Zaka sha matuqar mamaki, a matsayinka na mai da’awa ko mai gargaxi da faxakarwa, idan ka yi qoqarin ganar da mai yin irin wannan xabi’a cewa hakan bai halatta ba. Domin zai buxi baki ne ba kunya ba tsoron Allah ya soki lamirinka, ya kuma kalle ka xage a matsayin wanda kansa bai waye ba. Har kuma ya zarge ka da qoqarin raba kan ‘yan’uwa. Don wai idan ka ce kada su riqa gaisawa hannu da hannu, kamar kana cewa ne babu aminci a tsakaninsu.

Wannan irin mummunan tunani ya sa irin wannan xabi’a ta zama kamar ruwan dare a cikin al’ummarmu. Amma idan aka dubi abin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke cewa da idon basira, za a fahimci irin haxarin da ke kewaye da mai wannan xabi’a. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa: “Da za a kafa wa xayanku qusa inci tara a maxiga, zai fi sauqi gare shi, (Bisa ga azabar da zai haxuwa da ita) a kan ya tava jikin macen da bata halasta gare shi ba” (Xabarani: 25/212).

Ko shakka babu haxa hannu da mace, da sunan gaisuwa ko rangwaxa irin wadda ‘yan boko da wayayyun mutane ke yi a kan tituna ko cikin jami’o’i, wani nau’i ne na zina. Dalili kuwa shi ne, cewar da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: “Ana iya yin zina da idanu ko hannuwa ko qafafu. Uwa uba in an haxa al’aura” (Ahmad: 1/412).

In don kuwa tsarkin zuciya da qarfin imani da wasu ke gadara da shi ba hujja ba ne. Domin babu wanda ya kai ga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama tsarkin zuciya da qarfin imani. Amma kuma ya tabbata wa duniya cewa: “Ban tava gama hannu da mace ba” (Ahmad: 6/357). Ya kuma ce: Sallallahu Alaihi Wasallama: “Ni ban tava hannu ko wace mace” (Xabrani: 24/342). Haka kuma Sayyida Aisha Raliyallahu Anha ta ce: “Wallahi hannun Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bai tava shafar hannun wata mata wadda ba muharramarsa ba. Ko mubaya’ar da mata suka yi masa da baki ya karve ta kawai” (Muslim: 3/489).

Da wannan ne kuma muke kira da babbar murya ga mazajen da ke yi wa matansu barazanar sakinsu, idan sun qi musabaha da ‘yan’uwan su maza, da cewa su ji tsoron Allah.

Haka kuma ya kamata jama’a su faxaka cewa, safar da wasu matan ke amfani da ita, ko wasu qyallaye, duk ba su hana wannan xabi’a zama haram.
SHAFA TURARE GA MATA LOKACIN FITA

Irin wannan xabi’a ta shafa turare ga mata lokacin da za su fita, bayan sun cava ado, ta yawaita a waxannan kwanuka. Alhali kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gargaxi al’ummarsa da babbar murya a kan haka, inda ya ce: “Duk macen da ta shafa turare lokacin da zata fita ta shiga mutane, da nufin ta xauki hankalinsu da shi, ta sunanta mazinaciya” (Ahmad: 4/418)

Amma duk da wannan gargaxi na Manzon Allah, wasu matan ba su xauki wannan xabi’a bakin komai ba. Musamman idan za su fita tare da direbobinsu ko na haya, ko za su kai yaransu makaranta, da sauransu.

Halas ne ga mace ta shafa duk kalar turaren da take sha’awa idan tana zaune a cikin gidanta. Amma idan fita ta kama ta, shari’ah cewa ta yi ta yi wanka irin na janaba. Ko da kuwa masallaci zata tafi. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama cewa ya yi: “Duk matar da ta shafa turare lokacin da zata fita zuwa masallaci, da niyyar ta xauki hankalin mutane da shi, to Allah ba zai karvi sallarta ba. Har sai, ta yi wanka irin na janaba” (Ahmad: 2/444).

A kan wannan ko shakka babu Allah Subhanahu Wa Ta’ala zai isar wa mutane a kan irin qanshin turaren Bakhur da wasu mata ke kashe su da shi a lokacin bukukuwan aure da walima. Da kuma irin turaren zamani da wasunsu ke baxawa, masu tsananin qarfi da tayar da hankali, idan za su tafi kasuwanne, ko za su hau motocin sufuri, ko zasu halarci waxansu wurare, inda za su haxu da maza, kamar masallattai, musamman a dararen watan azumi.

Musulunci bai hana mace ta shafa turare ba, kamar yadda muka faxa a baya kaxan. Amma sai ya ce wanda zata shafa ya kasance mai launi ne amma ba mai tashin qamshi ba.

Muna roqon Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya sa mu tsira da mutuncinmu. Kada kuma Ya kama mu da laifin da wawaye daga cikin maza da matanmu suka aikata. Ya kuma xora mu a kan hanya madaidaiciya.
TAFIYAR MACE BA TARE DA MUHARRAMI BA

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ba ya halasta ga macen da ta yi imani da Allah da Ranar qiyama ta yi tafiyar kwana xaya ba tare da wani muharrami ba” (Muslim: 2/977).

Wannan hani da shari’ah ta yi, ta yi shi ne don kare martaba da alfarmar mata. Saboda a duk lokacin da mace ta bar gari ita kaxai, raunin xabi’arta da halittarta za su ba maza masu raunin imani damar qoqarin taya ta. Suna kewayar ta suna lasar baki kamar maye ya ga kurwa. Wanda a qarshe ko ba su sami damar sun zubar da mutuncinta ba, sun dai takura ta.

Wannan haramci ya haxa har da matar da zata hau jirgin sama. Koda kuwa wani zai raka ta zuwa filin jirgi, a can kuma inda zata sauka wani zai tarbe ta. To wa ye zai zauna tare da ita, kafaxa da kafaxa a cikin jirgin? Ko kuma ya zata yi idan wata matsala ta faru ga jirgin hakan kuma ta tilasta karkata akalansa zuwa wani filin jirgi, ko jirgin ya makara, ko… ko… ko…?

Matsaloli marasa daxin ji sun sha faruwa sanadiyyar irin wannan sakaci da riqon sakainar kashi da ake yi wa mata.

Wani abin lura kuma shi ne, ba ko wane mutum ne, shari’a ta lamunce ya zamo mata muharrami abokin tafiya ba, sai in ya kasance: 1) Namiji, 2) Musulmi, 3) Mai qarfin kare ta kuma 4) Mai kamun kai.

Abu Sa’id al-Khudri ya ce: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: ‘Kada wata mace da ta yi imani da Allah da Ranar qarshe ta yi tafiyar da ta kai kwana uku ko fiye, ba tare da mahaifinta ko xanta ko xan’uwanta ko wani muharraminta ba’” (Muslim: 2/977).
KALLON WANDA BA MUHARRAMI BA DA GANGAN

Kallon wanda ba Muharrami ba, namiji ko mace, ga ko wanensu haramun ne, matuqar hakan ta kasance da ganganci. Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce:

ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﮄﮅ ﮆ ﮇ ﮈﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﭼ النور: ٣٠

Ma’ana:

Ka ce wa muminai maza su kau da ganinsu, kuma su tsare farjojinsu. Wannan shi ne mafi tsarki a gare su. Haqiqa, Allah, mai qididdi gewa ne ga abin da suka sana’antawa (24:30).

Kallon wanda ba muharrami ba ta irin wannan siga wani nau’i ne na zina, kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Mugun kallo shi ne zinar idanu” (Bukhari: 11/26).

Shari’ar Musulunci bata hana kallo mai ma‘ana, a kan kuma wani dalili na shari’ah ba. Kamar kallon da wani zai yi wa wata da nufin aure. Ko wanda likita zai yi wa wata da nufin duba lafiyarta. Da sauransu.

Ba maza kawai ba. Haka su ma mata an haramta masu kallon mazajen da ba su halasta gare su ba, irin wannan mugun kallo na da gangan. Allah Subhanahu Wa Ta’ala na cewa:

ﭽ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﭼ النور: ٣١



Ma’ana:

Kuma ka ce wa muminai mata su kau da ganinsu kuma su tsare fajojinsu (24:3).

Haka kuma shari’ar musulunci ta haramta wa namiji ya kalli xan’uwansa namiji, kallo irin na kwaxai, irin wanda wasu kanyi wa hansari daga cikin matasa. Haka kuma haramun ne namiji ya dubi al’aurar xan’uwansa namiji, ko mace ta kalli al’aurar ‘yar uwarta mace. Ka ko ga duk abin da kallonsa ya haramta, ko shakka babu haramcin tavinsa tabbatacce ne, koda kuwa akwai wani shamaki (kamar qyalle) a tsakani.

Wata hanya kuma da shexan kan bi, ya iza mutane ga faxa wa wannan haramiya ita ce, saka masu tunanin cewa, kallon hotunan mata a cikin mujallu, da kallonsu a finafinai, bai shiga qarqashin wannan haramcin ba. Saboda ba abu ne da ke faruwa a zahiri ba. Alhali kuwa irin waxannan kallace-kallace na motsa qwazaba da tayar da hankali.


1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət