Ana səhifə

Gyara kayanka yi hattara da


Yüklə 401 Kb.
səhifə9/12
tarix26.06.2016
ölçüsü401 Kb.
1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12

ALGUSSU


Algussu a cikin sha’anin saye da sayarwa na xaya daga cikin abubuwan da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta, kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya tabbatar, amma mutane da yawa a yau, sun yi biris da haramcin.

Wata rana Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi kicivis da wani xan sakai ya baje hajarsa, ta kayan abinci. Saboda tabbatar da nagarta da xauke haqqin shugabanci, sai ya cusa hannunsa cikin wani kwando, sai ya ji sanyin ruwa a qasa. Nan take, ya tambayi mai kayan: “Ya aka yi haka? Shi kuma ya karva masa da cewa: “Ruwan sama ne ya dake shi jiya Ya Manzon Allah”. Daga nan sai Manzon ya ce: “To me ya hana ka zuba mai sanyin a sama don mutane su zama ala basiratin game da shi? Ka sani duk wanda ke yaudarar jama’a ba ya tare da mu”(Muslim: 1/99)

Kinin irin wannan algussu na faruwa a wannan zamani namu. Wasu ‘yan kasuwa da tsoron Allah bai ishe su ba kan yi qaru- qaru su voye aibin da kayan sayarwarsu ke da shi, ta hanyar canza masa takarda ko su saka kayan da ba su da kyau qasan akwati su xora na gari a sama. Bayan sun yi wa na qasan asin-da-asin da kaloli da zanen da, da an kalle su sai a xauka na qwarai ne. Wasu kuma sukan shaqe kukan wasu injinoni, ta yadda aibinsu ba zai fito zahiri ga mai saye ba. Sai ya kinkimo ya kawo gida, sa’annan ya gane kurensa. A yayin da wasu ‘yan kasuwa kuma ke canza ajullan kayan sayarwarsu na haqiqa (Expiring date). Ko su ce wa mai saye su ba a jarraba kayansu kafin a saye. Kamar masu sayar da motoci da wasu na’urori, sai dai kawai a biya a xauka. Duk abin da mai saye ya taras na aibi a cikinsu daga baya, wai ruwansu

Irin waxannan halaye da xabi’u gaba xaya haramun ne. Domin kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Musulmi duk xan’uwan musulmi ne. Saboda haka ba ya halatta musulmi ya sayar wa xan’uwansa musulmi da wani abu mai aibi ba tare da ya gaya masa ba” (Ibnu Majah: 2/752)

Wasu ‘yan kasuwar kuma suna tunanin cewa idan suka siffanta wa mai saye kayan nasu, siffantawa ta zahiri kuma jumlace kamar wanin ya ce: Ina da dalar tama ta sayarwa, in kana saye”. Suna jin idan suka yi haka sun gama komai. Alhali kuma irin wannan siffantawa ba ta wadatarwa. Kuma duk cinikin da aka qulla a kan irin haka to xebabben albarkar ciniki ne. Kamar yadda Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Mutum biyu masu ciniki na da cikakkar damar yi ko fasawa matuqar ba su rabu ba. Idan gaba xayansu sun yi gaskiya cikin cinikin sun kuma bayyana duk abin da kayan ya qunsa (na aibi) to, Allah zai sa wa cinikin albarka. Idan kuwa suka yi qarya suka kuma yi algussu, Allah zai xebe masa albarka” (Bukhari: 4/328).

KERI


Wata mummunar xabi’a kuma da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta ita ce tayar da farashin kaya ba kuma da nufin saye ba, sai dai kawai don a yaudari wanda ya zo saye, ya saye da mugunyar tsada.

Yin haka haramun ne. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa: “kar ku tayar da farashi da gangan” (Bukhari: 10/484).

Qarawa ko tayar da farashi da gangan, wani nau’i ne na yaudara. Kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Qarshen yaudara da cuta shi ne shiga wuta” (Silsilah: 1057).

Dillalai a gidajen sayar da motoci kan sami kuxaxen haram masu yawa ta wannan hanya. Sukan haxa baki ne da su wasu su xora wa motocin toliya, farashinsu ya xaga sama daidai yadda nasu kaso zai fito. Shi kuwa mai saye, ko oho. Ko kuma su haxa baki su kayar da farashin kayan nan take, don su yaudari wanda ya kawo nasa don sayar wa. Wani lokacin ma har shigar burtu suke yi su taho da sigar masu saye, su yi barazana kamar zasu saye, alhalin baqon ne ake son cuta. Wannan haramun ne.


CINIKI BAYAN KIRAN SALLAR JUMA’A


Allah Subhanahu Wa Ta’ala na cewa:

ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟﭠ ﭡ ﭢ ﭣ ﭤ ﭥ ﭦ ﭧ ﭼ الجمعة: ٩



Ma’ana:

Ya ku waxanda suka kayi imani! Idan an yi kiran salla ranar Juma’a, sai ku tafi zuwa ga ambaton Allah, kuma ku bar ciniki. Wannan ne mafi alheri a gare ku, idan kun kasance kuna sani” (62:9)

Xabi’a ce da ta zama ruwan dare a yau ka ga mutane na ta harkokinsu na saye da sayarwa a cikin shaguna da kan tebura, alhali an yi kiran sallar Juma’a (Kira na biyu). Babban abin ban takaiki ma, wasu baki da hanci suke da masallatan. Duk wanda ke da hannu a cikin irin wannan ciniki, yana da nashi kamisho na zunubi, ko da kuwa asawaki ne ake saya a lokacin. Tabxijan! An ko shiga uku ke nan.

A fahimta mafi nagarta, a tsakanin malamai, duk cinikin da aka qulla a irin wannan lokaci vatacce ne. Abin da wasu masu gidajen sayar da abinci ke yi, da masu gidajen burodi da kanfunna, na tilasta ma ma’aikatansu aiki a daidai lokacin sallar Juma’a haramun ne. kuma kuxin da suke samo na aikin daidai wannan lokaci ba zai yi albarka ba; zai zame masu hasara.

Su kuma ma’aikatan nasu wajibi ne, su san cewa bin koyarwar Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama sau da qafa a cikin ko wane aiki shi ne wajibi. Kamar yadda ya ce Sallallahu Alaihi Wasallama “Babu xa’a ga wani abokin halitta a cikin sava wa Mahalicci” (Ahmad: 1/129).
CACA

Caca na xaya daga cikin manyan laifukan da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta, in da Ya ce:

ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭼ المائدة: ٩٠

Ma’ana:

Ya ku waxanda suka yi imani! Haqiqa giya da caca reful da kiban quri’a duk qazanta ne daga cikin aikin shaixan. Sai ku nisance su, don ku ci nasara (5:90).

Caca wata daxaxxar al’ada ce ta jahiliyya. Hanya mafi shahara ta gudanar da ita a wancan lokaci ita ce: Mutum goma za su haxa kuxi dai-dai wa dai-da su sayi raqumi. Qarshe kuma a saka shi caca tsakaninsu, ta hanyar zana wasu kibau. A inda mutane bakwai daga cikinsu ka iya tashi da raqumin. Ko su kuma da kaso daban-daban. Sauran ukun kuma su tashi tsula.

A zamanin nan namu na yau kuma caca na da salailai da dama. Kaxan daga cikinsu sun haxa da:



  1. Reful: Wani nau’i ne na caca da mutane ke zuba kuxi su sayi lambobi. Waxanda za a rubuta a can voye, cewa lamba kaza ita ce matsayin ta xaya, wata kuma ta biyu. Haka haka, har qarshe.

Irin wannan caca haramun ce, ko da kuwa za a yi sadaqa da kuxin da aka ciwo cacar ne.

  1. Sayen wani abu da ya qunshi abinda ba a sani ba. Ko sayen wata lamba don ta zo da cikin wani abu na amfani.

  2. Inshora: Wannan kuma wani nau’i ne na cacar zamani. Wato kauce wa qaddara. A kan kuma yi ta ne wa: Rayuwa ko abun hawa ko wasu kayayyaki. Ko kuma a yi ta don tsere wa hasarar gobara ko sata. Kuma akwai ta falan xaya, akwai kuma mai fal uku, da makamantansu.

Kai qarewa da qarau ma har muryar wasu mawaqa ake yi wa inshora a yanzu. Kowa ya daxe a duniya sai ya ga daxai!

A wannan zamani namu har qungiyoyi ke akwai waxanda ba su da aiki sai caca. A mazaunansu (Clubs) har tebura ke akwai na musamman waxanda ake wa laqabi da “Korayen Tebura” da babu mai zama kan su sai kartagai da ‘yan korensu. Wani nau’in kuma na cacar zamani shi ne wadda ake qullawa a kan dawakin sukuwa da wasu wasanni. Ko a kan injinun niqe ababan marmari a gidajen shaqatawa na yara. Haka kuma wasu malamai sun saka sauran gasanni na zamani a wannan layi.


1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət