Ana səhifə

Gyara kayanka yi hattara da


Yüklə 401 Kb.
səhifə1/12
tarix26.06.2016
ölçüsü401 Kb.
  1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12


ترجمة كتاب محرمات استهان الناس بها

للشيخ صالح المنجد بلغة الهوسا

ترجمه: محمد المنصور إبراهيم وعلي رفاعي غسو

GYARA KAYANKA

YI HATTARA DA

ZUNUBAI 70

Waxanda Mutane Suka Yi Biris Da Su

WALLAFAR

SHEIKH MUHAMMAD SALEH AL MUNAJJID


FASSARAR

MUHAMMAD MANSUR IBRAHIM

Jami’ar Usmanu Xan Fodiyo, Sokoto

DA


ALIYU RUFA’i GUSAU

Ma’aikatar Lamurran Addini ta Jihar Zamfara


Xaukar Nauyin Bugawa

Xan Rinin Sakkwato, Alhaji Habibu Halilu Modachi



ABUBUWAN DA KE CIKI

Gabatarwar masu fassara: ………………………………………………….


Gabatarwar mawallafi: ……………………………………………………..

BABI NA XAYA:

Shirka: ……………………………………………………………………..

Bautar Qaburbura: …………………………………………………………

Yanka Don Wanin Allah: …………………………………………………

Halasta Abin Da Allah Ya Haramta: ……………………………………..

Sihiri, Bayar Da Sa’a Da Faxin Gaibi: ……………………………………

Imani da Taurari: …………………………………………………………

Imani da Tasirin Wani Abu : …………………………………………….

Riya: ……………………………………………………………………..

Camfi: ……………………………………………………………………

Rantsuwa da Wanin Allah: ………………………………………………

BABI NA BIYU

Zama da Munafukai da Mavarnata: ………………………………………


Rashin Natsuwa a cikin Sallah: …………………………………………..

Karauniya a Cikin Sallah: ………………………………………………..

Shiga Gaban Liman a Cikin Sallah da Gangan: ………………………….

Zuwa Masallaci Da Warin Albasa Ko Tafarnuwa: ………………………

Zina: ………………………………………………………………………

Luwaxi: …………………………………………………………………...

Neman Saki: ………………………………………………………………

Zihari: …………………………………………………………………….

Jima’i Lokacin Haila: ………………………………………………….....

Zo wa Mace ta Baya: ……………………………………………………..

Rashin Adalci Tsakanin Matan Aure : ……………………………………

Kaxaita da Matar da ba Muharrama ba: ………………………………….

Gama Hannu da Mata: ……………………………………………………

Shafa Turare Ga Mata Lokacin Fita: ……………………………………..

Tafiyar Mace ba Tare da Muharrami ba: …………………………………

Kallon Wanda ba Muharrami ba da Gangan: …………………………….

Rashin kula da Tarbiyar Iyali: ……………………………………………

Gurvata Zuri’a: ……………………………………………………………

Riba: ………………………………………………………………………

Algussu: …………………………………………………………………..

Keri: ………………………………………………………………………

Ciniki Bayan Kiran Sallar Juma’a: ……………………………………….

Sata: ………………………………………………………………………

Cin Hanci: ………………………………………………………………..

Qwacen Filin qasa: ……………………………………………………….

Ci Da Ceto: ……………………………………………………………….

Canye Haqqin Ma’aikata: ………………………………………………..

Rashin Adalci Tsakanin ‘Ya’ya: …………………………………………

Roqo Ba Buqata: …………………………………………………………

Turun Bashi: ………………………………………………………………

Cin Dukiyar Haram: ………………………………………………………

Shan Barasa: ……………………………………………………………..

Amfani Da Kasaken Zinari Da Na Azurfa: ………………………………

Shedar Zur: ……………………………………………………………….

Sauraren Kixa: ……………………………………………………………

Tsegumi: ………………………………………………………………….

Gulma: ……………………………………………………………………

Kwarmato: ………………………………………………………………..

Wariya: ……………………………………………………………………

Jan Sutura A Qasa Ga Maza: ……………………………………………..

Qawa da Zinari Ga Maza: ………………………………………………..

Tsiraici: …………………………………………………………………..

Sajin Suma Ga Mata: …………………………………………………….

Harkar ‘Yan Daudu: ……………………………………………………..

Budurwar Zuciya: ………………………………………………………..

Ado da Hotunan Abu Mai Rai: …………………………………………

Qaryar Mafarki: ………………………………………………………...

Tozarta Qaburbura: ……………………………………………………..

Raggon Tsarki: ………………………………………………………….

Tsince: …………………………………………………………………..

Cutar da Maqwabci: …………………………………………………….

Taushe Haqqin Maraya: …………………………………………………

Dara: ……………………………………………………………………..

La’antar Musulmi: ……………………………………………………….

Kukan Mutuwa Da Hargowa: ……………………………………………

Mari da Tsaga: …………………..............................................................

Gaba: ……………………………………………………………………..

Kammalawa: ………………………………………………..



GABATARWAR MASU FASSARA

Godiya ta tabbata ga Allah. Tsira da aminci su daxa tabbata akan shugaban talikai.

Faxakarwa dangane da iyakoki da dokokin Ubangiji Mahalicci na daga cikin abin da musulmi ke da buqatarsa a ko wane lokaci, to, balle kuma a wannan zamani namu da yake cike da abubuwan xaukar hankali masu kawar da mutum daga godaben Shari’a.

To, sai dai ba kowa ne yake amfanuwa da wannan faxakarwar ba sai wanda imani ya ratsa birnin zuciyarsa. Kamar yadda Allah ya ce;

ﭽ ﭭ ﭮ ﭯ ﭰ ﭱ ﭲ ﭼ الذاريات: ٥٥

Ma’ana:

“Ka faxakar domin, faxakarwa tana amfanin Muminai”.

Suratuz Dhariayt: 55

Wannan littafi na Sheikh Muhammad Saleh Al Munajjid yana da matuqar muhimmanci ta wannan fuskar. Shi ya sa muka ga dacewar mayar da shi zuwa harshen Hausa.

Roqon da muke ga Allah maxaukakin Sarki yasa mu cikin farko waxanda ke aiki da wannan faxakarwa. Ya bamu ladar wannan aikin, ya sanya shi cikin sikelin ayyukan alherinmu. Ya yafe mana duk wani kuskure ko tuntuven harshe ko varin baki idan auku a cikin aikinmu.

Masu Fassara:

Muhammad Mansur Ibrahim

Da Aliyu Rufa’i Gusau



GABATARWAR MAWALLAFI

Godiya ta tabbata ga Allah, Abin yabo, Abin nufi da buqata. Wanda muke neman gafararsa, muke kuma fatar Ya yi mana katangar dutse, a tsakanin mu da sharrin zukatanmu da miyagun ayyukanmu. Tabbas! Duk wanda Allah ya shiryar babu mai vatar da shi. Babu kuma mai iya shiryar da wanda Allah bai nufa da shiriya ba. Na Shaida, ba abin bauta wa da gaskiya Sai Allah, Shi kaxai, ba shi da abokin tarayya. Ina kuma shedar da cewa Muhammadu bawansa ne kuma manzonsa.

Bayan haka:

Tabbataccen abu ne cewa, Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya wajabta wasu abubuwa a kan mu, waxanda yin biris da su ba ya halasta. Ya kuma haramta mana wasu abubuwan, waxanda su ma, yi masu kallon hadarin kaji ba daidai ne ba. Allah a cikin ikonsa ya shimfixa mana wasu dokoki ya shata wasu iyakoki da ba ya son a tsallake su.

A qoqarin fitowa da matsayin waxannan abubuwa biyu ne da kuma abin da ke tsakanin su, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce:

“Duk abin da Allah Ya halasta a cikin littafinsa shi ne halas. Babu kuma wani abu da ke haram, sai abin da Ya haramta. Duk kuma abin da bai ce komai a kansa ba to garavasa ne. Ku karvi wannan rangwame na Allah da hannu biyu biyu. Don har abada Allah ba Ya mantuwa”. Daga nan kuma, sai ya karanta wannan aya:

ﭽ ﰖ ﰗ ﰘ ﰙ ﰚ ﭼ مريم: ٦٤

Ma’ana:

Kuma Ubangijinka bai kasance mai yin mantuwa ba (19:64).

Da wannan bayani na Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ne, ta bayyana cewa, duk abubuwan da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi wa bayinsa iyaka da su, su ne haram. Kuma yin biris da su zaluntar kai ne. Allah Subhanahu Wa Ta’ala na cewa:

ﭽ ﭯ ﭰ ﭱ ﭲ ﭳ ﭴ ﭵ ﭼ الطلاق: ١



Ma’ana:

Kuma wanda ya qetare iyakokin Allah to lalle ya zalunci kansa (65:1).

Bayan wannan kuma sai Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi tanadin wuta ga duk wanda ya qetare waxannan iyakoki da Ya shata. Ya ce:

ﭽ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰ ﯱ ﯲ ﯳ ﯴ ﯵ ﯶ ﯷ ﯸ ﭼ النساء: ١٤



Ma’ana:

Kuma wanda ya sava wa Allah da manzonsa, ya kuma qetara iyakokinsa, zai shigar da shi wuta, yana madawwami a cikin ta, yana kuma da wata azaba mai walaqantarwa (4:14).

Saboda irin qaunar da Allah Subhanahu Wa Ta’ala ke yi wa bayinsa kuma, sai ya wajabta masu nisantar waxannan abubuwa ta hanyar haramta masu su. Don kada su faxa cikin wannan azaba. A kan haka, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama Ya ce:

“Duk abin da na hane ku da shi, ku nisance shi. Abin da kuma duk na umurce ku da shi, ku aikata shi gwargwadon ikonku”. (Muslim: 130) .

Amma tattare da wannan irin gatanci, sai ka taras da waxanda suka saba da biyar soye-soyen zukatansu, saboda raunin imani da qarancin ilmi da suke da su, suna qorafe-qorafe. Da zarar an ce masu abu kaza da kaza haramun ne a musulunci, sai su fara gunguni suna cewa: “Kome dai haramun! Haramun!! Haramun!!! Wai wane irin addini ne wannan da kullum yake qoqarin gasa mana aya a hannu? Kai kun dai ishe mu. Ku ba ku da wata magana sai ta haram! Ai kamata ya yi addinin musulunci ya zama kadaura babbar inwa, mayalwanciya, wurin hutawa, ba aljannar masa ba. Kuma shin ko kun manta da cewa Allah Mai rahama ne, kuma Mai jinqai?”

Irin waxannan mutane yana da kyau su sani cewa, Allah Subhanahu Wa Ta’ala Sarki ne mai cikakken iko. Wanda ke gudanar da mulkinsa yadda Ya so, kuma babu wanda ya isa ya tayar da wani hukunci da Ya yi. Domin Ilminsa da hikimarsa sun kai matuqa. Yana halasta abin da Ya ga damar halastawa, Ya kuma haramta abin da Ya ga dama. Kuma mu, yana xaya daga cikin abubuwan da ke tabbatar da kasancewarmu bayinsa na gari, mu yarda da duk wata doka da zai shata muna; mu miqa wuya gare ta. Domin babu wata doka da zai yi face tana tsattsage da ilimi da hikima da adalcinsa. Ba abu ne na sakarci da sharholiya ba. Kamar yadda Allah Yake cewa:

ﭽ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮﮯ ﮰ ﮱ ﯓﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﭼ الأنعام: ١١٥

Ma’ana:

Kuma kalmar Ubangijinka ta cika, tana mai gaskiya da adalci. Babu mai musanyawa ga kalmominsa, kuma shi, Mai ji ne, Masani (6:115).

Wani abun kuma shi ne: Allah Subhanahu Wa Ta’ala a cikin wannan ilimi da hikima nasa, bai tsaya kawai ga halasta mana wasu abubuwa da haramta mana wasu ba. Sai da ya bayyana mana qa’idar da Yake bi a cikin yin haka. Dubi inda Yake cewa:

ﭽ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﭼ الأعراف: ١٥٧



Ma’ana:

Kuma Yana halatta masu abubuwa masu tsarki (waxanda suka shafi, Aqida da ibada da Mu’amala da Ababen ci, da saurasu). Yana kuma haramta masu qazantattun abubuwa. (7:157).

Ashe kenan Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya halatta mana wasu abubuwa ne saboda kasancewarsu masu tsarki. Ya kuma haramta mana wasu ne, saboda qazantar da suke da ita. Kuma irin wannan iko, na ware wani abu a ce halas ne, ko a ware wani a ce haram ne, Allah Subhanahu Wa Ta’ala ne kawai ke da shi. Kuma ko shakka babu, duk wanda ya naxa wa kansa irin wannan rawani, ko ya naxa wa wani, ya tabbata kafiri. Kafirci kuwa, laifi ne da babu kamar sa. Kamar yadda Allah Subhanahu Wa Ta’ala ke cewa.

ﭽ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﯙ ﭼ الشورى: ٢١



Ma’ana:

Ko suna da waxansu abokan tarayya (da Allah) waxanda ke shar’anta masu, abin da Allah bai yi izini da shi ba game da addini? (42:21).

Ba wannan kawai ba. Babu ma wanda Shari’a ta yarda ya tsoma baki, a cikin yin sharhi a kan kasancewar wani abu halas ne ko haram, face mutumin da ya naqalci asirin Alqura’ani da Sunnah. Saboda nauyin wannan al’amari ne ma, Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi kashedi da kakkausar murya, a kan masu wanke baki su tsoma, a zancen halas da haram, alhali iliminsu bai taka kara ya karya ba. Saurari wannan aya kuma ka kalle ta da idon basira:

ﭽ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﯙﯚ ﯛ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﭼ النحل: ١١٦



Ma’ana:

Kuma kada ku ce, wannan halas ne, wannan haram ne akan abin da harsunanku suke siffantawa na qarya. Domin ku qirqira qarya ga Allah. Lalle waxanda ke qirqira qarya ga Allah ba su rabauta. (16:116).

Kuma Saboda girman wannan mas’ala ne, da kariya ga alfarmarta, tare da tsare mutuncin musulmi, Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya qididdige abubuwan da aka daddale haramcin su cikin Alqur’ani, Sunnah kuma ta tunfaye su. Ga abin da Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce:

ﭽ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘﯙ ﯚ ﯛ ﯜ ﯝﯞ ﯟ ﯠﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥ ﯦﯧ ﯨ ﯩ ﯪﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰ ﯱ ﯲ ﯳﯴ ﯵ ﯶ ﯷ ﯸ ﯹ ﯺ ﯻ ﯼﯽ ﯾ ﯿ ﰀ ﰁ ﰂ ﰃ ﭼ الأنعام: ١٥١



Ma’ana:

Ka ce “ku zo in karanta abubuwan da Ubangijinku Ya haramta a kan ku: (Wajibi ne) kada ku yi Shirkan kome da shi, kuma ku kyautata wa mahaifa, kuma kada ku kashe xiyanku saboda talauci, Mu ne muke arzuta ku, da su, kuma kada ku kusanci abubuwan alfasha; abin da ya bayyana daga gare ta da abin da ya voyu, kada ku kashe rai wadda Allah Ya haramta, face da haqqi. Wannan ne (Allah) Ya yi muku wasiyya da shi, ko da zaku hankalta (6:151).

Bayan wannan kuma, Sunnah ta zo da qididdigar wasu haramtaccin abubuwa masu yawa. Kamar inda manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke cewa: Haqiqa Allah Ya haramta cinikin giya, da mushe da naman alade da kuma gumaka (Abu Dawud: 3:486).

Ya kuma ce: Duk abin da Allah Ya haramta, to kuxinsa haramun ne (Daraquxni: 3/7).

Bayan duk wannan kuma, akwai waxansu ayoyi da suka ambaci wasu haramtattun abubuwa, a matsayinsu na qungiya; ‘yan uwa xaya uba xaya. Kamar inda Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta wasu nau’uka na abinci. Ya ce:

ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣ ﭤ ﭥ ﭦ ﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭬﭭ ﭮ ﭯﭰ ﭼ المائدة: ٣



Ma’ana:

An haramta maku mushe da jini da naman alade da abin da aka ambaci sunan wanin Allah a gare shi (wurin yanka shi), da maqararriyar (dabba) da jefaffiya da wacce ta gangaro da sokakkiya da abin da masu dagi suka ci, - face abin da kuka yanka - da abin da aka yanka don gumaka (shi ma haramun ne). Kuma kada ku yi rabo da kibau na caca. Wancan fasiqanci ne.. (5:3).

Haka kuma a wata ayar, Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ambaci qungiyar wasu mata, da aka haramta wa musulmi aurensu. Inda Ya ce:

ﭽ ﮃ ﮄ ﮅ ﮆ ﮇ ﮈ ﮉ ﮊ ﮋ ﮌ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﮒ ﮓ ﮔ ﮕ ﮖ ﮗ ﮘ ﮙ ﮚ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮ ﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘﭙ ﭚ ﭛ ﭜﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣ ﭤ ﭥ ﭦ ﭧ ﭨﭩ ﭼ النساء: ٢٣ - ٢٤



Ma’ana:

An haramta maku (auren) uwayen ku (mata) da ‘ya’yanku, da ‘yan uwanku, da goggonninku, da innoninku, da ‘ya’yan xan uwa, da ‘ya’yan ‘yar uwa, da uwayenku waxanda suka shayar da ku mama, da ‘yan uwanku mata na shan mama, da uwayen matanku, da agololinku waxanda suke cikin xakunanku, daga matanku waxanda kuka yi baiko da su. Idan har baku riga kuka yi baiko da su ba to, ba laifi akan ku (ko auri ‘ya’yan nasu). Da matan ‘ya’yanku na tsatsonku (su ma basu halatta gare ku), da kuma ku haxa ‘yan uwa mata biyu (a lokaci xaya), sai dai abinda ya gabata (wannan Allah Ya yafe shi). Da matan da suke da igiyar aure (basu halatta ku aure su a wannan lokaci) sai fa in damanku ta mallake su (kuka kamo su a wurin jihadi da kafirai). Wannan hukuncin Allah ne gare ku. Kuma an halatta maku duk abinda ke bayan waxannan (da aka lisafta) ku neme (su) da dukiyoyinku kuna masu tsari da aure, ba masu zina ba. (4:23-24).

Haka nan kuma a wata ayar Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ambaci irin nau’in cinikin da yake haramta ga musulmi. Ya ce:

ﭽ ﭧ ﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭼ البقرة: ٢٧٥



Ma’ana:

Kuma Allah Ya halatta lafiyayyen ciniki. Ya kuma haramta Riba (2:275).

Wannan kenan. Amma kuma wani abin farin ciki, da ya kamata kowane musulmi ya yi godiya ga Allah Subhanahu Wa Ta’ala akai shi ne, kasancewar Buwayayyen Sarkin, Saboda tsananin rahamar da Yake da ita ga bayinsa, Ya halasta masu wasu abubuwa masu xinbin yawa, da yawun alqalami ba zasu iya qididigewa ba.

Saboda haka ne ma, maxaukakin Sarkin bai yi bayaninsu dalla- dalla ba. Amma Ya yi bayanin haramtattun abubuwa saboda zaman su ‘yan kaxan. Domin kuma su zama rubuce raxam a kan allon zukatanmu, har mu yi nesa- nesa da su koda yaushe. Ga abin da Yake cewa:

ﭽ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣ ﭼ الأنعام: ١١٩

Ma’ana:

Kuma haqiqa (Allah) Ya rarrabe maku daki-daki, abin da Ya haramta a kan ku, sai fa abin da aka buqatar da ku zuwa gare shi bisa lalura (6:119).

Amma a taqaice, duk abin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya halasta, to Ya yarda wa musulmi shi. Matuqar dai abu ne mai tsarki da nagarta a dai-dai lokacin. A kan sifofin waxannan abubuwa ne Yake cewa:

ﭽ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰ ﯱ ﯲﯳ ﯴ ﯵ ﯶ ﯷ ﯸ ﭼ البقرة: ١٦٨



Ma’ana:

Ya ku mutane! Ku ci daga abin da yake a cikin qasa, yana a matsayin halas, mai tsarki (2:168).

Kuma ko shakka babu, yanke hukuncin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi na kasancewar komai halas a taqaice, matuqar ba a sami wani dalili da ke haramta shi ba. Yin haka wata rahama ce da jinqayi Ya yi wa bayinsa. Kuma wajibi ne mu miqa wuya ga haka, mu kuma gode masa.

Haka kuma yin bayanin haramtattun abubuwa da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi dalla-dalla, shi ma wata rahama ce, da wani jinqayi. Don hakan na matuqar taimaka wa musulmi ga zama faxake, a kan dokokin shari’a. Musamman irin waxanda imaninsu da kaifin basirarsu ba su shige cikin cokali ba, a fagen addini musulunci.

Ba wannan kawai ba. Irin waxannan mutane, nada alamar buqatar a danqa masu jadawalin duk abubuwan da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya halasta dalla-dalla, kafin su gamsu da cewa addinin musulunci ba kurkuku ne ba.

Wato suna so ne aya ta sauka, tana cewa: Naman Raquma da na shanu da Tumaki da zomaye da Gada da Awaki da kaji da Xanragguwa da Agwagwar Ruwa da Zabbi, duk, halas ne, in an yanka su da sunan Allah. Haka kuma naman kaji da fari duk halas ne. Wata kuma ta ce: Ababen marmari da Furanni da Ganyaye, da duk wasu ire iren masu ciyawa halas ne. Kuma Ruwa da Madara da Zuma da Mayuka, duk halas ne. Wata kuma ta ce: “Gishiri da Yaji da Maggi da Kori” halas ne.

Sannan kuma a samu wani nassin na aya ko hadisi da zai ce: Amfani da katako da qarfe, ko Yashi da Duwatsu da Robobi da Gilasai da Qarau, su ma halas ne. Wani nassin kuma misali ya ce: Amfani da ababen hawa don yin tafiye tafiye cikin su har da Motoci da Jiragen qasa da na sama da jiragen Ruwa, su ma sun halasta.

Wannan na dasa aya kuma sai wani Nassin ya xauka: Amfani da Na’urorin sanyaya xaki da firijin, da Injinonin wanki da masu bushe kaya, da injinonin niqe Hatsi su koma Gari, da Na kwava fulawa, da Na niqe nama ko Ababen marmari, da Na’urorin binciken lafiyar mutum, da na qere qere, da Na Lissafi, da Na Hangen Nesa, da Na Tatso Ruwa da Mayuka da ma’adanai daga qasa da Na Tace Ruwa, da Na Xab’i da Masu qwaqwalwa, da Makamantansu. Duk amfani da waxannan abubuwa halas ne.

Wani Nassin kuma ya ce: Sanya Suturar da aka saqa da auduga ko ulu ko kittani ko roba ko gashin Raqumi ko fata, halas ne.

Haka kuma suna da buqatar wani Nassin ya gaya masu a fayyace, cewa Aure, Saye da Sayarwa, Xaukar Nauyin Wani, Yajejeniyar Cinikayya a Rubuce, rubuta Risit, Haya, Sana’oin Hannu kamar Saqa, qira, Jima, kanikanci da kiwo duk su ma halas ne,

Kai!!! Ko shakka babu idan aka ce haka za a bi duk abubuwan da ke halas tiryan- tiryan ana lissafi sai wani zamani ya qare ba a ci rabi ba.

ﭽ ﯽ ﯾ ﯿ ﰀ ﰁ ﰂ ﰃ ﰄ ﭼ النساء: ٧٨



Ma’ana:

Me ke faruwa ga waxannan mutane da ko kusa ga fahimtar magana ba su yi ba (sai in an yi ta dalla- dalla)? (4:78).

Wannan kenan. Mu koma ga cewar da suke ta yi, musulunci addini ne mai sauqi da rangwame. Wannan magana ko shakka babu gaskiya ce. Amma kuma a kaikaice mun fahimci suna son karkata akalar maganar ne a matsayinta na gaskiya, su xaure wa qarya gindi da ita.

Domin su, a tunaninsu musulunci ba zai karva sunan addini mai sauqi ba, sai ya tafi daidai da soye-soyen zukatansu. Alhali kuwa a haqiqa, sauqin da addini ke da shi na samuwa ne ga mutum a lokacin da ya bi abin duk da shari’a ta zo da shi sau da qafa. Akwai banbanci matuqa tsakanin sauqin da ke cikin addinin musulunci, da irin wanda waxannan mutane ke qoqarin tabbatarwa a cikinsa. Su a wurin su aikata miyagun xabi’u da halaye, a lave bayan wasu hujjoji na qarya shi ne sauqi. Ko alama. Ba haka abin yake ba. Sauqin da musulunci ya zo da shi, ya shafi xaga wa musulmi qafa ne a cikin waxansu abubuwa na halas don gudun su niqe shi. Kamar damar da aka ba shi ta haxa wata sallah da wata, ko taqaita wata, ko ajiye azumi a cikin halin tafiya, ko shafa a kan safa, na tsawon kwana xaya da yini ga mazaunin gida, da tsawon kwana uku da wuninsu ga matafiyi, ko wanda ke fargaban tava ruwa a kan wata lalura ya yi taimama, ko halatta kallon maccen da ba muharrama ba ga mai neman ta aure, ko zaven xaya daga cikin: ‘Yantar da Bawa ko Ciyar da Miskini ko Tufatar da shi ga wanda ya karya wani alwashi a matsayin kaffara, ko cin naman mushe idan wuri ya qure, da dai sauran rangwame- rangwamen da shari’a ta zo da su masu kama da waxannan.

Babban abin da ya kamata kowane musulmi, har da irin waxannan mutane, ya fahimta shi ne Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya shata wasu iyakoki da dokoki ne, ta hanyar haramta waxansu abubuwa a musulunci don Ya jaraba bayinsa. Kuma cin wannan jarrabawa ne, zai banbanta su da ‘yan wuta waxanda suka qare rayuwarsu cikin biyar qyaleqyalin duniya da son zuciya. Abubuwan da, da su ne Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi wa gidan wuta qawanya. Ya kuma yi wa gidan aljanna zoba da abubuwa masu nauyi da sosa zuciya waxanda haquri da su ke sa a samu isa tudun mun tsira. Ka ga kenan ta wannan hanya ce kawai Allah Subhanahu Wa Ta’ala zai ware bayinsa masu biyayya daga kangararru, ba don bai san su ba.

Sanin haka ne ya sa masu ingantaccen imani ke kallon irin waxannan jarabawoyi a matsayin wata hanya ta samun lada da yardar Allah. A haka sai ka taras saboda jin daxi, har tuman gada suke yi idan suna wata xa’a ga Allah, komai nauyinta. A yayin da su kuma munafukai ke kallon jarabawoyin a matsayin wata takurawa da musgunawa. A sakamakon haka sai al’amarin ya niqace su, su kasa cin jarrabawar bale su sami ladarta da yardar Allah.

Ka ga kenan, wannan bayani da ya gabata na tabbatar mana da cewa, duk wanda ya yi xa’a ga Allah Subhanahu Wa Ta’ala ta hanyar nisantar abubuwan da ya haramta, saboda shi kawai, to Allah zai maye masa gurbinsu da abin da ya fi wancan da ya nisanta zama Alheri. Bayan daular zaqin da zata cika zuciyarsa.

Don in faxakar da musulmi a kan wasu abubuwa da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta kuma Alqur’ani da Sunna suka tabbatar amma mutane suka yi biris da su, na rubuta wannan taqaitaccen littafi, ta hanyar fitowa da matsayin shari’a a kan abubuwan. Musamman saboda kasancewar ‘yan uwa musulmi na aikata da yawa daga cikin su.

A qarshe, ina roqon Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya yi mana jagora, mazanmu da mata. Ya kuma taimake mu a kan aikata abin da Ya umurce mu da aikatawa tare da nisantar abin da ya haramta. Ya kuma shiga tsakanin mu da miyagun ayyukanmu. Tabbas Allah shi ne mafi taimakon masu taimako ga shiriya. Shi ne kuma mafi jinqayin masu jinqayi.

BABI NA XAYA

SHIRKA


Shirka ita ce abu mafi girma daga cikin abubuwan da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta. Kuma haxarin da ke cikinta ya shafe na saura. Kamar yadda Abubakar Raliyallahu Anhu ya riwaito a wani hadisi cewa: “Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce wa Sahabbai wata rana: “kuna so in ba ku labarin zunubin da ba wanda da ya kai shi girma? Muka ce, qwarai muna so ya Manzon Allah! Sai ya ce, shi ne haxa Allah da wani abu a cikin bauta. (Bukhari: 2511).

Saboda girman wannan zunubi ne na Shirka, Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya sha alwashin ba ya gafarta wa duk wanda ya yi ta. Matuqar har ya mutu bai tuba ba. Savanin sauran zunubai da komai yawansu Yake shirye da ya gafarta wa wanda ya aikata su, qyaftawa da bisimillah.

Don tabbatar da wannan magana ne, Buwuyayyen Sarkin ke cewa:

ﭽ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﮭ ﮮﮯ ﮰ ﮱ ﯓ ﯔ ﯕ ﯖ ﯗ ﯘ ﭼ النساء: ٤٨



Ma’ana:

Haqiqa, Allah bai gafarta wa duk wanda ya haxa shi da wani a cikin bauta. Amma Yana gafarta abin da bai kai wannan ba, ga wanda Ya so (4:48).

Daga cikin nauo’an Shirka, da suka yawaita matuqa a qasashen musulunci a yau, akwai:

Bautar Qaburbura


Bautar qaburbura ita ce qudurce cewa, wani waliyyi daga cikin waliyyan da suka riga mu gidan gaskiya, na iya biyan wata buqatar mutum ko cetonsa daga wani haxari. Saboda haka sai a riqa kiran sunayensu don neman taimako ko agaji.

To, a idon shari’ah da aqidar musulunci ingantatta yin haka bauta wa irin waxannan bayin Allah ne. Alhali kuwa Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce:

ﭽ ﮍ ﮎ ﮏ ﮐ ﮑ ﭼ يوسف: ٤٠

Ma’ana:

Kuma Ubangijika Ya hukunta kada ku bauta wa kowa sai shi kaxai (17:23).

Irin wannan bauta ba ta tsaya ga waliyyai da qaburburansu ba. Har wasu Annabawa da Salihan mutane, da suka riga mu gidan gaskiya, wasu mutane kan nufa da wasu buqatu, da suka haxa da neman agaji, buqatar haifuwa, gyaran aure da makamantansu. Su ma sukan yi haka ne ta hanyar kiran sunayensu a irin waxannan lokuta. Alhali kuwa ba za su iya amfanin su da komai ba. Ga shi kuma Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce:

ﭽ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡﯢ ﯣ ﯤ ﯥﯦ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﭼ النمل: ٦٢



Ma’ana:

Ko wane ne yake karva wa mai buqata idan ya kira shi, kuma ya sanya ku mamayan qasa? Shin akwai wani abin bauta wa tare da Allah? Kaxan ne kuke faxaka (27:62).

Saboda tsananin kama jikin waxansu mutane da irin wannan Shirka ta yi, abin har ya fi qarfin qudurtawa a zuci. Wasu ma har ambaton sunayen wasu shehunai da waliyyai suke yi idan za su zauna ko za su tashi tsaye, ko idan suka yi tuntuve ko suka haxu da wata annoba. Sai ka ji suna cewa: “Ya Muhammadu” ko “Ya Aliyyu’’ ko “Ya Husaini”. A yayin da kuma wani zai ce: “Ya Badawi’’ ko “Ya jelani” ko “Ya shazali” ko “Ya Rufai”. Wasu ma har al-Aidarus ko Sayyidah Zainab suke kira. Alhali kuwa gaba xayansu su ma ta kansu suke yi, kuma bayin Allah ne kamar kowa. Kamar yadda Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya ce:

ﭽ ﯞ ﯟ ﯠ ﯡ ﯢ ﯣ ﯤ ﯥﯦ ﯧ ﯨ ﯩ ﯪ ﯫ ﯬ ﯭ ﭼ الأعراف: ١٩٤



Ma’ana:

Tabbas, waxanda ku ke kira ba Allah ba bayin Allah ne kamar ku. To, ku kira su su karva maku in gaskiya ne kuke yi (7:194).

Wasu ma har tattaki sukan yi zuwa wurin kusheyin waxannan bayi su dinga yin xawafi gare su kamar yadda ake yi ga xakin ka’abah, har ma su shafi kusurwoyinsu. Wasu kuma sukan har ma sunbanci kusheyin, su kuma kai hannayensu gare su, su shafi fuskokinsu da qurar kamar masu taimama. A yayin da wasu ko, da zarar sun tunkaro makwantan ba abin da za su yi sai ruku’i ko su yi tsaye qyam a gabansu suna masu tsananin ladabi da vari kamar su narke. A inda za su roqi buqatunsu kamar neman waraka daga wata rashin lafiya, ko albarka ga wani yaro, ko tsira daga wata matsala. A wasu lokutan ma zaka ji wasu daga cikinsu na magana da mamatan suna cewa: “Ya shugabana! ga ni na niqo gari daga uwa duniya ina fatar buqatuna sun gama biya. Alhali kuwa da za su share shekarun Abarshi suna kiran su ba za su karva masu ba. Allah Subhanahu Wa Ta’ala na cewa:

ﭽ ﯫ ﯬ ﯭ ﯮ ﯯ ﯰ ﯱ ﯲ ﯳ ﯴ ﯵ ﯶ ﯷ ﯸ ﯹ ﯺ ﯻ ﯼ ﯽﭼ الأحقاف: ٥



Ma’ana:

Kuma wane ne mafi vata daga wanda ke kiran wanin Allah wanda ba zai karva masa ba, har Ranar qiyama, alhali su (waxanda ake kiran) shagaltattu ne daga kiran su (46:5).

Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ke nufin wani da wata buqata banda Allah, makomarsa ita ce wuta (Buhari: 8/176).

Duk bayan waxannan kiraye-kiraye kuma, qarshe sai ka ga wasu daga cikin waxannan mutane sun karkata gefen kusheyin sun aske kansu. Wasu kuma sun shagala da karatun xan littafinsu mai suna: “al- Mashahid” wanda littafi ne da aka tsara yadda ziyarar qaburburran Waliyai da Annabawa zata kasance, da karance- karancen da wasu mutane suka ga ya dace ayi. Kamar dai Littafin “Manasik al- Hajji” wanda gamagarin Alhazzai ke amfani da shi. Qarewa da qarau ma, wasu daga cikin irin waxannan mutane sun yi imani da cewa a hannun waxannan matattu linzamen harkokin duniya suke. A sakamakon haka, suna iya amfanar da wanda suke so, su kuma cutar da wanda bai masu daidai ba. Tarqashi! Allah mai halitta!!.

Allah Subhanahu Wa Ta’ala dai cewa Ya yi

ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠﭡ ﭢ ﭣ ﭤ ﭥ ﭦ ﭧﭨ ﭩ ﭪ ﭫ ﭬ ﭼ يونس: ١٠٧



Ma’ana:

Kuma idan Allah Ya shafe ka da wata cuta, to babu mai yaye ta face shi, kuma idan Yana nufin ka da alheri, to babu mai iya hana falalarsa sauka. Yana bayar da alherinSa ga wanda Ya so, kuma Shi ne Mai yawan gafara, Mai Yawan jinqai (10:107).

Haka kuma duqa ma wani wanda ba Allah ba, Shirka ne. Kamar irin duqawar da irin waxannan mutane ke yi ko ajiye fitilu da kyandirora ga waxannan qaburbura. Bayan wannan nau’in Shirka sai kuma:

  1   2   3   4   5   6   7   8   9   ...   12


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət