Ana səhifə

Gyara kayanka yi hattara da


Yüklə 401 Kb.
səhifə11/12
tarix26.06.2016
ölçüsü401 Kb.
1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12

AMFANI DA KASAKEN ZINARI DA AZURFA

Da yawa ka kan samu kasake da kwanoni na zinari ko azurfa, ko waxanda aka yi wa ado da xayansu a gidajen masu hannu da shuni. Daxa a manyan hotel- hotel nan ne uwa uba.

Irin waxannan kasake da ake qawatawa da wasu zane zane sun yawaita a wasu qasashe na musulmi, saboda amfani da su da ake yi a matsayin kyautuka na masamman. Wasu mutane da Allah bai ba ikon mallakar irin waxannan kayayyaki a gidajensu ba, sai ka taras sun faxa cikin wannan haramiya don za a gayyace su wasu gidaje don wata hidima, qarshe a kawo masu abinci cikin irinsu.

Amfani da irin waxannan kayayyaki a irin waxannan hanyoyi haramun ne a musulunci. Saboda haka ne Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gargaxi dukan musulmi daga amfani da su. Ummu Salamata ta riwaito Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa: “Duk wanda ke ci ko shan wani abu a cikin kaskon zinari ko azurfa yana jefa garwashin wuta ne a cikin cikinsa” (Muslim: 3/1634).

Wannan haramci ya shafi duk wani nau’i na ababen amfani da aka qera da zinari ko azurfa. Kamar Farantai, cokula masu yatsu, da marasa yatsu, wuqaqe, tire- tire da makamantan su. Haka kuma ‘yan adikokin alawa, irin waxanda ake bayarwa a matsayin kyautar alfarma ga baqi ko amare da angwaye. Duk amfani da irin waxannan abubuwa haramun ne, matuqar da zinari ko azurfa aka qera su.

Wasu mutane na iya cewa “To har da mu da ke kwalliya da su kawai a cikin gilasai, abin ya shafa?” Eh, lalle ya shafe ku. Abin da kuke yi xin nan bai halasta ba. Domin kuwa idan dai ana yalla ido a gan su, to lalle wata rana sai an yi amfani da su. Malam Bin Baz ne ya faxi haka.


SHEDAR ZUR

Allah maxaukakin Sarki Ya ce:

ﭽ ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰ ﭼ الحج: ٣٠

Ma’ana:

Saboda haka ku nisanci qazantar gumaka, kuma ku nisanci Zhedar Zur. Kuna masu tsayuwa ga gaskiya domin Allah, ba masu yin shirka da Shi ba” (22:30-31).

Haka kuma Abdurrahaman xan Abubakar Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, mahaifinsa ya ce: Wata rana muna zaune tare da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sai ya ce : Kuna so in ba ku labarin manya- manyan zunubbai? Ya ko maimaita tambayar har sau uku. Sa’annan ya amsa masu da cewa: 1) haxa Allah da wani a cikin bauta, 2) qin uwaye… Manzon Allah yana gincire sai ya tashi zaune. Sannan ya ce: 3) Da kuma Shedar Zur. Mai riwayar (Sayyidina Abubakar) ya ce, Annabi ya yi ta maimaita na ukun nan har muka yi sauraren ya dasa aya.” (Bukhari: 5/261)

Gargaxi da jan kunnen mutane a kan su nisanci Shedar Zur abu ne da shari’a ta faxa ta maimaita ta kuma nanata, saboda irin yadda mutane ba su xauki yin hakan bakin komai ba. Duk da yake kuma an fahimci cewa qiyayya da gaba ne kan sa wasu mutane faxa wa wannan haramiya don fashe haushinsu akan wani wanda suke adawa da shi. Amma kuma hakan ba ya zama hujja gare su. Musamman idan aka yi la’akari da irin mummunan sakamakon da tagarar ke haifarwa wanda ya haxa da; i) Sa mutane da yawa hasarar wasu haqqoqa nasu, ii) jefa wasu mutane da yawa cikin baqar musiba ba su ji ba su gani ba, iii) share wa wasu mutane da yawa hanyar samu da mallakar abin da ba su cancanta ba. Da sauransu.

Wani babban misalin da ke tabbatar da irin yadda mutane ba su xauki Shedar Zur bakin komai ba shi ne abin da kan faru a wasu kotunanmu a yau. Nan take wani zai ce wa wani “Zo ka shede ni, ni kuma in shede ka”. Alhali kuwa a wannan lokacin ne suka fara haxuwa.

Ka ga kenan ko wanensu zai shedi xaya a kan abin da bai san komai game da shi ba, balle ya iya bayanin yadda ya faru dalla dalla. Wato kamar ya shede shi a kan mallakar wani fili ko gida, ko ya wanke shi daga wani bashi, alhali bai ko tava ganinshi ba kafin yau a kotu. Turqashi!

Wannan ita ce tantagaryar qarya da Shedar Zur. Domin kuwa Allah Subhanahu Wa Ta’ala cewa ya yi a yi sheda a kan abin da aka sani:

ﭽ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﮘ ﮙ ﭼ يوسف: ٨١



Ma’ana:

Kuma bamu yi sheda ba face da abin da muka sani. Kuma bamu kasance masu kiyaye aibi ba. (12:38)


SAURAREN KIXA

Kaxe- kaxe da waqe- waqe a idon shari’ar musulunci na xauke hankalin masu yin su da sauraren su ne kawai daga tafarkin Allah Subhanahu Wa Ta’ala zuwa ga na shexan. A kan haka ne xan Mas’udu Raliyallahu Anhu yake rantsuwa da Allah Subhanahu Wa Ta’ala kan cewa ayar nan da ke cewa:

ﭽ ﭰ ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ ﭶ ﭷ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭽﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﮃ ﭼ لقمان: ٦

Ma’ana:

Kuma daga cikin mutane akwai wanda ke sayen tatsuniyoyi domin ya vatar da mutane daga hanyar Allah” (31;6).

Ya ce, wannan ayar tana magana ne a kan waqe- waqe. Haka kuma Abu Amiru da Abu Maliki al- Ash’ari Raliyallahu Anhuma sun qarfafa haramcin kixa da saurarensa, da hadisin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke cewa a cikinsa: “Za a samu wasu mutane a cikin al’ummata da ke halasta zina da tufafin al-Hariri da giya da kaxe-kaxe” (Bukhari 10/51). Haka kuma Anas Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Nan gaba za a sami girgizar qasa da aman duwatsu da shafe mutane su koma dabbobi a cikin al’ummata, sakamakon fara shan giya da sauraren waqe-waqen mata da kaxe-kaxen da za ayi” (Silsilah Sahiha 2203).

Ka ga kai tsaye Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya haramta kaxe-kaxe. Sai kuma bushe bushe irin na kusumburwa da Siriqi da sarewa duka sabgogi ne na bayyana qasaitar sarakuna da kambama su, amma dai ba shari’a ce ta zo da su ba. Sannan kuma malamai magabata irin su Imamu Ahmad Rahimahullahu Sun bayyana cewa, kayayyakin kaxe kaxe da bushe bushe, irin su garaya da Goge da Molo da kwamsa da duk masu kama da su, sun shiga cikin wannan harantawa da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi. Saboda mummunan tasirin da suke da shi ya ma fi na duk wasu kayan kixa da ake amfani da su a zamanin duhun kai, waxanda anka ambata a cikin wasu hadisai. Kai! Yadda wasu ma daga cikin su ke sa maye da annashawa ko giya albarka. Kamar yadda malamai irin su Ibnul Qayyim suka faxa.

Wannan haramci na qara tsanani da qamari lokacin da aka haxa waxannan kaxe kaxe da bushe bushe da goge goge, da muryoyin mata mawaqa. Uwa uba kuma idan waqoqin da suke yi xin suka qunshi kalaman bege da soyayya da qauna, da siffanta kyawon halitta. A irin haka malamai sun ce waqoqin na matuqar haramta, saboda suna share hanya ne zuwa ga alfasha. Suna kuma tsirar da munafucci a cikin zukata. A taqaice dai, kaxe- kaxe da waqe- waqe na daga cikin manya- manyan abubuwan da ke sa mutane na kutsa kai ga varnace varnace. Kuma ga shi raba mutane da su na da matuqar wahala saboda ci gaban zamani ya sakaxa su cikin abubuwan amfani da dama kamar Agogayyen hannu, qararrawar qofa, kayan wasan yara, Na’urori masu qwaqwalwa da Tarho- tarho da sauransu. Amma kuma kar a manta haramun ne. Allah Ya agaje mu.

TSEGUMI

Giba ko tsegumi na nufin yin maganar wani musulmi a kan wani abu da ba ya so a ji, ko da kuwa abin gaskiya ne. Wataqila abin ya shafi halittar jikinsa ne, ko irin riqonsa da addini, ko rayuwarsa ta yau da kullum, ko xabiunsa. Haka kuma tattauna wasu kurakurai na wani, ko kwaikwayon wata xabi’a tashi don a yi dariya duk na iya zama Giba.

Mafi yawan majalisu da wuraren haxuwar jama’a a yau sun zama dandalin tsegunguma da cin naman mutane, da keta alfarmar musulmi. Irin wannan xabi’a ko, na daga cikin abubuwan da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta ga bayinsa, ta hanyar kwatanta masu ita da wani abin da ko wace rayuwa ke qyama. Ya ce;

ﭽ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢﭣ ﭤ ﭥ ﭦ ﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫﭬ ﭭ ﭮﭼ الحجرات: ١٢



Ma’ana:

Kuma kada sashenku ya yi tsegumin sashe. Shin xayanku na son ya ci naman xan’uwansa yana matacce? Ba za ku so ba. Kuma ku ji tsoron Allah. (49:12)

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya fito wa musulmi da tantagaryar abin da wannan aya ke qoqarin cewa, akan haramcin tsegumi, inda ya ce wa Sahabbai: “Ko kun san abin da ake ce wa Giba (tsegumi)? Suka karva masa da cewa: “Allah da Manzonsa ne kawai suka sani”. Sai ya ce, Giba ita ce ka tsegunta wani abu a kan xan’uwanka, wanda kuma ba ya son a ji”. Sai kuma Sahabban suka sake tambayarsa da cewa: To, me kake gani da abin da aka faxa a kansa gaskiya ne? Sai ya ce masu: Idan abin da aka faxa a kansa gaskiya ne a lokacin giba ta tabbata. Idan kuwa ba gaskiya ba ne ya zama qazafi kenan”. (Muslim: 4/2001).

Mutane, musamman a yau, sun yi biris da wannan lamari, sun xauki Giba ba bakin komai ba. Alhali kuwa abu ce mai tsananin girma da haxari a wurin Allah kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayyana, cewa: “Riba nau’i Saba’in da biyu ce. Mafi qarancin zunubi daga cikinsu ita ce, wadda zunubinta ke daidai da na wanda ya yi jima’i da mahaifiyarsa. Mafi girmanta kuma ita ce wadda zunubinta ke daidai da na keta rigar mutuncin xan’uwa musulmi (cin namansa)” (Silsilah Sahiha: 1871).

Maganin wannan kuwa shi ne, kada mutum ya yi. Idan kuma yana zaune da mutane, suka sa faifan wani; suna sara da sassaqa to, ya yi qoqarin ba shi kariya mai tsafta. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya umurci Musulmi da yin haka inda yake cewa: “Duk wanda ya rufa wa xan’uwansa musulmi asiri, Allah zai tsare fuskarsa daga shiga wuta Ranar Qiyama” (Ahmad: 6/450).
GULMA

Gulma ita ce safa da marwa a tsakanin mutane, ana jekadancin maganganun sashen su zuwa ga sashe, da nufin tayar da wata fitina da haifar da qiyayya da gaba a tsakaninsu. Wannan xabi’a haramun ce. Kuma Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya la’anci waxanda duk ke yin ta. Ya ce:

ﭽ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﭼ القلم: ١٠ - ١١

Ma’ana:

Kada ka bi duk mai yawan rantsuwa, walakantacce. Mai zunxe, mai yawo da gulma. (69:10-11).

Haka kuma Huzaifata ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ke yawo da gulma ba ya shiga aljanna” (Bukhari: 10/472).

Haka kuma xan Abbas ya ce: “Wata rana Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya wuce kusa da wata maqabarta a Madina sai ya ji hargowar wasu mutane biyu, ana yi masu azaba a cikin qaburburansu. Sai ya ce: Ai ana yi masu azaba ne, amma ba don wani babban zunubi ba. Kai! Amma fa ko laifukan nasu manya ne. Saboda xayansu ba ya tsalki idan ya gama bauli. Xayan kuma yana yawo ne da gulma” (Bukhari 1/317).

Wannan kenan. To kuma mafi munin Gulma duk bata fi wadda zata haifar da matsala tsakanin mata da miji ba. Ko wadda za a tsegunta wa wani maigida abin da ma’aikatansa ke cewa, don a haifar da wata qullalliya tsakaninsu.

Gaba xayan waxannan xabi’u da ire-irensu haramun ne. Kuma nisantar su ya zama wajibi.


KWARMATO

Allah maxaukakin Sarki na cewa:

ﭽ ﯯ ﯰ ﯱ ﯲ ﯳ ﯴ ﯵ ﯶ ﯷ ﯸ ﯹ ﯺ ﯻﯼ ﯽ ﯾ ﯿ ﰀ ﰁ ﰂ ﭼ النور: ٢٧

Ma’ana:

Ya ku waxanda suka yi imani! Kada ku shiga gidajen da ba gidajenku ba, sai kun sami izini, kuma kuna yi wa masu su sallama” (24: 27).

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya warware zare da abawar wannan aya, da ya bayyana cewa an wajabta wa musulmi neman izni ne, kafin ya shiga gidan da ba nasa ba, don kada ya ga wani abin da ba a so ya gani. Manzon yace: “An gindaya neman izni ne don a kange gani” (Bukhari: 11/24).

Wannan mugunyar xabi’a ta kwarmato, ta zama ruwan dare tsakanin jama’a a waxannan kwanuka namu. Musamman idan gidajen mutane na kusa da juna ko ma suna xafe ta yadda qofofi da tagoginsu ke fuskantar juna. Sai ka taras maqwabta na amfani da wannan dama suna leqen cikin gidajen maqwabtansu a kai a kai, maimakon su riqa kau da kansu. A yayin da waxansu kuma da ke kan tudu kan mayar da leqen gidajen maqwabtansu da ke kware abin yi da gangan ta hanyar tagoginsu ko wani abu mai kama da haka. Ko Shakka babu wannan cin amana ne, kuma wuce iyaka ne a cikin haqqin da maqwabci ke da shi na walwala (privacy). Kuma wata hanya ce da ke zama sanadiyyar faruwar wasu abubuwa na haram masu yawa. A kan haka ne shari’ah ta xauki idon mai kwarmato ba bakin komai ba. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya leqa gidan wasu ba tare da izninsu ba, to ya halatta gare su su soke idaniyarsa xaya” (Muslim 3/1699).

A wata ruwayar ma cewa ya yi : “Su soke idaniyarsa, kuma ba diyya ba qisasi” (Ahmad: 2/385).
WARIYA

Wariya a nan na nufin kevancewar mutane biyu daga cikin uku don wata tattaunawa ta asiri. Wannan xabi’a ta zama kamar ado a cikin mutane alhali kuwa wata hanya ce da shaixan kan bi, ya raba kan musulmi, har a wayi gari wasu na qyamar wasu.

Wannan xabi’a haramun ce a shari’a, kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya bayyana irin hikimar da ke cikin haramcin ta da cewa, idan kuna ku uku, kada biyu su ware suna ganawa su bar xaya. Su bari har sai sun yawaita. Don kada xayan ya samu damuwa” (Bukhari: 11/83).

Sannan kuma wannan hukunci bai taqaita ga mutane biyu kawai ba. Ba ya halatta ko mutane uku su ware su bar xaya, na huxunsu, tilo. Haka haka. Abin da Shari’a ta haramta a nan a taqaice shi ne, warewa a bar mutum xaya, komai ko yawan waxanda suka ware xin. Haka kuma haramun ne mutane biyu su canza harshe suna magana da wani yare da na ukunsu ba ya fahimta. Domin ko shakka babu hakan zai sa ya ji ya tozarta. Kuma duk wanda kenan zai fahimci sun yi haka ne don su cuta masa a zuci, da sauransu.


JAN WANDO A QAS

Kalmar “Isbal” kalma ce ta Larabci wadda ke nufin sa wando dogo har ya wuce idon sau. Mutane a yau ba su xauki wannan xabi’a bakin komai ba. Alhali kuwa komai ce a wurin Allah. Domin kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce, a wani hadisi da Abu zarri ya riwaito: “Mutane uku Allah ba zai haxa baki da su ba gobe qiyama. Kai! Ko kallon rahama ba zai yi masu ba, balle Ya tsirar da su. Za su tabbata cikin azaba mai raxaxi. i) Wanda wandonsa ke wuce idon sawunsa, ii) wanda ke yi wa mutane gori da, iii) Wanda ke rantsuwa a kan qarya idan zai sayar da wani abu” (Muslim: 1/102).

An sami wasu mutane a yau da, idan aka yi masu tanbihi a kan wannan xabi’a sai su ce; Ai ba don wani alfahari ko taqama na sa wandona har ya wuce idon sau ba”. To, wannan Magana riya ce a kaikaice. Kuma ba karvavviya ba ce. Haramcin sanya wando har ya wuce idon sau, abu ne da ya haxe kowa. Wanda ya yi a kan fankama da alfahari da wanda bai yi a kan haka ba. Domin kuwa cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: “Duk abin da ya gota idon sau na wando rabon wuta ne” (Ahmad: 6/254).

Wannan shi ne hukuncin wanda ya yi Isbal ba don wata fankama da feshi ba. Kuma wanda ya yi haka Saboda girman kai da feshi da fankama, hukuncinsa ya fi tsanani. Don cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi: “Duk wanda ya zuba tufafinsa har suka ja qasa saboda girman kai, Allah ba zai dube shi da ijiyar rahama ba ranar qiyama (Bukhari: 3465).

Shari’ar ta tsananta hukunci ne a kan wannan saboda haxa hancin laifi biyu da ya yi a lokaci xaya, kuma a cikin mas’ala xaya wato zuba tufafi su wuce idon sau da kuma alfahari.

Kar ka yi mamakin shigowar “tufafi’ a cikin wannan magana domin xan Umar Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa: “Isbal” na iya tabbata ta hanyar gyafto (wando) ko riga ko rawani. Kuma duk wanda ya wuce iyaka da xayansu saboda alfahari da girman kai, Allah ba zai dube shi da ijiyar rahama ba a ranar qiyama. (Abu Dawuda: 4/353).

Amma kuma shari’ah ta yi rangwame ga mata, su tsawaita tufafinsu da misalin kamu xaya ko biyu, don gudun iska ya kaxa a hangi wani abu na jikinsu. Amma ba ya halatta su wuce haka. Kamar yadda wasunsu kan yi musamman a tufafin bukukuwansu na aure, waxanda keda doguwar geza a baya. Ta yadda har sai abokan amarya sun kama mata ita, ta baya.
QAWA DA ZINARI GA MAZA

Abu Musal Ash’ari Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Qawa da Siliki da zinari ta mata ce daga cikin al’ummata. Amma an haramta su ga maza (Ahmad:4/393).

Kasuwanninmu a yau cike suke da abubuwan amfani na maza, kamar: Agogayyen Hannu, da Tabarau, da Aninai, da Alqalumma da makamantansu, da aka qera da zinari mai daraja daban-daban, ko kuma aka yave qarfen na asali da shi. Agogayen hannu a yau su ne maza suka fi gasa da juna a cikin mallakarsu duk kuwa da kasancewarsu na zinari.

Xan Abbas Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ga wani namiji sanye da zoben zinari, nan take ya karve shi ya kuma yi jifa da shi, ya ce; “Ko akwai wani daga cikinku da zai iya xaukar garwashin wuta ya liqa ga hannunsa? (Yana nufin duk namijin da ya sanya zoben zinari kamar ya xauki garwashin wuta ne ya liqa a hannunsa) Da Manzon ya bayar da baya, sai wasu suka ba wancan mutumin shawarar ya xauki zobensa mana, ya ci gaba da amfani da shi (ta hanyar sayarwa ya amfana da kuxin) shi ko ya ce faufau, Wallahi tunda Manzon Allah ya karve shi ya yas ba ni ba shi (Muslim; 3/1655).


TSIRAICI

Wata hanya da maqiyan Musulunci ke bi suna kawo mana hare- haren ba zata a cikin siga ta zamani, ita ce hanyar qirqire-qirqiren salailai daban-daban na kayan ado ta fuskar xinke-xinke, waxanda kullu yaumin suke canza wa sanfari da sunan yayi, waxanda kuma aka wari gari sun sami mutaqar karvuwa a qasashenmu na musulumi.

Irin waxannan kaya ba sa rufe komai na jikin mace. Saboda kasancewarsu qanqana, Shar-shar kuma tani tani. Ta yadda bai kamata macen da ta san kunya ta saka su ko gaban mace ‘yar’uwarta, ko wani muharraminta ba. Balle wanda ba su ba. Amma kuma Alhamdu lillahi, da ma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya riga ya faxa mana irin haka za ta bayyana ga matan qarshen zamani. A wani hadisi da Abu Harairata Raliyallahu Anhu ya riwaito:”Akwai wani nau’i biyu na mutanen ‘yan wuta da za su bayyana can gaba: i) Wasu mutane da ke yawo da wasu manyan buloli masu kama da wutsan sanuwa sana bugun mutane da su, da ii) Wasu mata masu tafiya kamar tsirara suna kakkarya jiki, kansu kamar tozayen raqumma, a karkace. Da su da aljanna faufau. Kai ! ko qanshinta ba za su ji ba. Duk da yake ko wanda ke nisan wuri kaza da kaza yana jin sa (Muslim; 3/1680)

Irin waxannan mata, da dabi’unsu sun bayyana kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ambata, babu abin da ya rage mana illa mu nisance su.

Haka kuma irin waxannan tufafi na tsiraici sun haxa da irin dogayen rigunan da mata ke sakawa a yau masu tsage-tsage, da wasu yaggwai can qasa, ga su kuma da faxin. Ta yadda da macce ta zauna al’aurarta za ta bayyana a fili. Na farko kenan. Ga shi kuma ta yi koyi da kafirai, don su aka sani da irin waxannan kaya masu nuna tsiraici. Muna roqon Allah ya kiyashe mu.

Wasu tufafin Kuma da su ma, saka su tsiranci ne, ko da sun rufe jiki, su ne waxanda ke da miyagun hotunan da suka haxa da kamar: Hotunan Mawaqa da Nigogi (‘yan rawa), da kwalaben giya da hotunan dabbobi masu rai. Waxanda dukansu haramun ne a musulunci. Wasu kuma na xauke ne da hoton kuros ko Tamburran qungiyoyin asiri, ko dai wasu miyagun kalamai da ba su dace da duk wani mutum mai muruwa ba. Duk da yake wani lokacin muninsu ba zai bayyana ga waxanda ke sanye da kayan ba. Saboda an yi rubutun ne da wani yare na mutanen qetare.


SAJIN GASHI (Atacimen)

A idon Shari’ar musulunci, duk macen da za ta sadar da gashin kanta na asali da wanda ba na asali ba, daxa na kanta ne, ko wanda aka yanko daga jikin wata dabba kai tsaye kamar doki, to ta yi al-gussu. Algussu kuwa haramun ne.

Asma’u ‘yar Abubakar Raliyallahu Anha ta ce: “Wata mata ta zo wurin Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ta ce, Ya Manzon Allah, akwai wata ‘ya tawa da zan wanke jibi. Amma kafin yau ta yi wani xan zazzavi har gashin kanta ya zuba. Ko ina iya yi mata sajin gashi?’ Ya karva mata da cewa: A’a. Allah Ya la’anci duk wadda ta yi Sajin gashi da wadda aka yi ma shi (Muslim: 3/1676).

Haka kuma Jabiru xan Abudullahi ya ce: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya hana mace ta yi sajin wani abu ga kanta (Muslim: 3/1679).

A bisa dalilin waxannan hadisai, duk wani nau’i na sajin gashi da ake yi a yau a gidajen gyaran gashi na mata, ko wane irin nau’i ne, to haramun ne. Haka kuma hulunan gashi da wasu taurarin ‘yan wasa ke amfani da su a finafinai rashin tarbiyya ne, kuma haramun ne.
HARKAR ‘YAN DAUDU

Namiji ya yi qoqarin komawa mace, ko mace ta yi qoqarin komawa namiji ta hanyar kwaikwayon xabi’un juna, mummunar xabi’a ce a idon shari’ar musulunci.

A xabi’ance ma kamata ya yi namiji ya yi ta tattali da qoqarin tabbata namiji. Ita ma mace, ta yi nata tattali da qoqarin na tabbata mace. Don wannan shi ne abin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya shirya kowanen su a kai asalatan. Kuma qoqarin sava wa wannan tsari nasa na sa nagartattar rayuwa ta ‘yan adamtaka ta yi wuya a bayan qasa. Domin hakan zai sa amon rayuwar jama’a ya xauki wani salo irin na hatsin bara, wato wake-wake a komai.

Irin wannan xabi’a haramun ce. Dalili kuwa shi ne, a tsarin shari’ar musulunci, duk abin da aka ce Allah Ta’ala ko Manzonsa ya la’anci mai shi, to ya zama haramun ke nan.

Xan Abbas Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Allah Ya la’anci Maza masu kwaikwayon mata. Ya kuma la’anci mata masu kwaikwayon maza (Bukhari: 10/332). Haka kuma xan Abbas xin ya riwaito wani hadisin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke cewa a cikinsa: “Allah Ya la’anci mata maza, da maza mata (Bukhari: 10/333)

“Kama” da waxannan hadisai ke ta Magana, na iya kasancewa ta fuskar kwaikwayon kai da komowa, magana da tafiya. Haka kuma hadisan na tabbatar mana da cewa haramun ne xayan jinsunan nan biyu ya yi kama da xan uwansa, ta hanyar saka duk wani abu da, a xabi’a xaya jinsin aka sani da shi.

A kan haka haramun ne namiji ya xaura Sarqar wuya, ko ta hannu, ko ta qafa, ko ‘yan kunne da sauransu, kamar yadda fitsararru ke yi a Turai. Haka kuma haramun ne mace ta yi amfani da duk wani abu da a xabi’a na maza ne, kamar: Riguna da Jallabiyoyi, da sauransu. Abin da ma aka fi buqata a cikin ko wace al’umma shi ne tufafin mata ya sava da na maza kwatakwata. Domin Abu Hurairata ya riwaito wani hadisi da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke cewa a cikinsa: “Allah Ya la’anci namijin da ke sa kayan maza, da macen da ke sa kayan mata (Abu Dawuda: 4/355).

BUDURWAR ZUCIYA

Buduruwar Zuciya a wannan babi, na nufin duk wani yunquri da wanda shekarunsa suka miqa zai yi don canza wata halittar Haliqu a jikinsa kamar hurhura, ta hanyar yi mata baqar garura, don ya koma layin matasa.

Nagartaccen ra’ayi na malaman Sunnah ya tafi a kan cewa, irin wannan Sabga haramun ce. Saboda wani nau’i ne na Al-gussu. Kuma an dace da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya hani musulmi xabi’ar a cikin wani hadisi da ke cewa: “Za a yi wasu mutane a qarshen zamani da za su riqa ture farin gashinsu da baqar garura har ya riqa walqiya kamar gaban baqar tantabara. To, ko qanshin aljanna ba za su ji ba. (Abu Dawuda).

Irin wannan sabga ta yawaita matuqa ga mutanen da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi wa ni’imar farin gashi tun suna da qurciya ko waxanda mutuwa ta fara barbaxa wa gishiri. Wanda hakan ke yaudarar mutane, ta hanyar mayar da tsoho yaro ko kuma tsohuwa ta koma yarinya. Ka ga an mayar da gaskiya qarya kenan.

Ba tura farin gashi ya koma wata kala ne haramun a shari’ar musulunci ba. A’a, ture shi ya koma baqi ne haramun. Saboda ai, ta tabbata Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na shafa wa farin gashinsa lalle, ya koma ja- ja- ja ko qasa –qasa. Abin ma bai tsaya ga shi ya yi wa kansa ba, har umurni ya yi da haka. Don a lokacin da aka ci garin Makka da yaqi, aka zo da Abu quhafata (Mahaifin Halifa Abubakar) don su gaisa. Ya ga gemu da sajensa irin na dattijai, ya yi fari kamar auduga sai Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Ku suturta wannan farin gashi da yi masa turi. Amma kada ku sa baqi (Muslim:3/1663).

Wannan hukunci na haramcin ture gashi ya koma baqi, ya haxa maza da mata. Amma su ma, suna iya yin wata kalar.


ADO DA HOTUNAN ABU MAI RAI

Abdullahi xan Mas’udu Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Mutanen da za su haxu da azaba mafi tsanani Ranar qiyama su ne masu sassaqa gumaka (Bukhari: 10/382).

Haka kuma Abu Harairata ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Allah Ta’ala Ya ce, “Babu wanda ya kai shisshigin wanda ke qoqarin yin halitta irin tawa. In gaskiya ne ya halitta gero da alkama mu gani (Bukhari: 10/385). Kuma xan Abbas Raliyallahu Anhu ya ce wani hadisi da ya karvo daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama: “Za a saka wa ko wane gunki da mutum ya sassaqa rai daga ran wanda ya sassaqa shi, a yi ta azabtar da shi a cikin wutar Jahannama”. Ya kuma qara da cewa: “Wanda ko duk sassaqa ta zamo sana’arsa, to, ya tsaya ga sassaqa itace, ko wani abu maras rai” (Muslim: 3/1671).

Ka ga kai tsaye, waxannan hadisai, sun haramta sassaqa hotuna ko zana su ko xaukar hoton su matuqar dai na ababe masu rai ne.

Tunda kuwa haka ne, ya zama wajibi a kan duk wani musulmi na qwarai ya karvi wannan hukunci da shari’ah ta yi da hannu biyu- biyu, ba tare da wata jayayya ba. Duk da yake wasu na iya kafa hujja da cewa, “Eh! To ai, mu ba bauta wa waxannan hotuna muke yi ba, don ba sujada muke yi musu ba”.

Amma kuma duk mai hankalin da ya dubi wannan matsala da idon basira zai tsinkayo tare da fahimtar irin hikimar da haramta irin waxannan abubuwa ta qunsa. Saboda mafi yawan ayyukan fitsara na faruwa ne ta hanyar hotuna. Musamman zinace-zinace. Domin ta hanyar kallace-kallacen hotunan banza ne qwazaba ke toroqo da bululluqai, daga nan har a kai ga varna.

Bisa wannan dalili ne ma, mala’ikun rahama ke qaurace wa duk wani gida da ake ajiye hotuna a cikinsa. Kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Mala’ikun Rahama ba su shiga duk wani gida da ke akwai kare a cikinsa ko hotuna (Bukhari: 10/380).

Wani abin mamaki da xaure kai shi ne, duk da wannan haramci, mutane a yau musamman masu hannu da shuni, ba su fasa aje gumakan wasu dabbobi ba, kai har da na mutane, a cikin gidajensu da sunan qawa ko ado. Alhali kuwa akwai wasu mutane da ke bauta wa wasu daga cikin waxannan abubuwa.

To, haramcin abubuwa irin waxannan ya fi qamari da tsanani. Sannan sauran hotunan da ake ratayewa na mutane da wasu dabbobi na bi masu. Qarshe kuma waxanda ba rataye su ake yi ba suna bi masu a haranci. Domin da yawa Sukan sa waxanda suka aje su, girmama su, da sabunta juyayi da jimami a cikin zukatansu. Duk da yake wasu mutane kan kafa hujja da cewa Suna aje hotunan mutanen ne, da suka haxa da na uwayensu ko shugabanni ko malamansu, ko masoyansu ko wasu gwaraje da suke ganin bajintar su ko suke sha’awarsu, don tunawa da su. Alhali kuwa ita tunawa da wani abu a zuciya ake yin ta. Ba sai da hoto ko mutum mutumi ba. Kuma mafi kyawon tunawa da mutum, bayan ya qaura, ita ce, idan ya faxo a zuciyar wani nasa, to ya yi masa kyakkyawar addu’a, ta hanyar roqa masa gafara da Rahamar Allah Subhanahu Wa Ta’ala.

Saboda haka, babu wani musulmi da ke da wani uzuri na aje wani hoto a xakinsa ko liqa shi a jikin bango ko abin hawansa. Lalle ne ya yi waje da duk wani hoto ko mutum mutumi na mutum ko dabba da ke gidansa. Sai fa idan hakan ta gagara. Balle kuwa ba zata gagara ba.

Hotuna irin waxanda ke jikin gwangwanaye da kwalayen abinci, waxanda ba makawa sai musulmi sun yi ta’amuli da su, ko waxanda ke cikin wasu littafai na karatu. Ana so mutum ya yi iyakar qoqarinsa na ganin ba su zame masa allaqaqai ba.

Babu laifi idan an aje hotuna irin waxanda babu makawa sai an aje su, kamar waxanda ake maqalawa ga takardun shedar qare karatu ko katin sheda, ko lasisi, ko irin waxanda ke saqe a kan dardumai.

Allah Subhanahu Wa Ta’ala na cewa:

ﭽ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﭼ التغابن: ١٦

Sai ku bi Allah da taqawa gwargwadon abin da kuka sami iko: (64:16).

1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət