Ana səhifə

Gyara kayanka yi hattara da


Yüklə 401 Kb.
səhifə10/12
tarix26.06.2016
ölçüsü401 Kb.
1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12

SATA


Sata haramun ce. Ga kuma hukuncin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya yanke wa duk wanda aka kama da laifin yin ta, namiji ne ko mace:

ﭽ ﭟ ﭠ ﭡ ﭢ ﭣ ﭤ ﭥ ﭦ ﭧ ﭨﭩ ﭪ ﭫ ﭬ ﭭ ﭼ المائدة: ٣٨



Ma’ana:

Kuma Varawo da Varauniya, sai ku yanke hannayensu, bisa sakamako ga abinda suka tsirfata, a matsayin azaba daga Allah. Kuma Allah Mabuwayi ne. Mai hikima (5:38).

Mafi munin sata a idon shari’a ita ce, satar kayan Mahajjata da masu aikin Umrah, a mafi tsarkin wuri a bayan qasa, kuma kusa ga Xakin Allah mai alfarma. Duk wanda zai yi sata a irin wannan wuri, to, ta babbata cewa bai san girman Allah da dokokinsa da birnin Makka ba.

A wani rahoto da aka bayar da wata sallah ta kisfewar wata da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya jagoranta, an ce an ga ya xan ja da baya. Ya kuma yi bayanin cewa: “Da kuka ga na xan ja da baya, wuta ce aka kusantto da ita. Don kada zafinta ya kai gare ni. Kuma a daidai wannan lokaci na hangi wani mutum da sanda mai gwafa, ana jan hanjin cikinsa qasa a cikin wutar. Laifinsa shi ne satar kayan Mahajjata da yakan yi da sandar tasa. Idan sun ganshi sai ya ce a’a gwafar ce ta sagale kayan shi bai sani ba. Idan kuma ba a faxaka da shi ba, satar ta tabbata kenan”.

Wata satar kuma mai muni a idon shari’a ita ce, satar kuxin Gwamnati. Wadda wasu masu yin ta kan kafa hujja da cewa “Ai ba gare mu farau ba”. Babban haxarin dake cikin irin wannan sata, wanda kuma masu yinta suka kasa ganowa shi ne, suna yi wa gaba xayan jama’a sata ne Domin dukiyar gwamnati ta kowa ce. Kuma ba wannan ba, ko dukiyar kafirai da waxansu musulmi ke sata wai don masu itan na kafirai, haramun ne, balle ta musulmi tsintsa. Kafiran kawai da aka halasta mana cin dukiyarsu ta ko wane hali su ne waxanda muke cikin yaqi da su; Ka ga waxanda ba haka ba, a matsayin xaixaiku ko cikin taron Jama’a sun tsira.

Wani nau’in satar kuma da shari’ah ta haramta shi ne “Tsame”. Wasu varayi kan shiga gidajen wasu mutane a matsayin masu ziyara. Amma a qarshe su tsame su. A yayin da wani lokacin ko, masu gidajen ne za su tsame baqin. Wasu kuma mata ne da kan shiga shagunan mutane su sace wasu abubuwa, su turo cikin aljihunsu ko wani cikin jikunna. Wasu mazan ma sukan yi haka. An ma samu wasu mutane a yau da ke jin irin waxannan ‘yan sace-sace qanana ba komai ba ne. Alhali kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Allah Ya la’anci Varawon da zai saci qwai ko igiya a yanke masa hannu” (Bukhari:12/81).

Wajibi ne ga duk wanda ya saci wani abu, farko ya tuba ga Allah. Sannan ya mayar wa mai abu da abunsa kai tsaye ko a kaikaice, ta hanyar wani. Koda ko a asirce. Idan kuwa har ya yi iyakar qoqarinsa ya ka sa gane mai shi, ko magadansa, to sai ya yi sadaqa da shi, da niyyar ladar ta je ga mai shi.

CIN HANCI


Bayarwa da Karvar Cin Hanci haramun ne a shari’ar musulunci. Kamar mutum ya ba alqali wani abu ko da na magana mai daxi ne, don ya kawar da kansa daga wata tabbatattar gaskiya ko ya xaure wa wata qarya gindi, Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya haramta irin haka don tana qarewa ne ga zaluntar mai gaskiya. Tana kuma watsa varna a cikin al’umma. Allah Subhanahu Wa Ta’ala na cewa:

ﭽ ﮛ ﮜ ﮝ ﮞ ﮟ ﮠ ﮡ ﮢ ﮣ ﮤ ﮥ ﮦ ﮧ ﮨ ﮩ ﮪ ﮫ ﮬ ﭼ البقرة: ١٨٨



Ma’ana:

Kuma kada ku ci dukiyoyinku a tsakanin ku ba da gaskiya ba, kuma don ku bayar da cin hanci ga mahukunta sai ku ci wani yanki na dukiyoyin mutane da zunubi alhali kuna sane” (2:188).

Haka kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce a wani hadisi da Abu Hurairata Raliyallahu Anhu ya riwaito: “Allah Ya la’anci duk wanda ya bayar da hanci da wanda ya karve shi a kan wata shari’ah” (Ahmad: /307).

Amma kuma yana da matuqar muhimmanci a nan, a lura cewa, abin duk da mutum zai bayar don qwato wani haqqi nasa da ke son salwanta, ko ya tunkuxe wani zalunci da ake son yi masa qahran, ba hanci ba ne, matuqar dai babu wata hanya da zai iya tabbatar da haqqinsa sai ta haka.

Wani abin ban takaici ma duk, bai fi irin yadda mutane a yau suka yi biris da wannan haramci ba. Har aka wayi gari hanci ya zama wata babbar hanya ga waxansu mutane, ta samun kuxin shiga fiye da albashinsu na yau da kullun. Kai! Ta kai ma wasu kanfunna, kasafinsu na shekara- shekara ba zai kammala ba sai sun ware na hanci. Don waxansu hulxoxin ko xanbansu ba za a xiga ba sai an lanqwashe hancin aljihu. Wasu kuwa ko an fara qarewar ba zata yiwu ba da hanci ba a hannu.

Yawaitar sabgar bayar da hanci da karvarsa na haifar da matsaloli da dama, musamman ga masu xan qarfi. A yayin da dokoki da dama ba sa kai labari saboda shi. Lalacewar tarbiyya da rashin ta, duk kan haifu ne sanadiyyar cin hanci. Sai ka ga tsakanin maigida da ma’aikatansa babu girma babu girmamawa. Saboda ba za a tsaya a yi wa duk wanda yaqi bayar da hanci aiki na gari ba. Qarshe sai an vata masa lokaci, kuma aikin da zai samu ya zamo rubabe- rubabe.

Yau da zaka zo a wata ma’aikata makare, zaka iya rigan wanda ya yo sammako samun biyan buqata, matuqar zaka bayar da na goro (hanci). Da yawa zaka taras a kamfani, kuxaxen da ya kamata su tafi aljihun mai shi, sun qare a hannun dillalansa na ciki da na waje. Ko shakka babu la’akari da waxannan matsaloli da musibu da cin hanci ke haifarwa, na hana mutum mamakin abin da ya sa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya roqi Allah Subhanahu Wa Ta’ala Ya nisanta duk wanda ke da hannu a cikin wata ma’amala ta cin hanci daga rahamarsa. Abudullahi xan Umar Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “La’anar Allah ta tabbata a kan duk wanda ya bayar da hanci ko ya karve shi” (Ibnu Majah: 2313).

QWACEN FILI

Idan ba sa’a aka yi tsoron Allah ya cika zukatan masu iko da qarfi da basira ba, sai hakan ta zama wata masifa gare su. Domin kuwa za su qarasa ne ga zaluntar wasu mutane, ta hanyar qwace masu ababen mallakarsu kamar Fili.

Hukuncin da shari’ar musulunci kuwa ta tanadar wa mai irin wannan xabi’a mai tsanani ne. Domin Abdullahi xan Umar ya riwaito cewa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama yace: “Duk wanda ya qwaci filin da ba halaliyarsa ba Allah zai sa qasa ta rusga da shi har qasa ta bakwai a ranar alqiyama” (Bukhari: 5/103).

Haka kuma Ya’ala xan Murrata Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya qwaci filin wata qasa, koda kamu xaya ne zulman. To, Allah zai tilasta masa gino faxinta har qasa ta bakwai, ya kuma xauke ta a kai har a qare hisabi ranar qiyama. (Amma a cikin Xabari cewa aka yi, za a tilasta masa dawowa da ita)” (Xabarani: 22/270).

Haka kuma wannan haramci ya haxa har da baje iyakar gonaki ko filaye, tare da canza masu bigire, don handama da babakere da nakkasa haqqin makwabci. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama na cewa: “La’anar Allah ta tabbata kan duk wanda ya canza iyakar fili” (Muslimu: 13/141).

CI DA CETO

Ko Shakka babu samun wani muqami a cikin mutane wata baiwa ce ta Allah Subhanahu Wa Ta’ala da yake yi wa wanda ya so daga cikin bayinsa. Musamman idan wanda aka yi wa xin ya gode.

Babbar hanyar da irin wannan bawa ke iya bi don tabbatar da godiyarsa ga Allah a irin wannan hauji, shi ne hanyar amfanar da sauran musulmi. Wannan shi ne wani abu na ma’anar hadisin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke cewa a cikinsa: “Duk wanda Allah Ya ba ikon amfanar da xan’uwansa daga cikinku, to ya hanzarta” (4:1726).

Duk mutumin da ya amfanar da wasu mutane, ta hanyar matsayinsa; ya tunkuxe masu wani zalunci, ko ya jawo masu wani alheri, ba kuma tare da ya aikata wata haramiya ba, ta hanyar taushe haqqin wasu, Allah Subhanahu Wa Ta’ala zai saka masa da alheri. Matuqar niyyarsa kyakkyawa ce. Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gaya mana cewa; Ku ceci mai xan qarfi sai ku sami lada” (Abu Dawuda; (5132).

Karvar wani abu a irin wannan matsayi na ceto, a matsayin goro haramun ne a shari’ah. Hadisin da Abu Umamata ya riwaito na tabbatar da wannan magana, cewa; Duk wanda ya ceci wani, ya kuma karvi na goro to, ya aikata babbar Riba (Ahmad: 5/261).

A ra’ayin wasu nagartattun malamai, wannan hadisi na Abu Umamata na tabbatar da cewa, xabi’ar da wasu masu maqamai ke yi ta taimakon wasu mutane, ta hanyar samar masu aiki, ko yi masu canji daga wani ofis zuwa wani, ko wata nahiya zuwa wata, ko shayar da su magani da sauransu, duk haramun ne matuqar dai sun yi haka ne da manufar karvar na goro daga baya. Koda kuwa ba a qulla wata yarjejeniya a kan haka ba. Ladar da Allah Subhanahu Wa Ta’ala zai saka wa wanda ya yi xaya daga cikin irin waxannan ayyuka don Shi, ta fi duk wani abu da zai karva nan duniya yawa da albarka.

An riwaito cewa wani mutum ya zo wurin Hassan xan Sahalu, ya roqe shi da ya kama masa wata harka, ya kuwa kama masa, aka yi nasara. Daga baya sai mutumin ya zo godiya gare shi sai ya ce masa; “Godiya ta me? Mun yi imani da cewa zakka na wajaba daga rigar arziki da sutura, kamar yadda take wajaba daga tarin dukiya” (Ibnu Muflih: 2/176).

Amma yana da matuqar kyau a lura, kuxin da mutum zai biya wani lauya, don ya yi masa wani aiki na shari’ah, ba ya cikin wannan mas’ala. Wannan ba haramun ba ne. Ya sava wa irin wancan da ake amfani da matsayi kawai a shiga tsakani, qarshe kuma a karvi wani kuxi a matsayin garo.


JINKIRIN BIYAN MA’AIKATA

Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya kwaxaitar da musulmi akan gaggauta biyan duk wanda aka yi wata jinga da shi a kan wani aiki, ladarsa nan take. Ga abin da yake cewa: “Ku biya xan qwadago ladarsa tun kafin zufan goshinsa ya bushe” (Ibnu Majah: 2/817).

Wannan matsala ta jinkirin biyan ma’aikaci albashinsa, ko xan qwadago jingarsa, ko ma hana masu kwata- kwata na xaya daga cikin zalunce-zaluncen da ake fama da su a kwanukan nan namu na yau. Akwai hanyoyi daban- daban da irin wannan zalunci ke faruwa, da suka haxa da kamar:


  1. Cin Haqqin Ma’aikata: Da yawa wasu mutane, saboda wani matsayi da suke da shi a ma’aikata, sukan canye haqqin wani ma’aikaci kwata- kwata. Musamman idan ba ya da wata hujja a hannu da zai tabbatar da haqqin nasa. Ma’aikatan da irin wannan zalunci ke faxa wa, na da cikkakken alqawari a wurin Allah cewa, koda waxannan haqqoqa nasu sun salwanta nan duniya, to zai qwatar masu su gobe qiyama. Ta hanyar xibar wani abu daga cikin kyawawan ayyukan azzaluman a basu. Idan kuma ayyukan nasu na gari suka kasa biyan bashin, sai a xebo wani abu daga cikin zunuban wanda aka zaluntar a jibga wa azzalumin. Qarshe kuma a iza qeyyarsa zuwa wuta.

  2. Tauye Haqqin Ma’aikaci: Wasu uwayen gida kuma, xabi’arsu ita ce, tauye haqqin ma’aikaci daga haqiqanin abin da aka yi yarjejeniya da shi tun asali. Irin waxannan mutane na da mummunan tanadi a wurin Allah Subhanahu Wa Ta’ala don Ya ce:

ﭽ ﯖ ﯗ ﯘ ﭼ المطففين: ١

Ma’ana:

“Bone ya tabbata ga masu tauye haqqi” (33:1).

Misalin wannan baqar xabi’a, shi ne abin da wasu masu hannu da shuni kan yi na xauko ma’aikata daga garuruwansu na asali, su kawo su birni da yarjejeniyar biyansu wani adadi na kuxi duk bayan wani qayyadajjen Lokaci. Amma kuma da an fara tafiya, aiki ya fara nisa, ya riga ya zarge wuyansu, sai ya lallava ya canza waccan yarjejeniya, ya tauye haqqin nasu na asali. Su kuma saboda rashin makarkata ko wata takamammar hujja a hannunsu, dole sai su haqura, a yi ta sha’ani wai an cuci baqauye, in ji xan birni!. Iyakar abin da irin waxannan ma’aikata ke iya yi shi ne; Allah Ya isa.

Babbar illar da ke cikin irin wannan nau’i na zalunci ita ce, idan mai irin wannan xabi’a musulmi ne, to zai tozarta musulunci a idon irin waxannan ma’aikata har ya cire masu sha’awar addini idan su ba musulmi ba ne. Duk mai irin wannan xabi’a ya sani yana da zunubi a wurin Allah.



  1. Niqe ma’aikaci: Wasu uwayen gidan kuma, xabi’arsu ita ce niqe ma’aikaci. Ta hanyar tsawaita lokacin aikin nasa, ko qara masa wani aikin ba kuma tare da yayi masa wata ‘yar toliya ba a kan jingayarsa ta asali (Over time).

  2. Jinkirta Haqqin Ma’aikaci: Wasu uwayen gidan kuma, tasu xabi’ar ita ce, jinkirta biyan haqqin ma’aikaci. Wani Lokacin ma sai ma’aikacin ya yi kamar yana yi, ta hanyar faxi tashi, hargowa da qorafi. Wani lokacin ma sai ya nemi ceton alqali. Manufar irin waxannan mutane ita ce su gajiyar da ma’aikacin ya fita batun haqqin nasa dole, su canye ko su juya shi ta hanyar Riba zuwa wani lokaci, kafin su ba shi. Alhali kuwa irin waxannan ma’aikata ba su da abin da za su aika wa iyalinsu da suka baro gida, suka taho birni don nema masu abinci. Ba ma wannan ba, ko abin da za su sayi abin karin kumallo kullum ba su da. Bone ya tabbata kan irin waxannan azzalumai a shu’umar ranar nan mai zuwa!

Abu Hurairata ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Allah Ya ce: zan yi fito na fito da wasu mutane uku a ranar qiyama: 1) Mutumin da ya rantse da sunana kuma ya sava, 2) Mutumin da ya sayar da xa a matsayin bawa, ya kuma sa kuxin aljihu da, 3) Mutumin da ya sa wani aiki ya kuma qi biyansa jingarsa” (Bukhari).
RASHIN ADALCI TSAKANIN ‘YA’YA

Wani abu kuma da shari’ar musulumci ta haramta, kuma wasu mutane suka yi biris da shi, shi ne Rashin Adalci tsakanin ‘ya’ya. Ta hanyar ba wa wani daga cikinsu abin da basu ba wani ko saura ba. Wanda hakan ke tabbatar da sun fifita shi a kan saura.

Wasu malamai nagartattu, na ganin cewa, idan mahaifi na da wani qwaqqwaran dalili na yin haka, to babu haramci. Kamar xan da ya fifita xin ya kasance ya kevantu da buqatar abin, saboda rashin lafiyar da yake fama da ita, ko wani bashi da ake bin sa, ko ya yi masa kyautar ne a matsayin goron qwazon hardace alqur’ani da ya yi, ko wani aiki da ya yi qoqarin samar wa kansa. Ko saboda yawan iyalinsa, ko shagala da neman karatu da ya yi. Ko dai wani dalili mai kama da waxannan.

Amma kuma duk da haka sun ce, ana so mahaifin ya qulla niyya a ransa, ta ba wa wani daga cikin sauran ‘ya’yan irin wancan abu, a duk lokacin da xaya daga cikin irin waxancan buqatoci suka kama shi. Domin kuwa qa’idar ta asali ita ce abin da Allah Subhanahu Wa Ta’ala ke cewa;

ﭽ ﯚ ﯛ ﯜ ﯝ ﭼ المائدة: ٨

Ma’ana:

Ku yi adalci, shi ne mafi kusa ga taqawa (5:8)

Babban abin da ke tabbatar da rashin halaccin irin wannan xabi’a shi ne, abin da Nu’umanu xan Bashiru Raliyallahu Anhu ya Riwaito daga Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama bayan mahaifinsa ya taho da shi wurin Manzon, inda shi mahaifin na Nu’umanu ya ce wa Manzon; “Na ba wa xan nan nawa wani bawa da nake da shi”. Sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Ina fatar ka ba wa gaba xayan ‘ya’yanka irinsa”. Ya karva masa da cewa: “A’a”. Daga nan sai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce masa:” To, ka fasa wannan kyauta (Bukhari: 5/211).

A wata riwaya kuma ce masa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya yi; “Ka ji tsoron Allah ka kuma yi adalci tsakanin ‘ya’yanka”. Daga nan shi kuma sai ya je ya tayar da waccan kyauta. (Fathul Bari 5/211). A wata riwaya ta uku kuma, cewa aka yi Manzon Allah ya ce masa: “Kar ka nemi in zama shedunka a kan wannan kyauta. Don ba zan zama sheda a kan zalunci ba” (Muslim: 3/1243).

Babu laifi a shari’a a ba wa xa namiji ninkin abin da aka ba wa xiya mace, kamar yadda hukuncin gado yake, inji Imamu Ahmad Rahimahullahu. (Abu Dawuda: 204).

Wannan ita ce qai’da ta shari’a. Amma sai ga shi a zamaninmu na yau a wasu gidaje, saboda rashin tsoron Allah, uwaye maza na fifita wasu ‘ya’ya nasu a kan wasu a cikin kyauta. Sun kuma kasa gane cewa, irin wannan banbanci da suke nunawa tsakanin ‘ya’yan na iya haifar da hassada da qiyayya da gaba a tsakaninsu.

Wasu uwayen kan nuna irin wannan banbanci ne ta hanyar yi wa wani daga cikin ‘ya’yan nasu wata kyauta, wai don kawai ya yi kama da danginsa na wajen uba a halitta. Ya kuma ba wa wanda ya ya yi kama da dangin uwarsa qasa ga abin da ya ba na farko. Ko kuma ya ba wa ‘ya’yan wata mata fiye da abin da ya ba na wata. Ko ya xauki ‘ya’yan wata ya saka makarantar kuxi, ya bar na saura a makarantun gwamnati. Wannan a qarshe ko shakka babu qaiqayi zai koma wa masheqiya. Don za a wayi gari a mafi yawan lokuta ‘ya’yan da ya tozarta su xauke shi ba bakin komai ba, ko har ma can gaba idan Allah Ya xaukaka su, su ma su walaqanta shi. Tabbas haka na iya faruwa, don Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Hala ba ku son su ma ‘ya’yan naku su girmama ku?” (Ahmad; 4/269).
ROQO BA BUKATA

Sahlu xan Hanzalata Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya roqi mutane kuxi alhali yana da abin da ke isar sa buqata, to yana roqar ma kansa garwashin wuta ne kawai”. Sai sahabbai suka tambayi Manzon; “Mene ne miqidarin abin da za a ce ya ishi mutum buqata har ya hana shi roqon qari? Sai ya karva masu da cewa: “Idan ya mallaki abin da zai ci abincin rana da na dare” (Abu dawuda: 2/281).

Haka kuma xan mas’udu Raliyallahu Anhu ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ke roqon mutane kuxi alhali yana da abinda ke isar sa biyan buqata, zai tashi Ranar qiyama fuskarsa da farxe- farxe” (Ahmad; 1/388).

Duk da irin wannan tanadi da shari’ah ta yi wa mai roqo ba da wata buqata ba. Wasu mutane a yau, sun sami sandar roqe-roqe har ma a masallaci. Inda zasu je su dami mutanen da ke sallah da salati babu li babu la. Su kan yi haka ne kuma ta hanyar shimfixa koke- koke na qarya. Wasu daga cikin su ma har takardun qarya suke yawo da su a masallatan sana damun mutane da dogon turanci. Wasu kuma iyalansu suke rarrabawa a masallatan don gudanar da wannan mugunyar sana’a. Ba su wannan masallaci ba su wancan. Alhali kuwa wasu daga cikinsu Allah ne kawai ya san iyakar abin da suka mallaka. Sai kuwa idan sun mutu, a yi ta jin sun bar kaza sun bar kaza. Alhali a lokacin da suke waxancan roqe- roqe suna rufe damar wasu mutane ne, da ba su mallaki komai ba, amma tsoron Allah da tsaron mutunci sun hana su fitowa su roqa. Mutane kuma zaton suke yi sun wadata. Qarshe sai a xauki abin da ya kamata a ba su a ba waxannan jeqaqqin.


TURUN BASHI

Haqqin wani a hannun wani nada matuqar girma a wurin Allah. Ta yadda har ta kai da mutum zai tava wani haqqi na Allah, ya kuma tuba, Allah na iya yafe masa. Amma da zai tava haqqin wani mutum xan’uwansa dole ne ya mayar masa da shi kafin ranar da Naira da Kobo ba su da wani tasiri face kyakkawan aikin mutum.

Allah Ta’ala ba ya yafe wa wani haqqin wani. Saboda haka Yace:

ﭽ ﯘ ﯙ ﯚ ﯛ ﯜ ﯝ ﯞ ﯟ ﯠ ﭼ النساء: ٥٨



Ma’ana:

Haqiqa Allah Yana umurnin ku ku bayar da amanoni zuwa ga masu su (4:58).

Yawan cin bashi ba da niyyar biya ba, na xaya daga cikin matsalolin da suka zama ruwan dare a cikin al’ummarmu a yau. Irin wannan bashi ma wasu kan karve shi ba don suna da wata buqata ta gari ba. Sai don kawai su faxaxa sana’o’insu, ko don su yi takarar sayen motocin shiga ko kayan alatu ko wasu qyale-qyalin rayuwa da wasu takwarorinsu. Wasu sukan mallaki irin waxannan kayayaki ne, ta hanyar qulla yarjejeniyar biyansu kaxan – kaxan. A qarshe kuma sai su qare cikin haramiya dumu- dumu.

Irin wannan xabi’a ta cin bashi a kai- akai ba kuma da niyyar biya ba, na sa wasu mutane zama turayen bashi, wanda kuma qarshe yakan haifar da talauci da kariyar arziqi. Don kauce wa faxawa cikin irin wannan matsala ne, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gargaxi Al’umarsa da cewa: “Duk wanda ya karvi kuxin mutane a matsayin bashi, da niyyar biya Allah zai ba shi ikon biya, amma wanda ya karva ba da niyyar biya ba sai don ya kaxas, Allah zai kaxas da shi’ (Bukhari: 5/54).

Da yawan mutane a yau sun xauki wannan matsala ba bakin komai ba. Alhali kuwa babbar matsala ce a wurin Allah. Wadda har ta kai ko shahidi, tattare da irin ladar da yake da ita, ba za a yafe masa bashin mutane da ke kansa ba. Tabbacin wannan magana shi ne hadisin da ke cewa: “Tsarki ya tabbata ga Allah. Don bai sanya wani tsanani a cikin addini ba, sai a cikin sha’anin bashi. Ina rantsuwa da wanda raina yake hannunsa, da za a kashe mutum a wurin yaqi, a raya shi a kuma sake kashe shi, a kuma sake raya shi a kuma sake kashe shi, to ba zai shiga aljanna ba matuqar ana bin sa bashi, sai an biya shi. (Nasa’i: 7/314).

Ya kamata duk wanda ke irin wannan xabi’a ya tuba, kafin wuri ya qure masa.


CIN DUKIYAR HARAM

Da yawa mutanen da tsoron Allah ya yi wa kaxan a zukata, ba su damu da ta ko wace hanya za su sami kuxi ba, balle wadda za su kasha su a cikin ta. Abin da kawai ya dame su, shi ne yadda ajiyarsu ta banki za ta qara kauri, koda ta hanyar haramiya ce.

Saboda cika wannan guri, sai su shiga wawure kuxaxen bayin Allah da suke amana a hannun su. Wasu kuma su kama ‘yan sace-sace ko fashi da makami ko damfara ko haramtattar sana’a kamar Riba, ko cin kuxin marayu, ko bokanci. Waxansu kuma sukan kama ‘yan tabanjamanci ko waqa, ko tatsar taskar musulmi, ko tava kayan mutane, ko yaudararsu ta hanyar karvar kayan da qarfi, ko tsawwala wa kayan da suke sayarwa farashi. A yayin da wasu kuma ke tsira sana’ar barace- barace ba da wani dalili ba. Ga su nan dai.

Da kuxin da waxannan mutane suka samu ta waxannan hanyoyi za su sayi abinci ko tufafi da ababen hawa, ko su gina gidaje, ko su kama haya, wasu ma har su sayi kayan alatu su zuba a gidajen. Alhali kuwa Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: Duk tsokar jikin da ta ginu da haramun wuta ce mafi cancanta da ita” (Xabarani: 19/136).

Kafin haka kuma a Ranar qiyama, Allah zai tambayi ko wane mutum a kan yadda ya sami dukiyarsa da yadda ya kashe ta. Ta haka sai kowa ya haxu da sakamakonsa daidai da aikinsa.

Da wannan muke kiran duk wanda ya san cewa akwai wata dukiya hannunsa ta haram ya yi gaggawar rabuwa da ita, ya mayar wa mai ita idan ya san shi, ya kuma nemi gafarar Allah. Kafin Ranar da kuxi ba su da wani amfani sai dai aikin qwarai.


SHAN BARASA

Allah Maxaukakin Sarki na cewa a cikin Littafinsa mai tsaki:

ﭽ ﭑ ﭒ ﭓ ﭔ ﭕ ﭖ ﭗ ﭘ ﭙ ﭚ ﭛ ﭜ ﭝ ﭞ ﭟ ﭠ ﭼ المائدة: ٩٠

Ma’ana:

Ya ku waxanda suka yi Imani! Haqiqa giya da caca da reful da kiban quri’a, duk qazanta ce kawai daga cikin aikin shaixan, sai ku nisance ta wa la’alla ku ce nasara” (5:90).

Wannan umurni da Buwayayyen Sarki Ya bayar na nisantar waxannan abubuwa, da suka haxa da shan Giya, Babban dalili ne da ke tabbatar da kasancewar gaba xayan haram. Kuma kawo giya da Sarkin ya yi tare da gumaka, kafaxa- da kafaxa ya tabbatar cewa, ita ma haramun ce.

Haka kuma Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya qara tabbatar da haramcin shan giya, a wani hadisi da Jabir ya riwaito, inda ya ce: “Allah Ya yi alkawalin shayar da duk wanda ya sha giya dagwalon khibal. Sahabbai suka ce, “Ya Manzon Allah mene ne dagwalon khibal? Sai ya ce: zufan ‘yan wuta ko rowan qurajensu! (Muslim: 3/1587). Haka kuma xan Abbas ya riwaito cewa, Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Duk wanda ya mutu yana mashayi, zai haxu da Allah a matsayin mai bautar gumaka” (Xabarani 12/45).

Yawan sunayen giya da banbancin kamfunan da suka sana’anta ta ba zai tada ita daga haramci ba. Daman dai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya ce: “Wasu mutane daga cikin al’ummata zasu sha giya suna kiran ta da wani suna” (Ahmad: 5/352). Kiranta da sunan “Tsime” da “Burkutu” da makamanta su idan ya zama da nufin yaudara to, mashayan ne ke yaudarar kansu. Kamar yadda Allah ya ce:

ﭽ ﭸ ﭹ ﭺ ﭻ ﭼ ﭽ ﭾ ﭿ ﮀ ﮁ ﮂ ﭼ البقرة: ٩



Ma’ana:

Suna (tunanin sun) yaudari Allah da waxanda suka yi imani, alhali ba su yaudarar kowa sai kan su, kuma ba su sakankancewa!” (2:9)

Shari’ar musulunci ta yi matuqar xaukar mataki a kan wannan matsala ta giya da shan ta. Ta kuma warware zare da abawarta don kada wani kokwanto ko tantama su shiga ga mutum a kai. Dubi abin da Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ke cewa: “Duk abin da ke sa maye giya ne, kuma ko wace irin giya haramun ce” (muslim: 3/1587).

Ka ga kenan wannan magana ta ma’aiki ta gama tabbatar mana da cewa, duk abin da ke dagula hankali da tunani idan an sha shi to giya ne, komai qanqantarsa. Kuma ko da an bashi sunaye daban daban, komai yawansu dai, giya ce. Hukuncinta ko sananne ne.

A qarshe ma dai Manzon Allah Sallallahu Alaihi Wasallama ya gaya wa mashaya giya farar gaskiya mai xaci, inda ya ce: “Duk wanda ya sha giya har ta bugar da shi, ba za a karvi sallarsa ba har kwana arba’in. Idan kuma ya mutu a cikin wannan hali makomarsa ita ce wuta. Idan kuma ya tuba Allah zai gafarta masa. In ya koma sha har ya yi maye, kuma za a sake qin karvar sallarsa ta kwana arba’in. Idan kuma ya mutu a wannan hali, wannan karon ma wuta ya yi. Amma idan aka yi sa’a ya tuba to, Allah zai yafe masa. Haka kuma da zai sake sha ya kuma sake buguwa, karo na uku, nan ma za a ba sallarsa baya har tsawon kwana arba’in. Da kuma zai kwanta dama a wannan hali, ba abin da zai hana shi shiga wuta. Da kuma zai tuba Allah zai karvi tubansa.

Amma da zai sake sha karo na huxu to, Allah Ya yi alkawalin shayar da shi dagwalon khibal a Ranar qiyama. Sahabbai suka ce: Ya Manzon Allah, mene ne dagwalon khibal? Ya ce: “Shi ne surkamin ‘yan wuta” (Ibn majah: 3377).

1   ...   4   5   6   7   8   9   10   11   12


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət