Ana səhifə

Karban shawara daga wurin allah "Masu-albarka ne masu-tsabtan zuciya gama su za su ga Allah." Daga


Yüklə 361.5 Kb.
səhifə4/11
tarix25.06.2016
ölçüsü361.5 Kb.
1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11

Sunaye da Hali na Ruhu Mai Tsarki


Yadda shatan yana matso kusa da kai domin ya hallaka da yaki, haka nan ne kuma Ruhu mai Tsarki yana zama kusa da kai domin ya kara maka karfi. Kuma yadda shaitan na harba maka tunani ta hallaka a sa’a zuwa zuciyarka haka nan ne kuma Ruhu Mai Tsarki yana harba maka tunani ta sa’a sa’a na rai zuwa zuaiyarka. Bari yanzu mu dubi irin hali da aiki na Ruhu Mai Tsarki.

Mai- Taimako da Lassa


Tushed halin shaitan shi ne ya yi sara. Tushen halin Ruhu Mai Tsarki kuma shi ne ya taimaka mana da lallasa da kalmoni na gaskiya. “……shi kuma za ya ba ku wani Mai-taimako, domin shi zamma tare da ku har abada; shi Ruhu na gaskiya… (Yohanna 14:16,17a).” Kalmonin da Ruhun zai fada mana suna kwantar mana da hankali, da kuma hura mana iska na warkasuwa da kuma shane mana hawaye. Ko ma da ace akwai tsantawa da kuma gyara daga wurinisa, za ta zo ne tare da kwanaiyar rai da kuma bege a cikinta. Suna sike da alheri, da tausayi da kuma bege. Suna kuma daga karfin zukatanmu su kuma kawo khekawa ta rai ga marayin ruhohinmu.

A lokacin da na fara gane halin irin tunanin da ke abko nani a zuciyata, ko daga shaitan ko kuma daga Ruhu Mai Tsarki, sai na soma lissaffa in gani lo wane irin kalmoni ne na fi kasa kunnuwa ga a kullum. Ko kalmar wa na fi bada hankalinwa? Kalmonin wane ne ne na fi bari a zuciyata domin ta yi tsewa har ta zuba ‘ya’ya?

Abinda da na iske ta ba ni mamaki’ kwarai da gaskiya. A wannan lokaci a rayuwata na iske ina ba shaitan 80 bisa dari na lokacina domin jin sora da karya da kuma dharantawa ta iblis. Ina kuma ba shi Ruhu Mai Tsarki da kalmomin sa ta bege da kwanajar rai 20 bisa dari ne kurum. Ba mamaki mana ina rayuwata cikin tunani hukunci, da sara da kuma bakin ciki a kullum.

Dole ne mu mika kanmu domin mu binciki zukatanmu domin mu kori duk tunai na jan baya, da sara, mu kuma rungumi dukan tutani na Lallasa da kuma ta kwaraijar rai. Dole mu tashi tsaye domin me kama kowane irin tunani wadda ba na rai ba kwarto domin mu sa shi ya yi imani da banta ga Kristi. Ka da dai mu ba wa shaitan file a wannan yaki ta zuciyarmu, domin kowane nasara a wannan fage tana mulki bisa kowane nasara a wannan fage tana mulki bisa kowane irin kalmar da muke fada da kuma irin abin da muke aikatawa.

Ta yaya ne za mu uja hambare wannan mai sara daga zukatanmu mu ku sa shi bauta ga iko ta yesu? Ba abu mai wuya ba ee. Ba sai an yi wani yawan addu’a ko aikata wata babban bangaskiya ba. Abin da irin wannan take bukata ita ne tsaro mai niya. Idan mun ji motsin wani tunani ta jan baya, da hallaka a zucijarmu, nan da nan sai mu yaki wannan mu kuma canza ta da wata kalma ta cirigaba daga wurin kalmar da kuma Ruhun. Idan shaitan ya yi maka magana a kunne cewa “Ai za ka fadi,” Ruhun zai mai da martani cewa, “ka yi imani da Allah.” Shaitan zai ce, “Ai da kasa,” Ruhu Mai Tsarki zai munfasa maka cewa, “Kana da dukan iyawa ta wurin ikona.” Shaitan zai nace cewa “Ai kai kadai ne kawai,” Ruhu Mai Tsarki kuma zai yi maka alkwali cewa, “Ina nan tare da kai a Kullum. Ba zan taba barinka ko kuma in yashe ka ba.”
An bar ka da wanda za ka zaba, ko kumaji a nan. Ko da a ce bangaskiyarka ta sauko kasa sosai kuma zuciyarka ta ksarki, ka ta kasa cewa amin ga kalmomin Ruhu Mai Tsarki, ka rike kalmomin gaskiya gam. Ka da ka bar motsi ta jiki ta gaya maka irin tunanin da da za ka karbba. Ka jimre da maganar Allah domin jikinka za ta zo ta bi baya ta kuma tashi ta yi yabo, har ta ji lallasa da murna irin ta Allah.
Ruhu na Gaskiya

Mun rigaya mun yi magana a kan cewa Ruhu Mai Tsarki yana fadin gaskiya ne kurum. Shaitan makaryaci ne, amma a cikin Ruhu Mai Tsarki, babu ko tabon kuskure, ko kasawa ko kuma yaudara.

“Amma sa’anda shi, Ruhu na gaskiya, ya tafo, za ya bishe ku chikin dukan gaskiya... (Yohanna 16:13)
Gaskiya tana kawo yanci! Yesu ya ce, “...zantattuka wadanda na fada maku ruhu ne, da rai kuma (Yohanna 6:63).” Shaitan yana neman ya daure mu da karya. Amma Ruhu na gaskiya na yantar da mu. Karya na kawo mana hallaka. Gaskiya kuma na bamu rai.
A yayin da ka ke karanta Littafin Allah a cikin addu’a, ka kasa kunne kana jin kalma daga bakin Allah, ka kuma rubuta rahoton wannan kalma, ka dauwama a gabansa, shi kuma za ya yi maka magana ba tare da wata cikas ba a cikin zuciyarka. Dole mu zabi kalmarsa mu kuma yi kiwonta a zuciyarmu kafin ta zaba mana ‘ya’ya ta adilci a rayuwarmu. Dole ne mu lura cewa ba mu bar wata tunani a zuciyarmu ba sai dai irin ta lallasa da kuma gaskiya. Ka yi nazari da ayoyin da aka jera a shafin nan ta gaba. Ka yi alkawarli a zuciyarka cewa idan ka dago karya ta iblis, kamar wadda ke bangare ta daya (wato a hagu) sai ka nace a zuciyarka ka yi kiyayya da ita, ka kuma yar da shi kasa, ka kuma canza ta da kalma ta Gaskiya wadda ba ta da karshe, kamar yadda aka jera a bangare ta biyu (wato hannun dama).
Mai Kada Duniya

A kullum Ruhu Mai Tsarki na neman ya lallashe mu ta wurin sa haske a zuciyarmu game da maganar gaskiya a zuciyarmu. Irin wannan hali ta kwanciyar rai da alheri tana barbada irin aikinsa a dukan rayuwarmu, ko da a ce yana yi mana magana ne game da zunubanmu.


“Shi kwa, sai’anda ya tafo, za ya kada (ja hankali) duniya a kan zunubi, da adilchi, da shari’a (Yohanna 16:8).”
Kalmar nan ta “kada” ta fi kyau a juya ta “ja hankali” ko kuma “kawo yarda” idan an ce kada, yawancin lokaci muna tunanin abu mai kawo jan baya ne kurum. Amma, a kowane lokacin da Ruhu Mai Tsarki ya yi magana a kan wata zunubi a rayuwarmu, yana yin ta ne domin neman cin gabanmu ne kurum. A maimakon ya cika mu da juyayi ta alhaki da hukunci, sai ya kirawo mu a hankali zuwa ga girma cikin adilci. Yana karfafamu mu canza halinmu da ayyukanmu ta wurin kaunarsa da alherinsa.

Tunani na Shaitan Jan Baya da Hallaka


Tunani na Allah Cin Gaba da karfafawa


Ba zan iya ba...




Na iya yin abu duka a chikin wannan da ya ke karfafata (Filibbiyawa 4:13)


Ina Cikin Rashi...


Allahna fa za ya biya kowache bukatata gwalgwadon wadatassa chikin daraja chikin Kristi Yesu (Filibbiyawa 4:19).


Ina Tsoro...


Gama Allah ba ya ba ka ruhun tsorata ba amma na iko da na kamna da na lafiyayyen hankali (Timothawus II 1:17).


Ba ni da bangaskiya...


Allah ya diba ma kowane mutum rabon bangaskiya (Romawa 13:3)


Ba ni da karfi...


Ubangiji shi ne karfin raina (Zabura 27:1)


Shaitan ya sha karfina


Shi wanda ke cikina ya fi wanda ke cikin duniya girma (Yohanna ta I, 4:4)


An Kada ni...


Allah na ba ni nasara a kullum


Ban san Abin da zan yi ba...


An zamadda Kristi Yesu a gareni hikima daga wurin Allah (Korinthiyawa 1, 1:30)


Na amince zan yi ciwo jefi jefi...


Ta wurin dukansa da ya sha na warke (Ishaya 53:5) shi da kansa ya karbi kurnamanciha, ya danki chichiwutanmu (Matta 8:17)


Ina cikin damuwa sosai da kasawa...


Ina zuba dukan damuwata bisansa, domin yana kula da ni (Bitrus I, 5:7)


Ina cikin kulle...


Inda Ruhun Ubangiji ya ke nan akwai yanci (Korinthiyawa II, 3:17)


Ina ji kamar an yanka mani hukunci...


Babu kayaswa a gareni yanzu domin ina cikin Kristi Yesu (Romawa 8:1)


Shaitan yana neman ya bazattar da mutuncinka, domin ya mamaye ka ya kuma hallakaka. Ruhu Mai Tsarki ruhu ne mai hankali, a sannu ne ya ke kira mu domin mu kawas da zunubanmu, mu kuma adana kanmu da adilci mu kuma gane shari’a ta gaskiya. Shi ne “Ruhu ta Rai”, wanda ke yantas da kai daga zunubi da mutuwa (Romawa 8:2). Shaian na kora amma Ruhu Mai Tsarki na jawowa shaitan na bida a dole, ammma Ruhu Mai Tsarki na shawara a sannu.




Mai Ginawa

Duk shawara ta sannu daga kalma ta gaskiya wadda ke nuna mana zunubanmu da kuma hanyar adilci za ta kara mana ginawa a karshenta, idan mun yi biyayya ga kalmarsa, ba za mu taba barin fuskar Allah ba in ba tare da ruhohinmu sun sami ginuwa ba.


“...Amma wanda ya ke annabchi yana yi ma mutane zanche na ginawa... (Korinthiyawa I, 14:3).”
Idan Ruhu Mai shawara ya magana ta wurin annabci zuwa ga ikkilissiyarsa asalin hidimarsa ita ne ya gina ta zuwa daraja ko da ace yana muna wata algus ce ko kuma kuskure, duk wannan hanya za ta sa shi mai ji din ya karu ya kuma sami karfafawa.
A cikin dokoki na Shari’a, ya kamata dukanmu mu hallaka. Amma ta alherin Kristi, mun sami rai na har abada. Za a iya fuskance mu a cikin zukatanmu ta hanyoyi biyu:1) ta wurin Shari’a, da kuma mabiye wato hukunci, ko kuma ta 2) da alheri da tausayi (jinkai) ta wurin jini da adilci na Yesu Kristi. Dole mu yi lura sosai mu ga cewa mun karbi kalmomin da ke bamu alheri, da rai da ginawa kurum. Kuma mu yi hankali mu fadi Kalmomi wadanda za su Karfafamu, da ginawa da kuma gyasta mana bege kurum. Mu mun zama ministoci masu kawo sulhu, ba tuwanmu da daukar rahoto na ban tsoro da hallaka.

Me ka ke yi da kanka idan ka yi zunubi? Kana iya karban alheri da tausayi wanda Kristi ke bayarwa idan ka tuba? Kana iya tashi tsaye ka ci gaba da ta fiya cikin Ruhu idan ka fadi? Ko kuma tana ta zama kana ganawa da ji ta alhaki na dan lokaci, har ka yi ta gunaguni da marin kanka a zuciyarka domin ka sake faduwa kuma?

Tana bani wuya in karbi gafara ta Kristi. Idan na fadi a kan wani hali wanda na sha fadiwa a kanta, sai na ji kamar akwai wani abin da sai na yi kafin in sami sulhu fiye da yin tuba kurum. Sai nawa nake zuwa a gaba Ubangiji a cikin tahotuna, da kuka da tuba. Shi kuwa zai amsa a hankali cewa,” Dana, na yi maka aikin gafara.” Sai in a gaba cewa, “Amma, ya Ubangiji ba ka san irin yuyayi na tuba wanda na ke ciki ba.” Sai shi kuma ya sake cewa, “Na yi maka aikin gafara, dana.” Amma sai ka ji wani abin na sa ni in roge darajana domin in ki karban wankewarsa da kuma karfinsa na cin gaba a cikin adalinsa. A karshe sai ya barke mani a cikin wadannan Kalmomin cewa, “Markus, Ni na gafarta maka. Kai ba za ka gafarta wa kanka ba?”

A shekaru masu yawa ina kayas da kaina, ina ta kaskure a cikin tunanina cewa Ubana Allah ne ya ke Kayas da ni. Ta wurin koyon jin mursa ne na uja yantas da kaina daga dauri na magabci da kayarsa zuwa ga yanci da gafara. Littafi ta ce, “Babu kayeswa fa yanzu ga wanda ke chikin Kristi Yesu (Romanwa 8:1).” Na amince da wannan ayar amana ba na ganin yalwatarta a rayuwata. Akwai Kayaswa a gare ni, ko ma da shike ina cikin Kristi! Sai bayanma soma gani da jin muryar Allah a zuciuyata kafin na some gane tushen wannan kayaswa. Da na zo na gane Allah, sai na soma ganin irin alherinsa da aikin gafararsa, shi ba mai marimarin sharanta mutum ne yadda ni na ke daukarsa a daiba.


1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət