Ana səhifə

Gyara kayanka yi hattara da


Yüklə 401 Kb.
səhifə4/12
tarix26.06.2016
ölçüsü401 Kb.
1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12

Rantsuwa Da Wanin Allah


Allah Maxaukakin Sarki shi ke da iko da damar yin rantsuwa da duk abin da ya ga dama daga cikin abubuwan da ya halitta. Babu wani mutum da ke da damar yin rantsuwa da wani abu da ba Allah ba. Amma kuma duk da haka akwai mutane da dama daga cikin musulmi da ke yin rantsuwa da wanin Allah. Yin haka kuwa ba wa abin da aka yi rantsuwar da shi ne matsayin Allah Subhanahu Wa Ta’ala. Wannan kuwa laifi ne babba. Xan Umar ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Haqiqa Allah Ya haramta maku yin rantsuwa da ubanninku. Duk wanda rantsuwa ta kama shi daga cikinku, to ya rantse da Allah ko ya kama bakinsa. (Bukhari: 11/530). Haka kuma xan Umar xin ya riwaito Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa:duk wanda ya rantse da wanin Allah ya yi Shirka. (Ahmad: 2/125).

Haramun ne mutum ya rantse da: Xakin Ka’aba, ko Gaskiyar wani ko tasa, ko Darajar wani ko tasa, ko suturar wane da wane, ko rayuwar wane da wane, ko Mu’ijizojin wani Manzo, ko karamar wasu Waliyyai, ko mutum ya rantse da Mahaifansa ko dai wani abu. Duk wanda ya aikata haka to, ya yi Shirka. Babu abinda zai kankare masa wannan laifi sai sake faxar kalmar shahada; ita ce: “La’ilaha Illal-lah”. Kamar yadda wani ingantaccen hadisi ya ce: “Duk wanda ya yi rantsuwa da Lata ko Uzza, to ya ce: “La’ilaha Illallah” (Bukhari: 11/536).

Bayan irin wannan rantsuwa da wanin Allah ta kai tsaye, akwai waxansu kalamai da musulmi ke furtawa waxanda kuma ba wani abu a cikinsu sai Shirka. Kalaman sun haxa da:


  1. Ina neman taimakon Allah da naka”

  2. Wannan abu daga Allah ne da kuma kai

  3. Ba ni da kowa sai Allah sai kai

  4. Taqamata Allah a sama da kai a qasa”

  5. Ba don Allah da wane da wane ba..”

  6. “….na jingine musulunci”

  7. Shekara ta karya ni

  8. Wannan mummunan lokaci ne”

  9. Zamani xan mangwaro ne.

Haka kuma akwai wasu sunaye da wasu musulmi ke amfani da su, waxanda ke xauke da amon Shirka, kamar:-

    1. Abdul- Masihi (Bawan Masihu)

    2. Abdun- Nabiyi (Bawan Annabi)

    3. Abdul- Husaini (Bawan Husaini)

Duk ire-iren waxannan Sunaye da ke danganta mutum ga wani wanda ba Allah ba, a matsayin bawansa, haramun ne. Kamar yadda yake haramun musulmi ya furta irin waxancan kalamai da muka faxa don sun qunshi haxa Allah da wani, ko sukar lamirin wani lokaci tun da yin haka suka ne ga Allah Shi kansa.

Haka kuma akwai waxansu kalamai da zamani ya zo da su waxanda ke takin saqa da Tauhidi. Su ma duk furta su da qudurce ingancinsu a zuci haramun ne ga musulmi. Waxannan kalamai sun haxa da kamar:



  1. Gurguzun Musulunci (Islamic Socialism)

  2. Dimuquraxiyyar Musulunci (Islamic Democracy)

  3. Ra’ayin Mutane shi ne Ra’ayin Allah

  4. Addini na Allah ne, qasa kuma ta kowa ce

Da sauran su.

Haka kuma haramun ne a ambaci wani munafuki ko kafiri da xaya daga cikin waxannan laqubba.



  • Alqalin Alqalai

  • Sarkin Sarakuna

  • Mai gida

Haka kuma yin “da-na sani” ta hanyar amfani da kalmarDa dai..” ko “in da ..” haramun ne. Domin kalmar na nuna cewa mutum bai gamsu da wani abin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya riga ya hukunta ba.

Haka kuma cewa:Allah ka gafarta mani in ka ga dama” shi ma haramun ne.

Mai son qarin bayani da faxaxa nazari sai ya duba littafin: Mu’ujamul Manahil Lafziyyah Na Sheikh Bakr Abu Zaidi.

BABI NA BIYU

Zama Da Munafukai Da Mavarnata


Wani abu kuma da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta kuma mutane suka yi biris da shi, shi ne zama wuri xaya da munafukai da mavarnata. Zaka sami mutane da dama saboda rashin qarfin imani suna zamansu gaba gaxi tare da irin waxannan mutane marasa tarbiyyah da tsoron Allah. Wani lokacin ma sukan zauna har tare da waxanda ke sukar lamirin shari’ar Musulunci, suna zolayar addini da masu kishinsa.

Ko shakka babu irin wannan xabi’a haramun ce. Kuma abu ne da ke rosa imanin mai yinsa. Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce;

ﭽ ﯷ ﯸ ﯹ ﯺ ﯻ ﯼ ﯽ ﯾ ﯿ ﰀ ﰁ ﰂ ﰃﰄ ﰅ ﰆ ﰇ ﰈ ﰉ ﰊ ﰋ ﰌ ﰍ ﰎ ﰏ ﭼ الأنعام: ٦٨

Ma’ana:

Kuma idan ka ga waxanda suke kutsawa a cikin ayoyinmu, to, ka kau- da- kai daga gare su, sai sun shiga cikin wani labari ba shi ba. Kuma in ma dai shexan ya mantar da kai, to kada ka zauna a bayan tanawa tare da mutane azzalumai (6:68).

Wannan aya ta tabbatar mana da haramcin zama tare da waxannan mutane, koda kuwa makusanta ne na qud-da qud. Sawa’un kun haxa zumuntar jini ko hulxar arziki. Sai fa idan za ka zauna ne a wurinsu don ka yi masu gargaxi ko ka qalubalance su game da abinda suke yi don su daina. Idan ba haka ba, to haramun ne mutum ya zauna da su. Allah Subhanahu Wa Ta’ala na cewa:

ﭽ ﮈ ﮉ ﮊ ﮋﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﭼ التوبة: ٩٦



Ma’ana:

Suna rantsuwa gare ku (Su Munafukai) don ku yarda da su. To, ko kun yarda da su haqiqa Allah ba shi yarda da mutane fasiqai. (8:96).

Ke nan duk wanda ya zauna tare da waxannan mutane zama na yarda da amincewa, to ya zama xaya da su.

Rashin Natsuwa A Cikin


Sallah

Wani abun kuma da shari’a ta haramta shi ne yin sallah ba cikin cikakkar ratsuwa ba. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Babu Babban Varawo irin wanda ke satar wani abu daga cikin sallarsa. Sai sahabbai suka ce: “Ya Manzon Allah, ya za a yi mutum ya saci wani abu daga cikin sallah”? Sai ya ce: “Idan ya qi yin ruku’i da sujuda cikin natsuwa” (Ahmad: 5/310).

Rashin cikakkar natsuwa a cikin ruku’i da sujuda da tsayuwa bayan ruku’i da zama tsakanin sajaddai biyu, abu ne da ya zama ruwan dare a tsakanin musulmi yau. Babu wani masallaci da zaka leqa sai ka tarar da irin wannan matsala birjik. Alhali kuwa natsuwa babban rukuni ce a cikin sallah, wanda sai ya samu ne take zama karvavviya a wurin Allah. Wannan mas’ala babba ce matuqa. Domin kuwa Manzon Rahama Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Sallar mutum ba zata zama karvavviya ba har sai gadon bayansa ya zama shimfixe a lokacin da yake ruku’i da sujada (Abu Dwuda: 1/533).

Ko shakka babu, rashin cikakkiyar natsuwa a sallah ba abu ne mai kyau ba. Kuma duk wanda ke haka ya cancanci gargaxi da faxakarwa da alwashin horo na musamman.

Abu Abdillahil Ash’ari ya riwaito cewa: Wata rana Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ba wa shabbansa wata sallah. Da aka qare kuma ya zauna wurin tare da wasu daga cikinsu. Suna nan zaune a haka, sai ga wani mutum ya shigo ya kabbarta sallah, yana ta qoton kurciya. Kafin xan wani lokaci ya sallace.

Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Kun ga yadda mutumin nan ya yi sallah ko? To, duk wanda ya mutu yana irin wannan sallah bai mutu a kan addinin Muhammadu ba. Kuma sallarsa ba ta da banbanci da hankaka a lokacin da take qoton jini. Mai irin wannan sallah kuma daidai yake da mayunwacin da zai ci qwarar dabino xaya ko biyu. Kuna ganin za su amfane shi? (Ibnu Khuzaimah 1/332).

Haka kuma Zaidu xan Wahabu ya ce: Huzaifah ya ga wani mutum na sallah, yana ruku’insa da sujada yadda ya ga dama sai ya ce masa: “Sallarka bata yi ba. Kuma da zaka mutu yau ka sani ba zaka mutu a kan addinin da Allah Ya saukar wa Muhamadu Sallallahu Alaihi Wasallama ba (Bukhari: 2/274).

Don haka, duk wanda yake da masaniya da waxannan hadisai, ya kuma qi yin sallah cikin natsuwa, to wajibi ne ya sake ta, ya kuma nemi gafarar Allah akan abin da ya gabata. Don ko Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce wa mai munana sallarsa: “Je ka sake wannan sallah, don ba ta yi ba”. Amma fa ba lalle ne sai ya maimaita gaba xayan sallolinsa da suka gataba ba.


1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət