Ana səhifə

Gyara kayanka yi hattara da


Yüklə 401 Kb.
səhifə12/12
tarix26.06.2016
ölçüsü401 Kb.
1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12

QARYAR MAFARKI

Da gangan wasu mutane ke qirqira mafarki, har su ce sun ga wani abu a cikinsa, don kawai neman girma a idon mutane ko wani abin duniya, alhali qarya suke yi ba su ga komai ba. Kai! Ko mafarkin ma ba su yi ba. A yayin da wasu mutanen kuma kan yi haka ne don su tsorata wasu magabata da ke masu barazana ko wani abu mai kama da haka.

Irin waxannan qaryace-qaryace kan yaudari hankalin mutane, saboda rashin isassar wayewa da cikakken Ilimi, da kuma imanin da suke da shi ga mafarki.

Wannan xabi’a na xaya daga cikin xabi’un da shari’ar musulunci ta haramta. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Mafi girman qarya ita ce danganta mutum ga wanda ba mahaifinsa ba. Ko iqirarin ganin wani abu (a cikin mafarki) a kan qarya. Ko a jingina wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama abin da bai ce ba (Bukhari: 6/540).

Haka kuma ya ce: “Duk wanda ya yi qaryar ya yi mafarkin wani abu alhalin bai yi ba za a titasta masa xaure ‘ya’yan sha’ir biyu. Ba kuma zai iya ba (Bukhari: 12/427).

Xaure qwayar sha’ir biyu wuri xaya abu ne da baya yiwuwa. Kamar yadda wancan mafarki da aka yi qaryar yi bai kasance ba.


TOZARTA QABURBURA

Abu Hurairata Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Da xayanku zai zauna a kan garwashin wuta, har ya ruru ya qone tufafinsa, ya kai ga fatar jikinsa, ya fi alheri gare shi bisa ga ya zauna a kan qabari (Muslim: 2/667).

Kafin zama a kan qabari ma, wasu mutane nada xabi’ar tattakawa da yin tafiya a kansa, ba tare da wata damuwa ba. Musamman a lokacin da aka tafi maqabarta don nufe wani. Wasu ma har da takalmi a qafafunsu. Haka za su bi qaburburan da ke maqwabtaka da wanda suka kai, suna tattaki a kai, ba kunya ba tsoron Allah, balle su tuna da wata alfarma da mamatan da ke kwance wurin ke da. Alhali kuwa wannan matsala mai matuqar nauyi ce. Musamman idan aka yi la’akari da faxar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama da ya ce: “Da zan yi tattaki a kan garwashi ko kaifin takobi, ko in wanke takalmina da xayan qafata, ya fi soyuwa gare ni bisa ga in yi tattaki a kan qabarin wani musulmi (Ibnu majah: 1/499).

Wannan kenan. To ina ga waxanda ke yankar filin maqabarta su gina gidaje ko shaguna? Wasu mutanen ma saboda tsananin rashin kirki da taskai, har bayan gari sukan yi a cikin maqabarta, suna damun bayin Allah da ke kwance wurin da qazanta. Irin waxannan mutane na fuskantar babban haxari. Domin kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Wanda ke biyan buqatarsa a cikin maqabarta daidai yake da wanda ke biyan ta a cikin tsakiyar kasuwa (Wato asirinsa a tone yake).

Haka kuma wannan gargaxi da kashedi ya haxa har da waxanda ke zubar da shara a cikin maqabarta. Ta hanyar amfani da damar kasancewar bangayen maqabartun sun zube, ko an daina amfani da su. Duk irin halin da maqabarta take ciki, haramun ne a yi mata irin wannan tozarci.

Kai! Har waxanda ke zuwa ziyara a maqabartu wajibi ne su cire takalminsu, matuqar dai za su ratsa qaburburan da ke ciki.


RAGGON TSARKI

Karantar da xan Adamu kowace irin tagara da za ta sa ya ci gaba da zama mutum kammalalle, na daga cikin abubuwan da addinin Musulunci ke alfahari da su. Don babu wani addini ko tsarin rayuwa da ya riga shi a wannan fagen.

Yin cikakken bankwana da qazantar fitsari ko gayaxi a lokacin da suka fita daga jikin mutum, ta hanyar wankewa da ruwa ko hoge tas-tas tas, na xaya daga cikin waxannan darussa. Amma kuma mutane da dama sun yi biris da wannan koyarwa ta musulunci. A inda suke sakaci har jikinsu da tufafinsu su yi kace-kace da xayan wannan najasa. Ta yadda ko sun yi sallah Allah ba zai karva ba. A qarshe kuma su taras da azaba a cikin qaburburansu. Kamar yadda xan Abbas ya riwaito cewa: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya wuce ta wata maqabarta a garin Madina sai ya ji qarar wasu mutane biyu ana yi masu azaba a cikin qaburburansu. Sai ya ce: “Ana azabtar da su ne, ba don wani babban laifi ba. Kai! Babban laifi ne shi ma: Xayan dai ba ya tsabtaci al’aurarsa da kyau idan ya yi fitsari. Xaya kuma ba ya da aiki sai yawo da tsegumi (Bukhari: 1/317).

Akwai ma hadisin da Manzon Allah ke cewa a ciki: “Mafi yawan azabar qabari a kan fitsari take (Ahmad: 2/326).

Abubuwan da kan haddasa irin wannan matsala ta rashin samun cikakken tsarki, sun haxa da: i) Gaggawa a gama, ii) Tsugunawa Wuri Mai Tsauri, iii) Rashin damuwa da wankewa da kyau.

Wata babbar matsala kuma da ke taka gagarumar rawa a wannan hauji, ita ce irin yadda muka yi nisa matuqa a cikin kwaikwayon al’adun Turawa. An wayi gari wasu wuraren da muke fitsari a yau irin na Turawa ne, da ake xafawa a bango kuma a fili. Ta yadda ma duk wanda zai wuce yana ganin wani abu na tsiraicin wanda ke biyan buqata a wurin.

Ka ga irin waxannan mutane laifinsu ya zama biyu kenan, ga qazanta ga tsiraici.
TSINCE

Allah maxaukakin Sarki Ya ce:

ﭽ ﭝ ﭞ ﭼ الحجرات: ١٢

Ma’ana:

Kuma kada ku yi leqen asirin (‘yan uwanku) (49:12)

Xan Abbas Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya tsinci maganar da wasu mutane ke yi, ba tare da sun sani ba, za a zuba ruwan narkakkar darma a kunnuwansa ranar qiyama (Xabarani: 11/248-249)

Idan wanda ya yi irin wannan haramtaccen aiki, ya yi ne da nufin kai wannan magana da ya tsinta a wani wurin, don ya tayar da wata wuta, to, Gummi ta haxu da Anka kenan; ga laifin tsince, ga kuma annamimanci. Wannan mutum ya tave domin kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Annamimi (mai tsince don ya haxa faxa) ba ya shiga aljanna (Bukhari: 10/472).


CUTAR DA MAQWABCI

Haqqin maqwabci a kan maqwabcinsa abu ne mai girma a wurin Allah Subhanahu Wa Ta’ala. Saboda haka ne Sarkin ya haramta cutarwa a tsakaninsu. Inda ya ce:

ﭽﮖ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜﮝ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﭼ النساء: ٣٦

Ma’ana:

Kuma ku bauta wa Allah, kuma kada ku haxa wani da shi, kuma ku kyautata ma mahaifa. Kuma ku kyautata ga ma‘abuta zumunta da marayu da matalauta, da maqwabci na kus da na nesa, da aboki na gefe, da xan hanya, da abin da hannuwanku na dama suka mallaka. Haqiqa Allah ba ya son wanda ya kasance mai taqama, mai yawan Alfahari (4:36)

Haka kuma, Abu Shuraihu Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Wallahi ba ya da imani, wallahi ba ya da imani, wallahi ba ya da imani. Sahabbai Suka ce: waye shi ya Manzon Allah? Ya ce : Wanda maqwabcinsa ba ya tsere wa sharrinsa. (Bukhari: 10/443)

Matsayin maqwabci a wurin maqwabci abu ne mai matuqar girma. Wanda har ta kai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya sa maqwabci shi ne ma’aunin gane kirki ko rashin kirkin mutum.

Xan Mas’udu ya riwaito cewa, wani mutum ya ce wa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama, ya Manzon Allah, ya zan yi in gane kirki ko rashin kirkina? Sai Ma’aki ya ce masa: “Duk lokacin da ka ji maqwabtanka na cewa kana da kirki, to, kana da shi. Idan kuwa ka ji suna cewa ba ka da shi, to, lalle ba ka da shi xin”. (Ahmad: 1/402)

Cutar da maqwabci na iya tabbata ta fuskoki da dama. Duk wanda ya hana maqwabcinsa jingina wani katakon runfa ga bangon da ya raba su, suke kuma da haqqi gaba xaya a cikinsa, ko ya faxaxa nasa gini, ta yadda xayan zai sami qarancin hasken rana ko iska, ba kuma tare da izinin xayan ba. Ko ya fasa, ko buxe tagoginsa ta yadda zai riqa leqen gidan xayan. Yadda ba wani abu na asiri da za a iya yi a xaya gidan sai bisa idonsa. ko ya dinga damunsa da kaxe-kaxe a kan fayafan garmaho, ko hargowa, musamman a lokacin da yake baccin dare ko na rana, ko ya xauki sabgar jibge shara a qofar gidan xayan. Duk wanda ke yi wa maqwabcinsa xayan waxannan xabi’u, to, ya cutar da shi matuqa. Daxa balle tava iyalinsa ko dukiyarsa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa: “Da mutum zai yi zina da mace goma can nesa, ya fi sauqi gare shi, bisa ga ya yi da matar maqwabcinsa. Da kuma zai fasa wasu gidaje goma can nesa, ya fi sauqi gare shi bisa ga ya fasa gidan maqwabcinsa (Bukhari:103).

Bone ya tabbata ga mutanen da ke da xabi’ar amfani da damar waxansu maqwauta nasu da basu kasancewa gida da dare don yanayin aikinsu, sai su faxa gidajensu su aikata varna. Ranar qiyama sun shiga uku.
TAUSHE HAQQIN MARAYU

Yana daga cikin dokokin shari’ar musulunci cewa, yana da matuqar kyau mutum ya yi qoqari iyakar zarafi ya yi haqurin cutarwar da xan’uwansa zai yi masa. Na farko kenan. Kuma haramun ne shi ya zama farkon wanda zai yi cutar.

Taushe haqqin maraya, wani zalunci ne da cutarwa, wanda kuma shari’a ta haramta. Abu ne mai sauqin gaske wanda za a gada ya taushe haqqin wasu daga cikin magadansa, tun kafin ya mutu. Wannan na faruwa idan ya yi amfani da sauran nunfashinsa a duniya, ya rubuta wata wasiyya a kan abin da zai bari na dukiya. A irin wannan dama ce wasu kan taushe haqqen wasu marayu ta hanyar kore su daga cikin magadansu na haqiqa. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi gargaxi da babbar murya ga duk mai irin wannan hali, da ya ce: “Duk wanda ya cutar da wani Allah zai musguna masa, duk kuma wanda ya tsananta wa wani Allah zai tsananta masa (Ahmad: 3/453).

Wata hanyar kuma da mutum ke iya karva sunan mai taushe haqqin marayu ita ce, a wasiyyarsa ya ware wa wani magadi, fiye da abin da shari’ah ta yanka masa ko ya yi wasici da ba wa wani mutum fiye da kashi xaya bisa uku na dukiyarsa.

Irin wannan matsala ma nada ‘yar dama a qasashen da musulunci ke jagoranci. A qasashen da ko ba dokokin shari’ar musulunci ne ake aiwatarwa ba, da yawa ake samun irin waxannan matsaloli. Kuma ko sun faru babu yadda magadi zai yi ya karvi haqqinsa wanda Allah Ya shata masa. Domin dokokin da kutunan da za a iya kai kuka gare su, ke aiwatarwa, na iya xaure wa irin wannan zalunci gindi, musamman idan da hannun wani lauya a ciki. Ga shi ko Allah Ta’ala ya ce:

ﭽ ﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭬ ﭭ ﭮ ﭯ ﭰ ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵﭶ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﭼ البقرة: ٧٩



Ma’ana:

Bone ya tabbata gare su daga abin da hannayensu ke rubutawa, kuma bone ya tabbata gare su daga abin da suke sana’antawa (2:79).


DARA

Dara da Ludo da Karta da Diraf da makamantansu, na duk wata wasa, da ake dibilwa da hannu da qwaqwalwa don fitar da gwani a cikin ta, haramun ne a musulunci. Dalili kuwa shi ne, dukansu qofofi ne da ke kai masu wasannin zuwa ga caca. Saboda haka ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi mana ahir da su ya ce: “Duk wanda ke Dara daidai yake da wanda ya cava hannunsa cikin naman alade ko jininsa (Muslim: 4/394).

Haka kuma Abu musa Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ke Dara, ya sava wa Allah da Manzonsa (Ahmad: 4/394).
LA’ANTAR MUSULMI

Mutane da yawa kan kasa ja wa halshensu lizzami lokacin da suka fuskanta. A sakamakon haka sai nan- da nan su furta kalmomin la’anta ga wasu mutane, ko dabbobi, ko sandararrun abubuwa. Wasu ma har kwanaki da awoyi suke la’anta. Da makamantansu. Kai! Saboda tsananin shaqawa da rashin taskai ma, wasu har kawukansu, ko ‘ya’yansu sukan la’anta. Wasu ma’aura kuma kan la’anci juna lokaci xaya, ko lokuta daban-daban.

Wannan matsala nada matuqar girma a idon shari’ah. Saboda haka ta haramta ta. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, a wani hadisi da Abu zaidi Sabitu xan Dhahhaku ya riwaito cewa: “Duk wanda ya La’anci mumini, to zunubinsa daidai yake da na wanda ya kashe shi (Bukhari: 10/465).

Al’adance, irin wannan xabi’a ta la’ance- la’ance, ta fi yawaita a bakunan mata a cikin ko wace al’umma. Saboda haka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayyana cewa wannan xabi’a ce zata kasance dalilin shigar mafi wayansu wuta. Kuma su, da duk wanda ke irin wannan sabga, basu cikin waxanda zai ceto ranar qiyama.

Wani babban haxari ma duk bai fi kasancewar la’antar duk da mutum ya yi ba bisa qa’ida ba, zata dawo kansa. Daxa kome kuwa ya la’anta. Kaga kenan qaiqayi ya koma kan masheqiya. Da haka kuma mutum ya nisanta kansa daga rahamar Allah.
KUKAN MUTUWA

Kukan mutuwa ta hanyar hargowa da kururuwa, da faxuwa ana tashi, yagar fuska da keta tufafin da ke jiki, kamar an yi sabuwar hauka, abu ne da shari’ar musulunci ta haramta.

Mata su suka fi yin irin wannnan mugunyar xabi’a. Kai! Wasu ma daga cikinsu har aske gashin kansu sukan yi, da yin wasu xabi’u da suka sava wa hankali. Waxanda ke nuna cewa ba su karvi wannan qaddara ta rashi da hannu biyu ba. Kuma ba shirye suke su yarda da hukuncin Allah kome xacinsa ba.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya la’anci duk mai irin wannan xabi’a. Abu Umamata Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya la’anci duk macen da ke yagar fuskarta, ta kece tufafin da ke jikinta, ta yi ta hargowa, tana faxin bone yoyo! (Ibnu majah: 1/505).

Haka kuma Abdullahi xan Masu’du Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ke yagar fuskarsa, ya kece tufafinsa, ya kuma yi kururuwa irin ta jahiliyyah, ba ya tare da mu (Bukhari: 3/163).

Haka kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Idan mai kukan mutuwa irin na jahiliyya ta mutu ba ta tuba ba, ranar qiyama za ta tashi da rigar qaya da maxaurin qarangiya (Muslim: 934).


MARI DA TSAGA

Wasu uwaye da malamai nada xabi’ar sa hannu ko wani abu su mari ‘ya’yansu ko xalibansu ko masu yi masu hidima, da nufin ladabtarwa. Ladabtarwa kuwa gaskiya ce. Amma fuskar xan Adamu na xaya daga cikin abubuwan da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya karrama. Kai mata mari kuwa tozartawa ne, da rena hikimar Allah, da walaqanta abin da ya girmama.

Abun kan wuce mari. Wasu mutane har aska, ko wani abu mai kaifi sukan sa su yi wa fuskar ‘ya’yansu raxam, da nufin tabbatar da wata al’ada ta gida a matsayin alama. A yayin da wasu kuma dabbobinsu suke yi wa tsagar, wai don a banbance tsakanin garken wane da na wane. Kuma hakan za ta taimaka ga gane ai wannan dabbar ta wane ce. Idan ta yi vatan kai nan take sai a mayar masa da abarsa.

Marin xan Adam haramun ne a shari’ar musulunci. Saboda hakan kan iya sa a rasa wani abu daga cikin martabobin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya sa a cikinta. Kamar: Gani, ko ji, ko shaqe. Wanda a qarshe za su kai wanda ya yi abun ga nadama. Kuma diyya za ta hau kansa.

Abin da ya shafi xan Adam kenan. Ta fuskar dabbobi kuwa, su ma shari’ah ta haramta yi masu wuta a fuska ko wata tsaga a matsayin alama. Idan ma har ya zama dole sai an yi masu wata alama, saboda kasancewar haka al’ada, to sai dai a yi masu a jiki ba a fuska ba, kuma ba da wuta ba.

Shari’ah ta haramta yi wa dabba mugun duka da tsaga ga fuska, kamar yadda ta haramta yi wa bil adama. Saboda tsagar na matuqar wahalar da dabbobin tare da takura su.

A taqaice dai, shari’ar musulunci ta haramta mari da tsaga a fuska. Jabir Raliyallahu Anhu ya ce: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya haramta mari da tsaga a fuska (Muslim: 3/1673).
GABA

Gaba, wani abu ne da shaixan ke haddasawa tsakanin musulmi, har wani ya yafe xan’uwa na tsawon lokaci ko har abada ba tare da wani qwaqqwaran dalili na shari’a ba. Wata ‘yar rashin jituwa ce kawai za ta faru tsakaninsu a kan wasu kuxi, ko wata ‘yar hayaniya akan banbancin yare, ko wata shiririta mai kama da haka. Sai kawai a qulla gaba.

Wani har rantsewa zai yi: Ni da wane wallahi, har abada. Shi kenan, ba zai sake taka qofar gidansa ba. Da ma ya hange shi sai ya sake hanya ko ya daure su haxu amma ba zai ce masa tin qanzil ba. Da kuma zai yi kicivis da shi a cikin dubu, zai gaisa da kowa hannu da hannu, ya yi banza da shi. Irin wannan xabi’a bata daxa al’ummar musulmi da komai sai rauni bisa rauni. Saboda haka Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi wa musulmi kashedi da babbar murya, a wani hadisi da Abu Hurairata Raliyallahu Anhu ya riwaito daga Annabi Sallallahu Alaihi Wasallama cewa: “Ba ya halalta ga musulmi ya qaurace wa xan’uwansa musulmi fiye da kwana uku. Duk wanda kuwa ya qauracen fiye da haka, makomarsa ita ce wuta (Abu Dawuda: 5/215).

Haka kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya qaurace wa xan uwansa tsawon shekara xaya, kamar ya zubar da jininsa ne (Bukhari: 406).

Wata babbar matsala ma duk, ba ta fi kasancewar gaba dalilin hushin ubangiji ga masu yin ta ba, da nisantar da su daga rahamarsa da gafara da jinqayi. Abu Hurairata ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ana gabatar da ayyukan mutane a kowane sati (ga Allah) sau biyu: Ranar Litinin da Alhamis. A inda Allah zai gafarta wa kowane mumini daga cikinsu, sai fa wanda ke gaba da wani xan uwansa, shi kuma ya yarda da gabar. Sai ubangiji ya ce: “Qyale waxannan sai sun shirya tukun (Muslim: 4/1988).

Da zarar xaya daga cikin su ya tubar wa Allah, har ya je ya fara gaisawa da abokin gabarsa, ko ya karva masa ko bai karva masa ba, shi dai ya fita; ya xauke nauyi. Matsalar ta rage kan wancan. Abu Ayyuba Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ba ya halalta ga mutum ya qaurace wa xan’uwansa fiye da kwana uku, su haxu kafaxa da kafaxa kowa ya xauke kai. Duk wanda ya fara yi wa xaya sallama shi ne mutumen kirki (Bukhari: 10/492).

Wannan, idan gabar ta kasance dalilin wani abin duniya ne. Amma a lokacin da mutum ya qulla gaba da wani musulmi xan’uwansa, saboda wasa da yake yi da sallah, ko wasu miyagun halaye da suka sava wa shari’ah, ba wani laifi. Musamman idan hakan na sa ya karkato ya gyara. A irin wannan hali ma wajibi ne a qulla gaba da shi don a tanqwaso shi zuwa ga gaskiya. Idan kuma qulla gabar da shi zata kawai qara sa ya dulmuya cikin ayyukan ne na assha, to, shari’a ba ta ce a qawaurace masa ba. Sai dai a ci gaba da lallashi da yi masa nasiha da gargaxi.
KAMMALAWA

A nan ne kuma muka kawo qarshen abubuwan da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya nufa da rubutawa daga cikin wasu haramtattun abubuwa da mutane suka yi biris da su a yau.

Wannan xan qoqari da akayi kamar share fage ne, don fagen yana da faxi matuqa. An yi wa masu karatu matashiya ne kawai domin akwai buqatar samar da wani aiki mai kama da wannan, inda za a tsame gaba xayan abubuwan da shari’ar musulunci ta haramta a harshen Alqur’ani daban da waxanda ta haramta a harshen Hadisi ko wane a tsara shi daban. Allah Ya bada ikon yin haka.

A qarshe ina roqon Allah Subhanahu Wa Ta’ala da sunayensa tsarkaka, Ya sa mu faxaka, mu kasance masu tsoro da shayinsa fai da voye. Ya kuma nisantar da mu daga ko wane irin savo. Ya sa muna cikakken karsashi da qwarin guiwar bauta ma sa har mu samu shiga aljanna. Kuma ya gafarta mana dukan kurakuranmu don Rahamarsa da jinqayinsa. Ya sa mu wadatu har zuci, da abubuwan da Ya halasta mana, Mu kuma nisanci waxanda Ya haramta.

Allah Ka karvi tubarmu, mun tuba. Ka yi mana wankan tsarki, ba mu sakewa. Mun yi imani da ka fi kowa jin kukanmu, kuma kai mai karva du’ai ne.

Ya Allah ka daxa tsira da salati da sallama ga Manzon nan da ya buwayi masu karatu da rubutu, Muhammadu, da iyalin gidansa da Sahabbansa kacokwam.

Godiya, A qarshen qarshe ta tabbata baki xaya ga Allah, Ubangijin talikai.

Muhammadu Salihu al-Munajjidu

Akwatin Gidan Waya 2999

Al- khobar



Qasar Saudiyyah.
Fassara ta kammala a safiyar Alhamis 24 ga Rabi’ul Akhir 1429 Hijira, wanda ya zo dai dai da 01 ga watan Mayu 2008 Miladiyyah. A Sakkwato Birnin Shehu. Godiya ta tabbata ga Allah shi kaxai.

1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət