Ana səhifə

Karban shawara daga wurin allah "Masu-albarka ne masu-tsabtan zuciya gama su za su ga Allah." Daga


Yüklə 361.5 Kb.
səhifə9/11
tarix25.06.2016
ölçüsü361.5 Kb.
1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11

YADDA ZA KA YI ADDU’A A LOKACIN BAKIN CIKI


A wata shahararriyar littafi wanda Tim LaHaye ya wallafa mai lakabi a turanci, How to win over Depression (Yadda za ka ci nasara bisa bakin ciki), ya yi magana game da wasu dalibai na wata makarantan koleji ta Kirista masu kokuwa da illa ta bakin ciki. Aka raba wannan yara zuwa sashi har guda uku. Sashi na farko sun sami taimako da shawara akan yadda za su bunkasa rayuwarse daga wannan illa ta wurin inganta kansu ta hannun amfani da kwakwalwa. Sashi na biyu kuma suna haduwa domin yin addu’a tare da mai bada shawara, shi yana ba su shawara da mataki na yin addu’a daidai yadda Allah ke so. Sashi na uku kuma ari aika su gida doni siu yi addu’a akan wannan danmwarsu. Sakamakon wannan ta ba kowa mamaki kwarai. Sashi na biyu wanda an koya masu hanyar addu’a ta fi sauransu duka samun lafiya. Sashi ta uku, wanda an galgadesu su yi addu’a kurum ba tare da taimako ba, sun nuna rashin karuwa har ma wasun su sun kara nuna wannan bakin ciki fiye da na da. Wannan ta nuna mani cewa akwai wasu hanyoyi ta addu’a masu amfani masu taimaka domin warkar da bakin ciki, akwai kuma wasu hanyoyi wadanda ba su da amfaoi.

Zabura 31 ta nuna hanya mafi kyau domin addu’a ga mai bakin ciki. Ba za me rubuta dukan wannan sura a Nan ba amma ina galgadinka ka karanta dukan wannan sura a cikin Littafinka.

A cikin nawa Bibul an ba wannan Lakabi “Zabura ta kawo kuka da kuma yabo” A wannan lokaci ta rubutu ta yi kamar Dauda na fuskantan irin matsalolini da muka ambata a cikin wannan littafi dazun. Hali ta rayuwarsa suna nan a birkice, kuma zunubansa suna danne masa kai ga kuma rashin lafiya ta jiki. Amma duk da wadannan matsaloli ta koma baya a rayuwarsa, dubi yadda ya fara wannan zabura:
“Ya Ubangiji, a gareka ni ke dogara:

“Kada ka bar ni in kumyata har abada:

Ka cheche ni chikin adilchinka.

Ka karkato kunnenka gareni, ka cheche ni da hamzari:

Ka zama pa mai – karfi gareni, dakin maraya domin, chetona

Gama kai ne pana da marayata.

Domin wannan sai ka bishe ni, ka

Nuna mani tafarki sabili da sunanka…..

Gama kai ne marayata.”
Dauda bai fara wannan addu’a a nan da nan da kawo kukansa ba, A maimakon haka, ya kafa ido ga Ubangiji, ya kuma sa hankalinsa ga aikin nagarta da kuma albarka na Allah, bayan haka ya yi shiri a gaban Allah. A nan shi Dauda ya bi ka’ida ta daidai. Ya furta begensa da bangaskiyarsa na yin aikin Allah. Tun daga farko shi ya kafa idonunsa a wuri ta daidai.
A aya ta 6 sai ya fara magana game da damuwarsa, a karshe kuma, a aya ta 9, sai ya fara kawo bacin rai da bukatunsa a gaban Ubangiji.

“……. Gama chikin kunchi ni ke. Idona yana shachewa domin bakinchiki, I, da raina duk da jikina. Gama na yi kwanakin raina da bakinchiki, shekaruna kuma da ajiyar zuchuiya: karfina yana kasawa sabada muguntata, kasusuwana kuma sun dudduge ……”

Rayuwarsa dai ba da lafiya ba. Masu gaba da shi suna ta neman su hallaka shi. Abokansa sun nuna cewa ba su san shi ba. An kuma bata sunansa a dukan kasar. Alhakin zunubansa sun yi masa nauyi, kuma jikinsa ta fada cikin ciwo da zafi. Amma nan da nan da ya zo wurin fuskar Allah, ya fara bayana dukan tsoronsa, da fushinsa, da rauninsa da kuma bain rai nasa. Amma ba ya tsaya a gurin ba. Idan addu’oinmu suna cike da zance na damuwarmue ne kurum, rai ta fita daga cikin ta kenan, kuma mutuwa ta sami zama daram kenan.

Bayan Dauda ya furta dukan damuwarsa a gabar Ubangiji, sai ya karfafa bege da danganarsa ga Allah wanda za ya cece shi daga dukan wannan.

“Amma na dogara gareka, ya Ubangiji…

kwanakina chikin hannunka su ke:

ka cheche ni daga hannun makiyana, da

wadanda ke tsanantanta …….

Ya Ubangiji, Kada ka bar ni in kumyata….

Ka bar lebuna masu karya su kawaita”

Daga aya ta 14 zuwa 18, Dauda ya gaya wa Ubangiji yadda shi ya ke so a yi da wannan matsala, amma duk a cikin wannan ya karfafa cewa Ubangji shi ne mai iko kuma yana da iyawa ta wurin cetonsa.

A karshe, cikin ayoyi na 19 zuwa 24, Dauda ya kalmasa addu’arsa da yabo, bangaskiya, kauna da kuma bege.

“Ina misalin girman alherinka, wanda

Ka ajiya ma wadanda ke tsoronka,

Wanda ka aiki kuma eabili da

Masu – dogara gareka, yan adam!

Albarka ga Ubangiji. Gama ya nuna mani rahamassa mai – ban mamaki

A chikin birni mai – karfi.”

Sai bayan mun taba Allah ne kurum kafin mu iya ganin juyawar wahalunmu zuwa yabo da kuma farinciki.

Sai bayan kuma mun ji kalmarsa na ta’aziya da hikima, da kuma ganin wahayi nasa na farinciki a gaban mu kafin mu fito daga ramin nan ta bakin ciki zuwa nasa haske ta farinciki.



TAKAITAWA


Tushen bakin ciki ita ne jin tausayin kai, wanda tana fitowa daga rashin zura wa Allah ido duka. Akwai ababa da yawa wanda za su iya jefa mu zuwa wannan “Korama” ta bakin ciki. A cikin wadanda muka fi sani su ne, matsaloli ta rayuwa, rashin furta zunubi, addini, rashin da’a rashin lura da jiki da kuma cuta ko rauni ta jiki. Dukan wadannan matsalolin za mu iya cin nasara akan su, idan mun juya hankalinmu zuwa ga Allah mu kuma yi shiru a gabansa, mu kuma ji muryar Allah, muna ganin wahayinsa muna kuma yin biyayya ga ita.

Ni ban ce wannan babi tana kumshe da dukan amsa ta wannan illa ta bakin ciki ba. Na bada amsa ne wanda na ga ta taimakeni da kuma wadanda na taimake su da irin wadannan amsoshin.



AMSA


Ko bakin ciki ta zama wata damuwa a rayuwarka? Kamar yaya ne take domun ka a kullum? Ko ka taba ganewa cewa ka daina kafa bege ga Allah a irin wadannan lokatan?

Ko kana cikin wannan illa ta bakin ciki a yanzu? Ka san abi da ta tsokano irin wannan illa mai sa ka shiga cikin wannan duhu? Kana yarda ka zo wurin Yesu a yansu, ka kuma yi shiru a gabansa ka kuma bar shi ya yi magana ta bangaskiya, da bege da kuma hikima, domin a gyare ganinka na sha’anin harka ta Allah? Kana so ka ga Allah a rayuwarka da duk ababan da ke aukuwa a rayuwaka? Ka yi wannan yanzu domin ka shiga cikin farin cikin Ubangijinka.


Babi Na 11

1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət