Ana səhifə

Karban shawara daga wurin allah "Masu-albarka ne masu-tsabtan zuciya gama su za su ga Allah." Daga


Yüklə 361.5 Kb.
səhifə7/11
tarix25.06.2016
ölçüsü361.5 Kb.
1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11

BABI NA 10

DAGA DAMUWA ZUWA FARIN CIKI


Na tabbata ka san wadannan matsaloli kamar: bakin ciki, rashin bege, damuwa, kiyayya, kuka, rashin cin abinci (Ko Kuma mugun Kwadayi na cin abinci), tausayi da kuma rashin barci mai ni’ ima. Me za ta fi wannan mallakar harkokin rayuwarmu? Za mu iya Kirata bakin ciki ko kuma damuwa, na tabbata cewa kowa a cikin mu ya taba fuskantar wannan illa a wata lokace na rayuwarsa. A Kasar Amrika daya cikin kowane mutane takwas yana fuskantar wannan illa wadda har sai ya nemi taimako daga hunnun likitoci. Wasu masu yawa kuma suna iya ci gaba da illa a rayuwarsu cewa ai haka ne wahalar duniya ta ke, don haka ba su ma tunanin naman taimako

Akwai wata hanya wanda za mu me sami fita daga wannan tarko ta damuwa da bakin ciki? Akwai abin da za mu iya yi wanda za ta dawo mana da hask zuwa cikin rayawarmu? Akwai dalilin da za mu yi bege? Ina ba da nawa taraihi domin ta zama shaida, bayan shekaru goma gonna na kokuwa da bakin ciki na iska cewa, lalle, akwai hanya ta kubuta daga wannan illa.


MENE NE AKE NUFI DA BAKIN CIKI?


Za mu iya bayana bakin ciki ko damuwa kamar haka, “Barin matsaloli ta duniya ta mamaye mu, har mu manta da bangaskiyarmu ga Allah”. Bakin ciki na zuwa na daga sauraron muryoyi na karya da kuma zura wa wahayi ta karya ido. Idan na kasa kunne ga karya na magabci na kuma rafe kunnuwa na daga jin murya ta ta’aziya da hikima na Ruhun Allah, na fara gungura wannan hanya ta bakin cikin ke nan. Idan kuma na kafa ido ga yanayi na matsalolin da ke kewaye da ni; na sa hankali kuma ga yadda suka cukume ni har ina tunanin yadda zan yake su da kaina a maimakon tuna da alkawalin da Allah ya ba ni domin inganta rayuwata to lalle na bude kofa ga yanyi ta duhu da hallake ke nan.

Akwai wasu mutane kalilan wandanda wannan irin damuwa ba ta yawan taba su ba. Amma yawanacin mautane kuma suna jin irin wannan damuwa dan kadan ko kuma sosai a jefi jefi cikin rayuwarsu. Wasu kuma na nan cikin zurfin bakin cikin a kullu, wadda ke shanye dukan farin cikinsu ta kuma barsu kango. Amma kome lrin bakin cikin da ka ke ciki. “Ubangiji yana kusa da masu – karyayyar zuchiya, Yana cheton irin wadanda su ke da ruhu mai – tuba (za – bura 34 : 18)”. Ubangiji ya yi alkawali za ya bude maka hanya don ka kubuta!


ABUBUWA MASU KAWO BAKIN CIKI.

Kamar yadda na ambata dazun cewa na yi kokuwa da rauni ta bakin ciki na wajen shekaru goma a rayuwata na Kirista. Na nemi fuskar Allah da gaskiye domin ya ba ni hikima na cin nasara ga irin wannan mugun hali mai so ta hallaka ni. Na bada gaskiya ya amsa mani adduata ta wurin wannan zane wanda an nuna a shafi ta gaba.

A ta wajen wannan zane za ka ga misalin irin alamu ta jiki da na rai wanda bakin ciki ke jawowa. Wannan ta banbanta daga mutum zuwa mutum bisa ga irin sarin rayuwar mutum. Duk da haka, irin wanna halaye wanda a rubuta za su bayana a rayuwar kowane irin mutumin da ke da bakin ciki.

Layi ta biyu ta na nuna wasu matsalolin da ke jawa bakin ciki a kullum, sun kumshi ababa kamar su : tsanani daga harka ta rayuwa, zunubin da ba a furta ba, addini, ciwo ko kuma rashin aiki na wata sashin jiki, rashin kulawa da jiki da kuma rashin da’a. A kullum, idan an tambaye mu ko me ke kawo wannan ji ta bakin ciki, muna nuna daya daga cikin wadanan.” Ai rajuuaata na da wuya sosai. Ina ganin mura da zazzabi kama ni. Ban sami isasshen barci jiya da dare ba”. Tana zama kamar daga wadannan ne bakin cikin mu ke fitowa.

Amma ina so in sanar cewa wadannan ba dalilen da ke jawo bakin ciki ba amma yan tsokana ne kurum domin ingata bakin ciki. Wato, ba tsananin da na ke ciki a yanzu ne ke jawo mani bakin ciki ba. Idan gaskiya ce ai duk sauran mutane wadanda ke fuskantan wannan tsanani su ma za su zama da bakin ciki. Wannan dai ba gaskiya ba ne. A yayinda wasu na fadi cikin bakin ciki idan sun shiga tsanani, wasu kuwa na cin gaba da aikinsu a cikin ni’ima har su ci nasara daga duk tsananin da ke gabansu, har ma su sami sabon girma a cikin bangaskijarsu da kuma halinsu. Domin haka dole mu sa ke duba da zurfi domin mu sami tushen irin wannan hali ta bakin ciki.

Idan ka matso kusa da O na tsakiya, kusa da tushen abin da ke jawo bakin ciki, akwai wata sashi mai suna “Jin tausayin kai”. Wannan, ita ne abin da na bada gaskiya tana jawo dukan bakin ciki a rayuwar mutane. “Wayyo ni, rayuwata ta zama abin tausayi. Wayyo ni, ba na jin/ Lafiya jikina. Wayyo ni, ashe ai rayuwa ba ta da imani.” Tunani masu muni suna cika mana kai da ruhu nan da nan har idan cuta da tsanani da kuma yanayi ta balai’ in ta shigo rayuwarmu, babu wuya mu ga kanmu can cikin mugun rami ta duhu.

Amma wai, ta yaya ne ranmu ke cika da jin tausayin kai? A saukake, wannan na faruwa idan mun kauce idanunmu daga Allah da kuma nufinsa, sai mun fuskanta karya daga bakin shaidan. A maimakon mu dubi Yesu, sai mun sa hankalinmu ga irin rashin dadi ta matsalolic rayuwarmu. A maimakon mu yi shiru domin mu ji karamar muryar nan mai sannu a zukatanmu, mu mun dage da yakan abubuwa na jiki da zafin rai. Maganin wannan bakin ciki wadda mu ke ji ita ne mu ji muryar Allah da kuma ganin wahayi ta Allah. Amma bari mu binciki abubuwa masu tsokano bakin ciki t a sama sama a hankali domin mu ga yadda ka’idodinsu sun shafi juna.

TSANANI TA HARKAN RAYUWA


Ba kowa ne ke fuskantan tsanani ta rayuwa da hali iri daya ba. Wasu na ganin tsanani ne kurum, da jin zafi da kuma jin muryar mai hallaka ne kurum. Irin wadannan na amsa da fushi, konar zuciya da kuma bakin ciki. Wasu kuwa na amsawa kamar yadda Bulus da Yakub su ka umurta: “Yan – uwna, kadan jarabobi masu yawa sun same ku, ku maishe shi abin farincniki sarai……. (Yakubu 1 : 2).” “Ba kwa wannan kadai ba, amma mu yi farinchiki kuma chikin kunchinmu: muna sane kunchi yana faradda hankuri; hankuri kuma, gwadawa; gwadawa kuma, bege, bege kuma ba ya kumyataswa… (Romawa 5 : 3 – 5).

Ta yaya za a ce mana mu karbi wahala ko kuma kunci ba tare da mun yi gunaguni ba, amma wai mu yi tsalle da farin ciki a lokacin da kunci da damuwa ta zo kanmu? Akwai hanya daya ne kurum. Dole mu bada gaskiya cewa, “Shi Madaukaki Allah shi ne mai mulki a dukan duniya ta mutane” kuma cewa a kullum yana sa “Dukan al’amura suna aikatawa zuwa alheri ……..(Romawa 8:28).” Saninsa ta wurin karatu ta kai kurum ba ta isa ba amma sanin kaunarsa ga mutum ta wurin aukuwa da ke rayuwar mu na kanmu shi ke da matukar anfarin alkawalinsa a gare nue lokacin wannan bala’I wanda ke gaya mana ga cewa shi yana nufanmu da nagarta.

Ba abu mai wuya ba ne mu yarda cewa Allah yana amfani da mutane masu tsarki da gaskiya domin ya cika munufinsa. Ai su suna neman nufinsa domin su yi buyayya ga ita. Amma tana da wuya sosai mu bada gaskiya cewa ayukan mugayen mutane masu kishi da kiyayya na iya cika nufin Allah a rayuwarmu. I, wadannan kiyayya mugayen mutane masu aikata ayuka na sonkai ba su da dama su sami tuba. Amma wannan a gaskiya ba haka ba ne.

Allah ya yi wa Yusuf alkawali cewa za ya yi mulki bisa kowa a iyalinsa, har ma bisa iyayensa. Amma ba da dadewa ba an sayar da shi zuwa baranci a yayin da yana aikata wata aika ta babanshi, an kuma jefa shi zuwa cikin kuruki domin ya ki ya aikata halin lalata an kuma manta da shi bayan ya yi ma wasu hali ta kirki. Za ta yi wuya Yusufu ya bada gaskiya cewa hannun Allah na bisa kanshi. Na bada gaskiya cewa akwai lokacin da yana cikin duhun kurkuku wanda har ya kusa ya yi shakkar zancen da Allah ya yi masa har ma ya yi kusa ya ba fushi da bakin ciki dama su mallake shi. Amma littafi ta ce shi ya tsabtace zuciyarsa. Ba ya dunkule kansa zuwa wata lungu, domin ya yi ta lallasar tausayin kai ba, bai kuma zauna yana ta tunanin irin rashin gskiyar da aka yi masa ba, ko da shi ke yana da gaskiyarsa. Ba ya hau ma su rikonsa da fushi ba. Amma a kullum rahunsa na nan da tsabta, har ya sami farin jini a gabar masu rikonsa da wadanda sun saye shi. A kullum yana rikon kansa da daraja har ya sa masu lura da shi sun ba shi iko bisa sauran mutanen da ya ke tare da su. Ta yaya ne ya iya jimre ga irin wannan tsanani da kunci? Domin kullum a cikin zuciujarsa akwai wannan wahayi wanda Allah ya ba shi tun yana kamari, wanda ke karfafa shi da kuma cika shi da bege da kuma bangaskiya. Wannan wahayi ta sami kafuwa sosai a zuciyarsa, domini haka ya iya karban masu yi masa makirci da kauna da kuma gafara, ya bada geskiya cewa su sun shirya masa mugunta, amma Allah ya maida komai ta zama nagarta (Farawa 50).

Manzo Bulus ya sha azaba sosai a rayuwarsa na Kirista. An jefe shi da duwatsu, an buge shi, an jefa shi cikin kurkuku, an kuma yi masa ba’a. “Mun matsu ga kowane sashi, amma ba mu kuntata ba; mun damu, amma ba ya kai fidda zuchiya ba; ana binmu da tsanani, amma ba a bar mu yasassu ba: an fyada mu a kasa. Amma ba a hallaka mu ba (Korinthiyawa 4:8,9).” Me ya sa har ya iya shan karfin wadannan matsi har ye rubuto daga kurkuku cewa, “Ku yi farinchiki chikin Ubangiji kullayaumi: Sai in sake chewa ku yi farinchiki !” Me ya sa bai fidda rai ba? Domin ya sani cewa duk wannan na faruwa da shi a kan wata dalili wadda za ta kawo sakamako ta nagarta: “Gama dukan abu sabili da ku ne, domin alheri, da ya ribanbanya ta wurin masu - yawa, shi sa godija ta yawaita zuwa darajar Allah (Korinthiyawa 4:15)”. Wahayin de Allah ya ba shi ita ne shi ya zama manzo na bishara Kristi zuwa ga al’ummai. Wannan ita kadai ne burisa, kuma duk wadannan matsaloli suna zama hanyoyi ne ta cika wannan. Allah na amfani da wahalasa domin ya aikata alheri zuwa cikin rayuwar wasu. “Gama kunchinmu mai sauki, wanda ke na lokachi kadan, yana aika dominmu nauyin daraja madawami gaba gaba kwarai muna nan ba mu lura da al’amuran da ke ganuwa, amma sai da marasa – ganuwa: gama al’amuran da a ke gani na zamani ne; amma al’amuran da ba su ganuwa madawama ne (Korinthiyawa 2,4:17,18)”. Da ya gwada irin farinciki ta rai madawwami wanda za ya samu tare da wadanda sun tuba zuwa wurin Kristi ta wurinsa, duk wahalun da ya ke sha sun zama kamar wasa ne kurum. A zamansa cikin kurkuku, cikin daki mai kazanta, kuma da jini na zuba daga dukan da aka yi masa, tunaninsa ba ta ga abubuwa ta duniya ko kuma zafin da ya ke ji daga jiki. A maimakon wannan, sai ya zura wa gaskiya ta har abada ido, wanda ba a gani da ido ta jiki, amma sai ta ru’ya ta Ruhu wato ceto ta har abada na rayuka.

A shekarun da suka shige, Ubangiji ya jagoranceni domin in sanka daga matsayina ta fasto a wata ikkikisiya. Domin ina da mata da kuma yara kanana guda biyu a hannuna, sai nan da nan na yi tunanin neman aiki. A wannan lokaci akwai wahalar samun aiki sosai, amma wannan ba ta dameni ba, domin ni mai jin dadin aiki ta hannu ne sosai, idan dai aiki ne ta gaskiya. Tunani ta ta fari ita ne in riga faskaren itace da kuma sayar da ita. Na yi girma daga gona ne, kuma ina murna domin in koma zama a cikin kurmi kamar ta da. Bayan ‘yan makonne, komai ta tafi daidai, kuma albashi mai kyau tana shigowa. Sai nan da nan na iske ba zan iya cin gaba da wannan ciki mai tsanani ga jikina ba. Tun ina yaro na ji wata rauni a kwankwasona, amma tun da ina lallabawa da ita. Amma saboda yawan matsi ta faskare da kuma dako, sai wannan ciwo ta farfado sosai.

Na yi godiya ga Allah domin na saba da rubuta rahoto, ta wannan hanya ce na koma wurin Allah a wannan lokaci ta tsanani domin neman hikima. Na fadi damuwa na akan rashin iyawana ta wurin ciyar da iyalina domin ciwon da ke damun hannun damana. Na gaya masa damuwana akan yanda zan dauki nauyin iyalina da wannan irin matsala. Na roke shi domin ya warkar da kwankwasona domin in iya yin aiki. Amma ya amsa mani, cewa, “Markus, ba ka amince da ni domin in baka kudi ba. A kullum kana amince da iyawar kanka ne kurum domin samun biyar bukata. Ina so ka sani cewa ni ne tushen biyar bukatarka, za ka iya amince da ni, ko da a ce dukan kokarinka ta fadi kasa. Ba na so ka yi aikin faskare ko kuma aiki a ma’aikata. Na kira ka domin ka koya wa mutanena. Ba na so ka nemi wata aiki mai biyan albasni a yanzu. Yanzu Ina so ka yi wa wani kungiya ta Kirista aiki ta yardan rai. Ka amince da ni ni zan dauki nauyin biyan albashinka.”

Ina fata da na ce na yi biyayya ga kalmar Ubangiji, a ana da nan. Ubangiji, a ya fadi gaskiya. Ban ta ba amince da shi domin samun kudi ba. A gania bata kamata mutum mai lafiya ya yi zaman tukuru ba, dole ya tashi ya ciyar da iyalinsa idan yana da karfi. Domin haka Ubangiji ya gurgunta ni domin ka da na iya yin komai. Ya ki ya warkar da bayana kuma wannan ciwon ta ci gaba, domin haka na shiga yanayi ta matsuwa sosai. Wannan sako ne shi ya yi ta maimaitawa a cikin rahotona kullum. A karshe, na yarda da maganarsa, na daina nema aiki, na kuma fara aikin yardar rai da watan ikkilisiya wanda ya nuna mani. Daga wannan tunanina ta zama cewa tun da na yi biyayya da maganarsa, za ya ce ai na bi maganarsa da bangaskiya domin haka za ya ba ni wata aiki mai biyan albashi. Wannan ashe kuskiri ne na yi. Cikin watanna takwas ina nan cikin rashin aiki. Ba ni da gida, babu mota kuma babu albashi, domin duk kayana na da duka na ikkilisiya wanda da na bari ne. Kowana mako sai in tuna masa da wannan zance ta rashin aiki, kuma kowane mako za ya gaya mani, “Ka jira, ka amince da ni.” Sai a hankali na soma gane irin aikin da ya ke yi a rayuwata. Ya dauki nauyin iyalina ta wurin ba mu gida da kuma mota. Ba a kuma bi mu bashi a dukan harkarmu ba. A karshan wannan watanne na rashin aikin, mun sami ragin kudi sosai fiye da dukan rayuwar aurenmu. Ni dai ban san yadda ya yi wannan ba, amma ya nuna mani cewa shi mai mutunci ne wanda zan iya amince da shi a kowane lokaci. Bayan wannan ne sai ya bar ni in nemi aiki mai biyan albashi.

A wadannan watanne takwas, akwai lokatai wanda zan dubi yadda Allah da mutanensa suna bi da ni, duk da aikin kirki wanda na yi da zuciya daya a garesu, ni ban yarda cewa suna bi da ni daidai cikin mutunce ba. Idan na bar yanayi ta rayuwata su mamaye hankalina, babu wuya in fadi cikin bakin ciki. Amma idan na zura ido ga kalma da kuma wahayin Allah, cewa zan zama mutu na Allah mai kwari da kuma bangaskiya mai karfai agareshi, ta yaya zan nuna sanyin gwiwa? Ko da shi ke duk wannan aukuwa ba yi na bane, kuma yawancinsu sun zo mani da tsami, amma na sani akwai dalili a cikinsu duka! Allah na kan aikata ikonsa a cikinsu duka kuma yara yin kome domin nagarta a gareni.

Allah ya yi alkawali cewa, duk wannan matsi mai zuwa kanmu za ta haifar da daukaka mai girma za ta har abada, wato kayar ado mara lalaxcewa da mai kyau. Amma wannan alkawali tina sharadi. Cikakken nufin Allah a ruyarmu za ta bayyana idan “Ba mu lura da al’amuran da ke ganuwa, amma sai da marasa – ganuwa.” Dole mu cire idanunmu daga ciwon, mu kuma kafa ta a bisa daukaka mai zuwa. Ka da mu dubi yadda abin take zuwa amma mu duba karshenta. Bacin rai namu a yanzu ba abu ta har abada ba ne, ko da shi ke suna zama da mu har na tsawon watanne ko ma shekaru. Idan mun gwada ta da al’amura ta har abada ai duk wannan abu kadan ne kurum.

A lokaci ta matsi, ko kuma gwadawa ta rayuwa, muna bukatan wahayi. Dole, mu tambayi Ubangiji ko me ya ke yi ta wurin irin wannan al’amari. Dole mu samo wahayi wanda za ta kai mu har zuma ga haye wannan al’amura. Idan za mu ji muryar Allah, mu kuma nemi wahayinsa, mu kuma dangana ga abin da muka karba, ba ta kamata fidda rai ta kawo mana hari ba, amma za mu iya zama zakara masu cike da farin ciki da kuma alherin Allah.

RASHIN FADIN LAIFINMU

Idan mun sani cewa muna da laifi a rayuwarmu wanda ba mu nemi gafara ba, kuma mun sani cewa mu masu laifi ne a gaban Allah mai tsarki, za mu iya jawo bakin ciki a rayuwarmu. Dauda ya yi magana daidai domin kowa a yayin da ya ce, “Gama kurakuraina sun sha kaina: Kamar kaya mai – nauyi sun fi karfina (Zabura 38:4).” Rashin fadin laifi tana kawo nauyi, bakin ciki da kuma cuta ta jiki.

Me ke sa mu dade kafin mu yi tuba? Ko muna rudin kanmu da cewa neman dadi ta jiki tana iya ba mu jin dadi ta har abada? Ko ba mu sani cewa ba a taba kosar da jiki ba, amma jiki tana da kwadayi wanda gaba gaba ta ke yi idan mun ci gaba da ba ta abin nema? Ko kuma girman kai ne take hana mu yarda cewa muna da kasawa a gaban Allah da kuma mutane?

Ka yi alkawali da kanka cewa babu wata abu wanda za ta sa ka saba wa Allah a cikin lamirinka. Ka mika kanka ga furta kowane irin zunubi ko kasawa a kowane rana a gaban Allah idan Ruhu Mai Tsarki ya nuna maka. Ka tuba da dukan ranka ka kuma karbi wankewa ta jinin Yesu. Ka koma cikin farin ciki ta cetonka.

Idan bayan ka fadi dukan laifinka amma kana jin bakin ciki da kuma alhaki, ka sake yin bincike ta babin da ta yi magana a kan mai kara da mai lallasa din nan (Wato babi na uku a wannan littafi ke nan). Ka tabbata ba dai kana jin maganaci magabu wanda ya ke so ya gurguntar da kai da bacin rai ba. Ka nemi shawara daga dattibai masu harka ta ruhaniya a kusa da kai domin a taimaka maka ka san banbancin. Bayan haka sai ka yi rayuwarka a cikin farin ciki na mai tsabtaciyar zuciya.
ADDINI

Yanzu dai mun zo kan wannan dalili mai kawo bakin ciki, wanda na sha kokuwa da ita na shekaru masu yawa. A tawa harkan ibada, kafin in sami sanin zumunci da Allah sosai, ina rayuwata bisa ga jerin dokoki na Kirista masu tsanani, ina bada gaskiya cewa dole in kula da yin su domin ni Kirista ne.Na nace da yin nazari ta littafi, kuma ina rubuta duk umurni da ka’ ida din da na samu daga cikin ta. Kowane rana ina ajiye wannan jerin dokoki a gabana, ina kuma yin matukar kokarina domin in bi ka’ idondinta sosai. Na gurgunta yawancin sashin rayuwata domin cikata wannan, domin haka na soma ganin mutuwar basirata da kuma mutuncina. Misalin wannan ita ne, na soma daukan rayuwa ta Kirista kamar wata nauyi ce mai tsanani domin haka ba ni da lokaci domin wasa ko kuma nishadi. Ji na jiki ta zama abu ta rai kurum, kuma ba ta shafi yanayi ta ruhaniya ba (a ganina ke nan), domin haka na hana ba su dama na kuma kashe su gaba ki daya. Kowarce rana ta zama kokuwa ne domin neman yarda daga wurina da kuma daga wunin Allah. Kuma kowane rana ta zama dalili ta fidda rai domin kasawata in lika wadannan dokoki. Bakin cika ta zama mani magabcina a kullum.

Halin bi nawa ta zama yanayi ta addini kurum. Kamar Kirista na Galantiya, na karbi Kristi ta wurin bangaskiya amma ina so in yi rayuwa ta wurin karfina. Addini da rayuwa ta Kirista ba abu daya ba ne ko kadan. Addini ita ne bin ka’idodi wanda mutane suka kafa; Amma Kiristanci kuwa zumunci ne. Addini na hana cin gaba a farnen hikima da kirkiro sabobin abubuwa; amma Kiristanci na kara bunkas’a basira mai kirkiro dabaru daga zuiyar ma halicci ta hannunmu Addini na kawo nauyi ga ruhohinmu domin irin kasawarmu ta iya cika umurninta; amma Kiristanci na kawo saki ga zukatanmu bayan mun karbi karfi domin mu aikata nufin Allah. Addini aikin tukuru ne; ammaKiristanci hutu da wasa ne, domin mun daina aiki da kanmu (Romawa 4). Addini na nuna kanta ta wurin gwaninta, wato yiniya kar kokarina donuin in yi abin da ka’idodinta ta fada; Kristanci kuwa na nuna kanta a wurin iyawa mara aibi, ta wurin barin aikin Allah mafi kyau ta zuba daga rayuwata. Addini na haifar da bakin ciki, Kiristanci kuwa na fitar da farin ciki.

Ta yaya ne zan sami yanci daga wannan dauri ta addini? Bayan na koyi jin muryar Allah, na iske cewa ashe Allah ba kamar yadda na ke ganinsa a zuciyata ba. Na ji muryar kalmomi na kauna da gafartawa da kuma yarda. Na ga mai son daukan lokaci domin ya nuna mani abokantaka, mai son wasa da yara har ma mai daukan lokaci domin nishadi. Abu mafi muhimmanci a nan ita ne, na iske cawa akwai wani a cikina wanda yana iya cikata dokokin Allah a rayuwarsa na jiki, shi kuma yana sa ya aikata nufin Allah ta wurina! NA kuma isko cewa zan iya jawo karfi daga alherin Allah wanda ke cikina domin in ci nasara bisa ga jaraban da ke neman ta sha kaina.

Idan danniya ta dokokin addini ta shake ka, za ka iya samun yanci. Ka hada kai da wannan Mai Tsarki wanda ke cikinka. Ka kasa kunne ga maganarsa na gaskiya. Ka kuma dubi wahayinsa na daukaka. Ka dubi sama ka kuma yi farin ciki!

1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət