Ana səhifə

Gyara kayanka yi hattara da


Yüklə 401 Kb.
səhifə8/12
tarix26.06.2016
ölçüsü401 Kb.
1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12

RASHIN KULA DA TARBIYYAR IYALI


Da gangan, a zamaninmu na yau, wasu magidanta ke yin biris da tarbiyyar iyalinsu, musamman ‘ya’ya mata. Ta hanyar sa masu ido suna cuxanya da mazajen da ba su halatta gare su ba. Suna cika masu kunnuwa da zukata da maganganun soyayya. Abu mafi muni ma, wasu magidanta har matansu na aure suke ba irin wannan dama. Ko kuma iyalin nasu su kaxaita da wani ajanabi daga cikin direbobinsu ko masu yi masu hidima. A yayin da wasu yaran ma, irin wannan sakaci na mahaifansu, kan ba su cikakkar dammar fita ba da nagartaccen hijabi ba, ta yadda kowa zai iya gane su. Wasu daga cikinsu kuma ma har mujallu da finafinan batsa suke kawowa a gidajen babu ma ice masu kul.

Irin waxannan magidanta na fuskantar babban haxari gobe qiyama. Saboda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Akwai waxansu mutane uku da Allah Ya haramta wa aljanna: 1) Mashayin giya, 2) Maras biyayya ga uwaye, da 3) Wanda ba ya kula da tarbiyar iyalinsa” (Ahmad: 2/69).


GURVATA ZURI’A


Gurvata zuri’a da yamutsa hazonta na xaya daga cikin abubuwan da shari’ar musulunci ta haramta.

Bai halatta ba a musulunci, mutum ya danganta kansa ga wani a matsayin mahaifi, savanin ubansa wanda ya haife shi da cikinsa. Ko ya yi qaryar zama xan wata qabila wadda ba tasa ba.

Wasu mutane kan yi waxannan qaryace-qaryace ne, da guje wa danginsu, na asali don kawai neman abin duniya. A qoqarin haka ma har takardun sheda sukan nema don xaure wa qaryar tasu gindi a hukumance.

A yayin da kuma wasu uwaye su kan zama sanadiyyar ‘ya’yansu su xauki irin wannan mataki, idan suka yi watsi da su tun suna qanana. Su ma irin waxannan uwaye sun aikata haram. Domin irin wannan aiki nasu ka iya gurvata zuri’a kwatakwata. Ta hanyar kawo tajin-tajin da fitsara ta hanyoyi daban-daban. Kamar kasa gane wanda yake muharrami ga wani. Wanda a sanadiyyar haka za a yi ta kabra da kai a cikin auratayya da gado, da wasu matsaloli masu kama da wannan. Kuma ga shi Sa’adu da Abubakar Raliyallahu Anhuma sun riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya danganta kansa ga wanda ba mahaifinsa ba da gangan, ba zai shiga aljanna ba” (Bukhari: 8/45).

Haka kuma haramun ne a shari’ah, a gurvata ma mutum asali, a qashin kansa ko abin da ya haifa. Kamar abin da wasu mazaje ke yi, idan suna son yi wa matansu ciwon baki, a yayin da wata ‘yar hayaniya ta haxa su. Sai kawai su yi masu qazafin alfasha, ko su kore ‘ya’yansu daga zama nasu. Alhali kuma ba su da wani qwaqqwaran dalili a kan haka. Domin kuwa ko gadajensu na kwana na shedar cewa ‘ya’yan jininsu ne ba inki ba wai.

A xaya vangaren kuma akwai wasu fanfararrun mata, dakarai da ke gurvata zuri’ar musulmi ta hanyar cin amanar da ke tsakaninsu da mazajen su, su yo ciki da wasu mazan daban su liqa masu ‘ya’yan.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi gargaxi da hani akan wannan xabi’a. Abu Hurairata Raliyallahu Anhu ya riwaito, cewa a lokacin da ayar li’ani ta sauko, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk matar da ta kawo wani baqon haure a cikin wata zuri’a, to ta yi bankwana da Allah. Shi kuma ya yi bankwana da ita. Kuma ko labarin aljannarsa ba zata ji ba. Haka Shi ma duk namijin da ya kore xansa daga zama nasa, shi ma Allah zai yi hushi da shi, Ya kuma tona masa asiri kowa ya gama da ganinsa” (Abu Dauda: 2/695).

RIBA


Riba na xaya daga cikin manyan laifukan da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta. Saboda ma girman sha'aninta ne, ta zama abu xaya qwal, da Allah Ta'ala Ya shelanta yaqi da masu shi, a cikin alqur'ani. Inda Yake cewa:

ﭽ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛﯜ ﭼ البقرة: ٢٧٨ - ٢٧٩



Ma’ana:

Ya ku waxanda suka yi imani! Ku bi Allah da taqawa kuma ku bar abin da ya rage daga riba, idan kun kasance masu imani. Idan ko ba ku aikata ba, to, ku sani akwai yaqi daga Allah da Manzonsa” (2:278-279).

Ko shakka babu wannan gargaxi da Allah Maxaukakin Sarki Ya yi, ya ishi ko wane mutum musulmi gane irin yadda Allah Ya xauki mai cin riba. Kuma duk mai hankali zai iya gano mugun tasirin da Riba ke da shi, a rayuwar xaixaiku da ta al’umma. Irin yadda wasu mutane suka zama turayen bashi, ta yadda ko shexa sai da qyar suke yi, matsalolin tattalin arziki, yawan rashin aikin yi, durqushewar kanfunna, da ma’aikatu, duk waxannan na daga cikin ayubban da Riba ta haifar a duniya.

Kai! Dubi irin yadda wasu mutane ba su da aikin yi kullum sai fama da baqin cikin yadda za su yi su biya kuxin ruwan da ke yi masu ambaliya na bankuna. Kuma aka wayi gari al’umma ta kasu gida biyu, ‘yan Bora da na Mowa, saboda irin yadda ‘yan tsirarun suka mallake mafi yawan arziqin qasa. Kuma irin waxannan matsalolin kusan na daga cikin nau’o’an yaqin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya sha alwashin gwabza wa da duk al’ummar da ke mu’amala da Riba. Domin kuwa aiwatar da Riba ba zai yiwu ba, sai da sa hannun vangaroran mutane da dama, har su talakawan.

Bayan wannan kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya la’anci duk wanda ke da hannu ko masosa a cikin aiwatar da wannan haramiya. Daxa ko jigon hulxar ne ko jekada ko xan dako. Jabir Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa: Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “…wanda ke cin riba da wanda ke bayar da ita, da wanda ke rubuta ta da wanda ke sheda duk uwarsu xaya ubansu xaya” (Muslim: 3/1219).

A kan wannan nagana ta Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke nan, haramun ne ga mutum musulmi ya yi ko wane aiki, matuqar dai yana da alaqa ta qud-da- qud da Riba. Wato kamar ya zama magatakardan wasu kanfunna da ke ta’amuli na Riba. Ko ya zama mai karva ko bayar da ita, ko kai saqonta ko gadinta. Wato a taqaice, haramun ne mutum ya kasance yana da wata alaqa ta kai tsaye ko ta kaikaice da Riba.

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yayi matuqar bayyanawa al’ummarsa munin Riba. Yana cewa a wani hadisi da Abdullahi xan Mas’udu Raliyallahu Anhu ya riwaito: “Akwai Riba nau’i saba’in da uku. Mafi sauqi daga cikinsu ita ce wadda zunubinta yake daidai da na wanda ya tara da mahaifiyarsa. Mafi girmanta kuma ita ce wadda zunubinta yake daidai da na wanda ya keta alfarmar musulmi” (Hakim: 2/37).

Haka kuma Abdullahi xan Hanzalata Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Cin dirhami xaya ta hanyar Riba da gangan, ya fi zunubi a kan yin zina har sau talatin da shida” (Ahmad: 5/225).

Wani kuma abin da ya kamata a lura da shi shine, haramcin mu’amala da Riba bai taqaita tsakanin “Ni da kai” ba, kamar yadda wasu mutane ke zato. A’a, haramcinta, haramci ne na game gari. Ya shafi mutane baki xaya a matsayinsu na xaixaiku ko kamfuna ko ma’aikatu da sauransu.

Manyan mutane kuma hamshaqan ‘yan kasuwa waxanda Riba ta zama ajalinsu, ta fuskar ma’amalar kuxi da bankuna da manyan kanfanoni, ba su da iyaka. Dole ne al’ amarin ya zama haka. Kuma ba wani mamaki a ciki. Domin kwashe albarkar dukiya da lalata ta shi ne bala’i mafi qaranci da Riba ke haifarwa. Kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk yadda dukiyar Riba ta yawaita qarshenta rashi” (Hakim: 2/37).

Kuma wannan mummunan qarshe da dukiyar Riba zata yi, ba wai sai an tara ta da yawa ba. Ko da ‘yar kaxan ce, to, ta haramta. Kuma Allah Subhanahu Wa Ta’ala zai tayar da duk wanda ke ma’amala da ita, Ranar qiyama kamar wanda ya sha banjo, ko wanda shexan ya yi sukuwar sallah a kansa.

Amma kuma a cikin rahamar Allah, duk irin wannan matsala da ke tattare da Riba, Sarkin bai bar mu da ita ba. Sai da Ya faxa mana yadda wanda ya faxa cikinta zai yi ya kuvuta. Ga abin da Yake cewa:

ﭽ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦ ﭼ البقرة: ٢٧٩

Ma’ana:

Kuma idan kun tuba, to, kuna da asalin dukiyoyinku (uwar kuxi) ba zaku zalunta ba, kuma ba za a zaluntar ku ba” (2:279).

Wannan shi ne tantagaryar adalci; Kuma a kan haka wajibi ne duk musulmi ya nisanci wannan babban zunubi, ya kuma yi imani da cewa mu’amalar haramun ce. Koda kuwa dole ta sa ya kai kuxin ajiya a wani banki da ke irin wannan mu’amala ta Riba, to kada ya kuskura ya ji cewa hakan ta halasta. Kuma idan ba don tsoron kuxin nasa su halaka ta hanyar sacewa ko wata qaddara ba, to bai halatta ya kai ajiya a irin waxannan bankuna ba. Kuma lalle ne idan haka ta faru ya xauki kansa matsayin wanda tsananin yunwa ya sa cin naman mushe, ko wani laifi fiye da shi, kuma a lokaci xaya wajibi ne a tsare istigfari tare da qoqarin neman wata hanya ta halas da zai adana dukiyarsa ta ita. Yin hakan wajibi ne a kansa matuqar yana da iko.

Wani abun kuma shi ne da Allah zai sa bankin ya kasa saka masa nasa kaso na Ribar a cikin uwar kuxinsa, to ba ya halatta gare shi ya bi kadinta balle ya qalubalance su. Idan kuma ya tarar cewa sun saka masa baki alaikum, to lalle ne ya gaggauta sanin yadda ya yi da su. Ba ya halatta ya yi sadaqa da su. Ko ya yi kuma, Allah ba zai karva ba. Don shi mai tsarki ne, ba Ya kuma karvar abinda ba mai tsarki ba. Haka kuma, ba ya kamata ya yi amfani da kuxin ruwan nan ya ciyar da iyalinsa, ko ya shayar da su, ko ya yi masu sutura, ko ya saya masu abun hawa ko wani sabon gida. Haka kuma ba ya halatta ya cika wani alkawali da ya yi da kuxin, ga matarsa ko xansa ko mahaifiyarsa, ko ya yi zakka ko ya biya haraji da su, ko ya kare kansa da su a kotu.

A taqaice dai, ba ya halasta gare shi shi, ya yi amfani da waxannan kuxi ta ko wane hali. Magani shi ne, ya xaure hannunsa da dutse daga gare su, don ya tsira daga azabar Allah.

1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət