Ana səhifə

Karban shawara daga wurin allah "Masu-albarka ne masu-tsabtan zuciya gama su za su ga Allah." Daga


Yüklə 361.5 Kb.
səhifə11/11
tarix25.06.2016
ölçüsü361.5 Kb.
1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11

TAKAITAWA


“Hakika, hakika, ina che maku, kwayar alkama idan ba ta fadi a chikin kasa ta mutu kuma, sai ta zamna ita dayanta; amma idan ta mutu sai ta bada yaya dayawa. Mai – son ransa yana batar da shi ke nan: shi kwa wanda yana kin ransa a wannan duniya, za ya rike shi zuwa rai na har abada (Yohanna 12 :24, 25).” Mutuwa da tashiwan matattu su ne mabudi ta ai madawwani. Idan mun rike rayuwar mu kim kim, muna neman yancein kanmu, mu na kuma yin shagali da zunubi, to mun nasa rai ke nan. Amma idan mun onika ranmiue, muka ki neman yancinmu, muna kuma manne wa Kristi, za mu sami wannan aukuwa ta tashiwan matattu. Iri ta adilci za ta fara tsiro, za mu kuma zama aljanna ta salama a wannan busasshiyar duniya.

AMSA


Ko Ruhu na yi maka magana game da wata sashi ta rayuwarka wanda yana bukata a giciye ta? Ko za ka sami naka Jathsaimani, naka wuri ta addu’a wanda za ka sami zarafi ka yi addu’a har sai ka sani nasara? Ko za ka saurara wa wannan murya mai sannu ta Ruhu wanda ke cikin ka, mai ba ka hikima, ganewa da kuma alherie? Ko kana da marimari ka karbi wannan wahayi wanda Yesu yana so ya saka a royuwarka game da rayuwa ta tsarki da kuma ta tsabta? Za ka manne ga Maganarsa ka kuma zuba ido ga wahayinsa kurum, domin ka bar shi ya jagorance ka cikin mutuwa zuwa cikin rai na tashiwan matattu?

Babi Na 12

GANIN ALLAH A CIKIN DUKAN

AL’AMURA


“Masu – albarka ne masu – tsabtan zuchinya: Gama su za su ga Allah.” Mun rigaya mun yi bincike game da banbanci tsakanin abin da ake nufi da tsabtan – zuciya da kuma abin da ba tsabtan – zuciya ba. Mun bayana cewa zuciya mai tsabta ita ne wanda tana da yanci daga zunubi, tsoro, alhaki, fushi, rainin kai, bakin ciki da kuma aukuwa na da mai gurgunta cin gabanmu. Zuciya mai tsabta tana ciki. Masu tsabtan zuciya euna sanin asalinsu a cikin Kiristic,wanda ke kawo nasara bisa zunubi.

Tsabtan zuciya tana zuwa ne kurum daga aiki na Ruhun Allah. Ehawara ta yan’uwa cikin Kiristi na taimaka ta zama makami ta gyara da kuma warkasuwa, amma Ruhu ne kadai yana iya yi wa zuciya kaciya ya kuma tsabtar da ita. Ma’amala da Allah ta wurin yin tsit a gabarsa, da jin muryarsa, da hangan wahayinsa da kuma rubuta abin da mun gani da wanda muka ji ita ne daya daga cikin hanyoyi mafi amfani ta samun gamuwa da Kiristi mai rai. Idan mun rufe kunnuwanmu daga jin muryoyi masu jan hankulanmu, muka ki yarda da duk wahayi ta ban tsoro, da kasawa da kuma zunubi, kuma muka zuba wa Ubangiji da Mai ceto mai rai ido shi kadai, za mu taba. Yesu, kuma ta wurin taba, shi ne za mu sami warkasuwa.

Ga yawancinwu, samun tsabtar zuciya ta zama abin fama sosai. Ga wasu kuma wannan na nufin su bar duk fushi da kiyayya wanda ta mamaye rayuwarsu na shekaru masu yawa. Ga wasu kuma wannnan na nufin su koyi yadda za su ce a’a ga dukan matsalolin da ke neman hankalinsu a rayuwansu domin su ce I zuwa ga Yesu kurum. Ga wasu kuma wannan na nufin lokaci ta zuwa Jathsaimani ya yi, domin su sami iko da karfi ta jimrewa ga giciye domin su sami rayuwa cikin iko ta tashiwan matattu bisa kan zunubi. Ga dukan mu kuma, wannan na kira mu domin mu mayar da hankulanmu ga harka ta Allah, domin samun sabontaka na uja ganin Allah da kuma iya muryarsa a zukatanmu.

Bayan wannan doguwar tafiya ta koyo, to yaya za mu ci gaba da ajiye zuciya mai tsabta a kullum? Ta yaya za mu ci gaba da rayuwa cikin yanci daga danniya irin wanda ta rike mu a da? Yesu ya ce masu tsabtan zuciya za su ga Allah. Na bada gaskiya cewa: duk wanda suka ga Allah za su sami tasbtan zuciya. Domin haka na bada gaskiya cewa, Mabudi ta samun tsbtan zuciya a kullum ita ne ganin Allah a dukan Ko’ina.

Idan ina sujada, babu wuya in sami tsabtan zuciya. Ba ina nufin lokacin da ina waka kurum ba; ina nufin lokacin da na taba zuciyar Allah a cikin sujada. Idan ina sujada, ina zuba ido ga Ubangiji kuma a yayin da na ke dubawa, ina daukan irin kamanninsa. Damuwa tana zuwa idan na cire ido daga sujada na soma duba mutane, da aukuwa da kuma duniyar da ke kusa da ni. Nan da nan ina rasa ganinsa da kuma ikonsa! Domin haka, dole ne in koyi yadda zan iya ganin Allah a ko’inan da na duba.

Ina iya ganin Allah a tsakiyar dukan abubuwa domin “a chikinsa kwa dukan abu suna harhada (Kolossiyawa 1:17).” Ina iya ganinsa a dukan al’amura, domin shi ne “Wannan da ke cikata dukan abu bisa ga shawarar nufinsa (Afisawa 1:11).” Ina ganin Kristi cikin dukan cin gabata na ruhaniya, domin “… daga gareshi ku ke chikin Kristi Yesu, wanda aka zamadda shi hikima garemu daga wurin Allah, da adilchi kuma da tsarkakewa, da pansa (Korinthiyawa 1:30).” Ina ganin shi a tsakiyar raina, da motsi na da kuma rayuwata, domin “chikinsa mu ke rayuwa, mu ke motsi, mu ke zamanmu (Ayukan Manzanni 17:28).” Zan iya ganin Allah a Ko’ina, domin yana nan a ko’ina. “Ina za ni in rabu da ruhunka? Ina za ni kwa inguje ma fuskarka? Idan na hau zuwa chikin sama, kana chan. Idan na yi shimfidata chikin Lahira ga ka a chan kuma. Idan na dauki fukafukan assubahi, Har in zamna chikin matukan nisan teku; Har chan ma hannunka za ya bishe ri,Hannun damanka za ya rike ni (Zabura 139:7-10).” Dauda ya koyi cewa ko da a ce yana cikin mugun wuri ne, ko da a ce Lahira da kanta, Allah yana wurin kuma masu idanun bangaskiya na iya ganinsa.

Annabi Habakkuk ya yi magana game da wannan rana mai daraa wanda dukan duniya za su ga irin yadda Dauda ya gani: Gama duniya za ta chika da sanin darajar Ubangiji, kamar yadda ruwaye sun rufe teku (Habakkuk 2:14).” Ka lura, shi bai ce wai wata rana tana zuwa na daukakar Ubangiji a bisa duniya ba. A gaskiya, wannan rana ta rigaya ta iso nan ko kuma tana nan da mu tun daga farkon halitta. Amma, sanin wannan daraja ne ake zance akai, wato iya gane wannan daraya, wanda za ta mamaje dukan dunija. Bayan mutum ya fadi, ya rasa idanunsa na ganin zuwa cikin yanayi ta ruhaniya. Amma bayan mun sami hailuwa ta biyu, wannan ido tana sake dawo mana, amma idan dai za mu iya karban ta. Domin haka bari addu’ar mu a kullum ta zama, “Ka bude mani idanuna, domin in duba… (Zabura 119:18).”

ALLAH NA A BAYYANE CIKIN HALITTARSA


“Gama tun halittar duniya al’amura nasa da ba su ganuwa, watau ikonsa madawami da allahntassa, a sarari a ke ganinsu; ta wurin abubuwa da an halitta ana gane su; har kwa su rasa hujja (Romawa 1:20).” Akwai abu dayawa game da Allah wanda za mu iya gani cikin halittarsa. Ko da shi ke shi ne maahalacci, amma ya hada kome duka da Ruhunsa. Idan idanunmu na a bude, za mu iya koyi abu na Allah daga yanayi nuda hudu na halitta, wato su lokacin damina da rani, har ma za mu iya koyi abu daga tsunsaye da kuma dabbobi. Za mu iya gane wannan abokinmu na zuciya ta wurin ganinsa a cikin aikinsa ta halitta.

Akwai ayoyi da yawa masu yin magana a kan ganin Allah cikin dukan halittarsa.

“Ku kasa kunne ga karar muryatasa,

Da rurin da ke fitowa daga bakinsa.

Ya kan aike ta ta tafi har uyakar sama;

Walkiyassa kuma har iyakar gefen duniya.

Bayan wannan sai wata murya

Tana ruri: Yana tsawa da muryar

Sarautasa: Ba ya kwa hana

Walkiyoyin ba sa’anda an ji muryassa.

Allah yana tsawa da muryatasa

Abin ban mamaki; Manyan al’amura

Ya ke yi, wadanda sun fi karfinmu.

Gama ya kan che ma snow, fada

A kasa; Hakanan kuma ga ruwan

Zi’rnaniya, Da manyan hadduransa….

Sa’annan naman jeji su kan nemi

Mabuya, su kan zamna a kogunansu.

Daga dakin kudu hadari ke fitowa,

Daga arewa sai dari.

Daga lumfashin Allah a ke ba da

Kankara, Ruwaye masu – fadi kuma

Su kan daskare. I, ya kan labta

Ma kakkabran hadari kayan laima:

Ya kan shifimda girgije na walkiyassa.

Girgijen kwa ya kan juya inda

Allah ya nufe shi, Domin a yi

Iyakachin abin da ya umurta

A bisa fuskar iyakar duniya inda

Mutane ke zamne: ko domin foro ne,

Ko domin jinkai, ya sa shi shi zo.

(Ayuba 37:2-13)


Ga abin mamaki na nuna ikonsa na har abada!

Yesu ya kaimu ga halitta domin ya nuna mana irin hali ta allahntaka na Ubansa.

“Ku duba tsuntsaye na sama, ba su

kan yi shibka ba, ba su kan yi girbi ba,

ba su kan tattara chikin rumbuna ba;

amma Ubanku na sama yana chiyadda su.

Ku ba ku fi su daraja dayawa ba?…….

Ku lura da furaye na jeji, girman da

Su ke yi, ba su yi wahala ba, ba su

Yi kada ba: duk da haka ina che

Maku, ko Solomon, da darajassa duka,

Ba ya yafa kawa kamar guda dayansu ba.

Idan fa Allah ya kan yi ma ganyayen

Saura sutura haka, abin da ke rayuwa

Yau, gobe ana jefewa chikin tanderu,

Belle ku ….. gama Ubanku na sama

Ya sani kuna bukatar wadannan abu

Duka (Matta 6:25-34)”

Idan mun gani irin kauna da kuma jinkai wanda Allah na muna ga abubuwa na halittarsa wanda basu da daraja sosai, muna iya koyon irin halinsa ta kauna mara iyaka da kuma kulawa wanda yaria yi mana. Idan mun gan shi haka, bangaskiyarmu tana karuwa kuma zukatanmu su na samun warkasuwa.

A yayin da Dauda ya yi kokarin ya bayana irin iko ta Allahnsa wanda ba a iya gani da ido ba, sai ya yi amfani da halitta domin ya sani daidai kalmar da za ya yi bayani da ita.

“Rahamarka tana chikin sammai, ya

Ubangiji; Aminchinka ya kai har sammai

Adilchinka yana kama da duwatsun Allah;

Hukumtanka babban zurfi ne: Ya Ubangiji,

Kana kiyayadda mutum duk da

Dabba. Ina misalin darajar rahamarka,

Ya Allah! Yan adam kuma suna

Samun mafaka kalkashin inuwar

Fukafukanka. Za su koshi sarai da

Romon gidanra; za ka shayadda su

Kuma daga chikin kogin nishatsanka.

Gama a wurinka mabulbular rai ta ke:

A chikin haskanka za mu ga haske

(Zabura 36:5-9).”

Sai dai ka karanci girman halittar Allah kafin ka soma gane girman darajar hali na Allah.

Bari addu’armu a kullum ta zama, “Bude idanuna, ya Allah Ubangiji, domin in uja ganin ka a cikin halittaraka mai ban mamaki.”


GANIN ALLAH A CIKIN GIRMA TA RUHANIYA


Kafin in tuba in zama Kirist ina ganin kaina kamar ni ne nake sarauta na rayuwata, ni nake shirya kome na rayuwata, , kuma ina yin abin da na ga dama. Wannan kuwa ba gaskiya ba ne, domin ina hunnun mulkin wannan dan sarki na iska – wato ibilis, wanda ya na rudi na in ce wai ni ne mai iko da kaina.

Bayar na zama Kirista sai na ci gaba da irin wannan wawan tunani zuwa cikin sabon rayuwata. Domin ni mai bin Kiristi ne, ni zan yi biyayya ga Kirsiti in kuma yi rayuwa irin ta hali ta Allah, duk a ciki karfina. Ta dauke ni shekaru masu yawa na kasawa kafin na sani cewa mutum na jiki ba za ya iya aikata hali ta rayuwa ta ruhaniya ba. Ta wurin iko na Ruhun da ke aiki a cikina ne rayuwa ta Kirista ke faruwa a daidai. Idan na mance cewa na rigaya na mutu kuma Kiristi shi ne tushen raina a yanzu, zan sake fadi cikin wannan kokari ta kaina domin cikin wannan kokari ta kaina domin cika Doka, ta haka kuma zan rasa wannan zuciya mai tsabta wanda na karba.

Ba wai ba na kokarin in aikata adilci ba, amma ta wurin ikonsa ne, wanda ke aiki da karfi a cikina, kuma ta canza ni zuwa cikakken mutum a cikin Kristi (Kolossiyawa 1:28,29). Domin, haka, idan ana kira ni in aikata dokokinsa, sai in kowa baya zuwa cikina domin in kira wannan wanda shi ne kadai yana iya aikata wannan. Ga wata misali, Yohanna ya tunashemu cewa, “Idan muna kamnar junanmu, Allah yana zamne chikinmu, kuma kamnatasa ta chika a chikinmu (Yohanna ta 1,4:12).” A cikin karfinmu ba za mu iya kaunar kowa ba. Idan kuwa za mu ija yin kauna, za ta zama domin wannan kauna ta Allah wanda ke cikin mu ne kurum.

Idan akwai wata sashi ta rayuwa ta ruhaniya wanda har yanzu kana kokuwa da ita, ka zo ka mika wannan *** kokarinka ga wannan wanda shi ne ya uja kuma ya rigaya ya ci nasara ga wannan yaki. Ka sani cewa kai reshe daya ne kurum, wanda aka hada da babban itace, wanda kuma rayuwarka tana samun girma da tsirowa ta wurin wani na” Ka tambaye sji domin ya bude idanunka domin ka gani aikinsa a rayuwarka, ta wurin canza ka zuma irin kamannin sa.



BAYYANAR ALLAH CIKIN AIKI TA KULLUM DA KUMA BAUTA


Da a ce muna ciki siyada da cikin Allah kullum! Ba za ta yi mana wuya mu ga Kiristi ba! Idan mun yarda da wannan lalle muna bada gaskiya ga wata karya ta shaidan ke nan, mai cewa a banbataka tsakanin aiki ta dunija da kuma abu ta Allah. A cikin Kiristi babu banbarci. Dukan rayuwa tana zama aiki ta sujada ga wadanda suna gain Allah a cikin kome.

“Iyakar abin da ku ke yi kuma, chikin magana ko aiki, ku yi duka chikin sunan Ubngiji Yesu (Kolosiyawa 3:17)”. Ko a gida, ko a wurin aiki, ko majamia, ko da me nake yi ya kamata in yi ta zuwa g Ubangiji. Matayan aurw ku yi biyayya kamar ga Ubangiji (Afisawa 5:22). Muzan aure ku yi kauna kamar yadda Kiristi ya yi kauna (Adiawa 5:25). Yara ku yi biyayya ga iyayenku cikin Ubangiji (Afisawa 6:2). Ubanne, ku goyi yayanku cikin horon Allah (Afisawa 6:4). Masu aiki, ku yi biyayya ga wadanda suka ba ku aiki kamar yadda kuna yi da Ubangiji (Afisawa 6:5,6). Ku kuma masa ba da aiki, ku yi harka ta gaskuja da masu yi maku aiki a gaban Ubangiki (Afisawa 6:9)

Idan ka ba mai kishinruwa kofi daya na ruwa mai sanyi, kana yi wa Ubangiji ne. Idan ka ba mai junwa abinci, kana yi wa Ubangjij. Idan ka ziyarci marasa lafiya ko kuma wadanda ke cikin kurukuku kana yi wa Kiristi bauta ke nan (Matta 25:31-46). Idan idanunmu na bude, shi yana nan a ko’ina, kuma dukan abin da muke yi muna yi masa ne. “Iyakar abin da ku ke yi, ku aika da zuchiya daya kamar ga Ubangiji, ba ga mutare ba; da shi ke kun sani daga murin Ubangiji za ku karbi gadon da ya wajaba gareku: Ubangiji Kiristi ku ke banta ma (Kolossiyawa 3:23,24).”

Bari mu yi addu’a domin a bude mana idanunme domin me ija garuin Allah a cikin dukan al’amura ta sashi ta rayuwarmu, kuma bari dukan abin da muka fada da kuma aikata ta zama aiyada a gabar Ubangijinmu.


Allah NA A BAYYANE CIKIN YANAYI TA RAYUWARMU


Na bada gaskiya cewa abu mai wuya ne a ce Allah ya ba kowa yancin kai dolmin ya zabi abin da ya ga dama, kuma a ce wai shi yana kuma aiki da me ta wurin aikata nasa nufi . Wannan sabani ta gaskiya tana da wuya a gane ta. Godiya ta tabbata ga Allah domin ba sai an gane kome a cike ba kafin ya karbe mu amm shiyana neman bangaskiya mara lilo ne kurum daga wurin mu!

“Mun sani kuma dukan al’amura suna aikatawa zuwa alheri ga wadanda ke kamnar Allah, watau wadanda ke kirayayyu bisa kadarassa (Romawa 8: 28).” “ Shi wanda aka maishe mu gado a chikinsa, kadararru abu bisa ga nufin wannan da ke aikata dukan abu bisa ga shawarar nufinsa (Afisawa 1:11).” Tilas ne mu bude idanunmu ga duka motsin harnun Allah a cikin duk yanayin da ka a kewaye da mu.

Amma, za ka iya yin mamaki, akan cewa ai akwai mugayen hukumai da kuma shugabanne? Ai kan ba za a ce Allah ne ya kafa su a matsayi ta iko ba! “Gama ba daga gabas, ko daga yamma, ko kwa daga kudu, daukaka ta ke fitowa ba. Amma Allah ne mai – sharia: (Zabura 75:6,7).” To me za mu ce ga rashin adilcinsu a game da shari’arsu? Me za mu ce idan sun yanka hukunic wanda ba daidai ta ke da abin da Allah ke so ba? “Zuchiyar sarki tana hannun Ubangiji kamar magudanan ruwaye: Ya kan juya ta dukan inda ya ga dama (Misalai 21:1).” Domin na sani cewa Allah newa yafi karfin koware irin hukuma a dunija, zan iya mika kaina ga koware irin hukuma a rayuwata b tare da shakka ba. Ta wurin yin addu’a, ina iya murda kowane irin sarki, alkali da kuma mai bari aiki. Idan na yi addu’a da gaskiye cewa Allah ya bi da kalmominsu da kuma hukuncinsu, zan iya huta daga damuwa ko da me suka yi, domin na sani Allah ya murda zukatansu zuwa daidai yadda sli yake so. Na yarda,, idan na ki in yi aikina ta yin addu’a gaskije har da kawo kuka domin dukan hukuma, kamar yadda Allah ya umurta a (Timithawus ta daga 2:1,2), Allah na ija barin mugayan shugabanne marasa imani su yanka hukunci mara gaskiya domin a gyara mari kuskuri na a kuma jawo ni zuma dangana a gareshi.

Babu wuya ko kadan mu bada gaskiya cewa Allah ne mai iko duka idan muna cikin hali ta farinciki da kuma salama! Amma tana da wuya mu yarda cewa yana da iko a lokacin bacin rai da kuma bala’. Amma ta bada gaskiya ne za mu ija ci gaba da smun zunciya mai tsabta mu kuma sha karfin fargaba, shakka da fushi. “Ni ne Ubangiji, babu wani kuma; banda ni babu wani kuma, Zan danarche ka, ko da shi ke ba ka san ni ba: domin daga mafitar rana har ga mafadatta, su sani, babu wani sai ni: ne Ubangiji, babu wanina. Ni ke sifanta haske, na kuma halichi dufu; ni ma kawo lafiya ne, ni kuma mahalichin masifa ne; ni ne Ubangiji, da ke aika dukan wadannan abu (Ishaya 45:5-7).”

Tilas ne mu ga hannun Allah a dukan kome, mu kuma kasa kunne domin mu ji muryarsa domin me san yadda za me yi masa biyayya. Amma domin Allah ya bar wata bala’I ta shigo cikin rayuwarmu bala’in ba. Akwa lokace ta karba, akwai kuma lokaci ta cinnasara bisa masifar. Murya da wahayi ta Allah ne kadai za ta bamu jagoranci domin san ko me ta kamata mu yi.

Mutanen Yahudiya suna zama cikin hali ta tawaye na shekaru masu yawa. A kullum da kukullum muryar maganarsa na zuwa a garesu ta bakin annabawa wai tilas ne su tuba ko kuma su shiga cikin masifa da hallaka. Amma sun ki su yi biyayya. A karshe ranar cika shari’a ta adilicinsa ta gabato. Ya yi wa Irmiya magana cewa, “In ji Ubangiji mai – runduna fa; Tun da ba ku ji maganata ba, ga shi, sai in aiki in dauki dukan kabilan arewa, in ji Ubangiji, da Nebuchadrezzar sarkin Babila, bawana, in kawo su su yi yaki da wannan kasa da mazamnanta, da dukan al’ummai na wajen nan; inhallaka su sarai, in maishe su abin al’ajibi, abin reni, kufan har abda kuma “(Irmiya 25:8,9)” Saboda zumubanku, in ji Irmiya, wannan hukunci ta zo kanku. Domin haka ku yi biyayya da magabcinku, domin yana aikata aikin nan domin shi bawan Allah wanda ar aiko ya yi maku horo. Amma bayan lokacin hukunci ta shige, Ubangiji za ya sharanta shi Nehu chadrezzar domin irin yarda wanda ya yi na hallaka ku, kuma daga nan zan mayar da ku gida kamar na da. Amma a yanza wannan ita ce haka, ku nika kanku.


Wannan ba ta nufin cewa kullum sai mu tsaya cib mu zama marasa karfi a gaban magacin Allah. Anabi Elisha ya shiga irin wanna hali da mutanin Yahuda (Sarakuna 11, 6:14-23). Yana nan a kewaye da abokan gaba wadanda sun abko masa domin su kashe shi. Amma a nan ba mika kansa garesu ba. Domin shi mai hange ne, ya sani cewa mufi Allah a wannan lota ba domin ya yi biyayya ga magabcinsa ba amma ya nuna mulki. Ko da shi ke shi da bawansa su biya ne a daki, amma ya ce, “Gama wadanda ke tara da mu sun fi wadanda ke tare da su yawa”. An bude idanunsa domin ya ga runduna ta Allah domin haka ya yi magana ta bangaskiya. Karusai na mala’iku sun tsaya da shiri su hallaka magabatansa, amma dukan su na hannun iko na wannan bawan Allah. Amma, duk lokacin da Elisha ya yi magana, cewa “Ina rokonka, ka buga wannan al’umma da makamta,” sai Ubangiji ya bada amsa daidai da kukansa, Alisha kuma ya zama gwarzo.

Akwai lokaci na mika kai, akwai kuma likaci na cin nasara. Muna ija gane wannan irin yanayi in dai muna sa hankali mu san yadda ko me nene nufin Allah yake a lokaci ta wurin samun jagora ta wurin kalmarsa.

Abin ta’azuja ce sosai mu sani cewa Allah yana mulki ko ma idan muna cikin masifa rayuwarmu. Lokaci mafi wuya a garee ni ita ne idan Alla h yana kira ni ni yi kaura zuwa wata sabon farne ta aikinsa a rayuwata. Lokacin da wannan ta fara faruwa da ni ban ma san ko me ke faruwa ba. Duk abubuwa masu tushe a rayuwata suna ta rushewa kurum. Domin ban gani murgar Allah a zuciyata ba, sai na soma shakka, da fushi da kuma fidda rai. Domi ni mutum ne mai aikata abu nan da nan sai na fara neman wata sabon matsayi. Kaf daya ne kurum ta bude mani a ciki sauran. Domin babu wata hanya sai na sa kai ga wannan kofar. Ni ina gani cewa ai ina aikiata wannan domin matsi ne kurum. Amma daga baya ne nake ganewa cewa a she akwai hannun Allah mai jagoranceni a lokacin da ni ba ni da bangaskiya koma kome ta zama mani da duhu sosai. Abin farin ciki da kuma albarka ne lokacin da na gana cewa duk wannan lokacin Allahbai bar mulkinsa rayuwata ba.

Kaurata biyu ta zo a gareni bayan na rigaya na koyi yadda zan ji muryar Allah da kuma ganin wahayinsa. A nan kamar da kome ta zama hali ta koma baya. A wata loto sai in ciki da bakin ciki, ina cewa ci wasu suna neman su yi mulki a rayuwata. Amma bayan na yi magana da Allah ta wurin rubuta rahoto sai in ji yana cewa sli ne mai, kuma babu abin da ke faruwa da ni wanda ba shi ne ya kadara ba. Ya kuma nuna mani lokaci wanda takamata in yi magana ko kuma yi shiru, lokaci ta aikatawa ko kuma na tsayawa shiru, da kuma likaci ta mika kai da kuma lokaci ta nuna iko. Ba zan ce a yanza na shiga wannan hali ba tare da shakka ko kuskure ba, amma na ci nasara fiye da yadda na yi a farko.

A yanzu haka ina cikin wata lokaci ta canji. Taimakon Allah ne kurum ya sa na ija rubuta wannan littafi a wannan lokaci. Kowane rana ina samun zarafi domin in aikata abubuwan da naka gaya maku ku yi a wanna littafi. Na tabbata za ta yi maku aiki dmin tana yi mani aiki a ta wa rayuwa ta yau da kullum. A yanzu kuma ina dada karuwa fiye da da. Idan an ci mani mutunci, ina da tabbata cewa nufin Allah a rayuwata sai dai ni da kaina. Idan ina da zuciya ta aikata nufinsa, kuma ina tsabtacce zuciyata daga dukan ya yi mani alnarka maffici. Na bada gaskiya cewa babu wanda yana da iko daga sama (Yohanna 19:11). Domin yanzu na zama mai hange, ina rikon wahayi na abubuwan da Allah ya shirya mani, kuma wannan wahayi tana bi da ni ciki dukan lokaci ta masifa.

Ko da me ta ke faruwa da kai a yanzu, Allah yana mulkinsa yar wa yau. Ka tambaye s hi ya bude idamunka domin ka ga hannun sa na kauna akan. Ka bude kurnuwanka domin ka ji maganarsa an gaskuja.



TAKITAWA

“Za a che da sunansa Al’ajibi, Mai – Sha-wara …!:” Idan zukatanmu sun ji rauni, kuma ruhohinmu suka gurgunce, kuma ranmu ta ciku da shakka da kuma fidda rai, mu tuna muna da Abokiwanda fidda rai, mu tuna muna da Aboki wanda yana kaunarmu kuma yana bamu bege. Idan za mu yi shiru, mu kasa kumme, mu kuma duba, za ya yi mana magana ta warkasuwa da salama ya kuma ba mu wahayi ta farinciki da bega. Idan halinmu ta komo zuma irin gani ta Allah, zukatanmu za su zama da tsabta, domin mu iya ganin Allah a ko’ina.



1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət