Ana səhifə

Karban shawara daga wurin allah "Masu-albarka ne masu-tsabtan zuciya gama su za su ga Allah." Daga


Yüklə 361.5 Kb.
səhifə5/11
tarix25.06.2016
ölçüsü361.5 Kb.
1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11

Mai Gargadi/Malami


“Amma wanda ya ke annabci, yana yi ma mutane zanche na … galgadi (Korinthiyawa 14:3)” “… Mai-taimakon (ta’aziya)… za ya shaida ni/(Yohanna 15:26).”

“Galgadi” daya ce daga cikin kalmomin nan da ma’anarsa ta banbanta a garemu daga fadda marubuta sun nufa a lokacin da suka rubutata. Wasu mutane na ganin kanar locacin gargadi ita ne lokaci na “rama wa wasu magane” kamar yadda mai sara ya ke yi da mu, maimakon irin aiki na Ruhu mai ta’azuifa.

Asalin ma’anar gargadi (a harshen Greek “Parakaleo” kenan) ita ce “ a kira mutum zuwa gefe domin a karfafa shi game da yanayin halinsa, domin uri gaba a nan gaba.” Ka lura da yadda ma’anar ta yi kusa da “Parakletos” wanda ana juya ta “Ta’aziya” ko “Mai-shawara” ko kuma “Mai-lallasa.”

Gargadi tana da farne guda uku:



  1. Mu kira mutum a gefe. Wato ba kullum ba ne a yi wa mutum gyara a fili. Za mu hakura me jira domin me yi magana da shi a hungu, idan tana yiwuwa. 2) muna karfafawa ne a game da wata hali tamutumin. Ba aikin mu ne mu riga maimaita kuskurinsa ba. Yawanan me mun san irin zunubanmu da kasawarmu sarai. Ba mu bukatar wani ya zo yana nanata mana se ba. Abin bukata a garemu ita ne taimako domin mu sami kubuta daga daurin da ta sha kanmu, da kuma shawarwari wanda za su taimaka mana domin aikata rayuwa ta gurbin Allah wadda dukanmu muna bidan mu yi. 3) Gargadi a kullum tana hangan nesa ne. Ka da mu yi ta tattauna al’amura ta da.

Wata muhimiyar misali a kan gergadi ita ne irin amsar da Yesu ya ba wa matan nan wadda aka kama kwarto (Yohanna 8:3-11). A bise ga shirin Shari’a ta yi laifi, ya kamata kuma a kashe ta. Amma Yesu ya leka gaba da Shari’a, ya kuma nuna mata tansayi da alheri da kuma muna mata tausayi da alheri da kuma gafara. Ya yi magana daya kurum, cewa; Ni ma ban kashe ki ba; ki tafi, daga nan gaba kada ki kara yin zunubi.” Bai bada lecca, da tsautawa ko wa’azi ba, yadda ni zan yi kamar in yi ba. Amma, a maimakon haka, ya mika mata gafara, da yarda da kuma karfofawa domin ta sami warkasuwa. A kan haka kuma babu bukata na nuna zunubanta. Yana nan a gabanta a kullum. A kamar haka ne, sumba ta kauna, tareda kalmomi na gardadi, za su iya kawo mana warkasuwa da wahalar rayuwarmu. Idan kuwa muna so, za mu uja barin Ruhun Allah ya more mu domin ya kawo wa wasu irin wannan warkasuwa.

Idan mun gaskata cewa, Ubangiji yana so mu gargadi jinna, dole mu tuna cewa kowane gargadi ya kamata, a yi ta a cikin kauna (Korinthiyawa I, 13), a cikin saukin rai (Galantiyawa 6:1), cikin tausayi mai zurfi (Korinthiyawa II, 1:36) da kuma da nufin kawo ta’aziya (Korinthiyawa 1:3c). “Kado kowane rubaben zanche shi fita daga chikin bakinku, sai irin abin da ke mai-kyau garin ginawa yayinda a ke bukata, domin shi bada alheri ga wadanda su ke ji kada kwa ku bata zuchiyar Ruhu Mai-Tsarki na Allah (Afisawa 4:29, 30a).”


Takaitawa


A takaile, bari mu duba zabura ta Asaph, wato zabura 73. Ba za mu iya rubuta dukan wannan shafi ba domin tana da tsawo sosai, amma ina karfafaka ka karanata dukan zaburan (73). Ka da ka saya a wadannan ayoyin da zan yanka kurum ba.

Asaph ya fara da cewa “Hakika Allah mai-alheri ne ga Israila, Ga irin wadanda su ke da tsabtar zuchiya. Amma ni dai Kafafuna sun Kusa su zame; saura kadan takawata ta yi talabiya. Gama na ji kishin zuchiga masu-girman kai, sa’anda na ga arzinkin masu-mugunta….” Asaph ya fara da zuciya mai tsabta amma nan da nan sai ya kau da ido doga gurbi na Allah, zuwa ga irin rayuwa sai zuciyarsa ta lalace. Maimakon ganin Allah sai ya soma ganin mutum. A maimakon da karya ta magabci. Idan ka karanta aya ta 4 zuwa ta 15, za ka ga a sarari cewa uban karyan nan ya cabke zuciyarsa da aikinsa ta karya. Akwai wasu gaskiya wadda aka bada; “… girman kai yana rataye a wuyansu kamar murjani; suna yafe da zalumchi kamar tufa… sumunsu ya fi abin da zuchiya ta ke guri… suna ba’a ….” Dukan wannan gaskiya ne. Amma a garwaye da wannan ita ce wasu karya wanda shi Asaph ya karba komar gaskiya ne: “Gama a chikin mutuwassu babu mirkaki (zafi)… Ba su chikin wahala kamar sauran mutane; Ba a yi masu masibu kamar sauran mutane ba….” Wannan ba gaskiya bane! Daga waje, a idanun masu kishi, ana ganin kamar masu murgunta suna jin dadi sosai, amma alhali kuwa ba haka ba ne. Wannan tunani ta Asaph ta kauce daga fuskar Ruhu Mai Tsarki, kuma idan mun bi irin wannan hale, nan danan tunaninmu za ta sa mu fadi cikin rami a kasa.

Amma kuma Asaph ya yi hikima domin bai ci gaba da zama a irin wannan hali ba. Ya san wurin da zai je domin neman gaskiya. Ya gane cewa kafin ya sake samun tsabtacciya zuciya, dole ne ya sake koma da fuskarsa zuwa ga gurbi ta Allah. A karshe, mun ya a cikin aya ta 17, cewa ya soma koma wurin mai-tsarki na Allah….” A sauran ayoyin da suka biyo wannan, soi muka ga rahotonensa, wato amsar da Allah ya ba shi game da tambayoyin da ya yi. Na farko, Allah ya muna masa asehin gaskiya game da mugaye. “Duba yadda suka zama a risbe Parat daya: Sun kare sarai da razaizani!” A farat daya Allah ya nuna hoton wadannan mutane, Allah ya kuma haska hasken gaskiyarsa a cikin duhun karya na shaitan, domin hake nufin shaitan ta fadi a nan da nan.

A biye da wannan, sai Asaph ya fadi wasu kalmoni na gaskiya a kanshi. “Gama zuchiyata ta damu,… Ma soku a chikina… Halin dabba na yi, mara-sani.. Har na zama kamar naman jeji a gabeks.. “Duk lokacin da na soma tunani a waje da fuskar Allah, in dai na karbi karya kamar gaskiya ce, na kan sa ke kamanni in zama kamar dabba ta jeji. Duk da haka kullum in a tare da kai; ka rike ni a hannuna na dama. Za ka bishe ni da shawararka, Bayan wannan kuma za ka karbe ni zuwa daraya.” Ka da dhike a yaudari Asaph, har yayi Zunubi, ya kuma kauce daga hanyar Allah, amma ba a yashe shi ba. Bayan ya ga zumubinsa, sai a bisanta ya ga tausayi da alherin Allah. Ba mamaki mana wannan sura ta kare da sujada! Idan mun ga Allah kuma aka nuna mana gaskiyarsa a cikinma, zukatanmu na samun tsabtcewa, ma’amalarmu na samun gyaruwa, kuma farinciki ta Allah na barkowa karnar rana ta safiya.

Ta irin wannan gurbi ne dukan mu ya kamata mu bi. Idan idanunnu sun kauce daga gurbin Allah, kuma ba mu ganin hannun Allah, kuma hankalinmu ta kidima da haduwa gaskiya da algus, dole mu ma mushiga cikin hacikahin Allah mar Tsarki. Dole mu ma mu zo gabansa, mu kuma furta shakkanmu, da fushimmu da tsoratanmu, mu kuma ba shi dama ya yi mana amsa. Ta wurin muryarsa da wahayi nasa ne kadai za mu iya samun warkasuwa.

Amsa


A wannan babin da ka karanta, shin, ko ka soma ganin irin aikin da shaitan ya ka yi a zuciyarka? Ka so garin banbanci tsakarin muryar magabci mai-sorai? Ko yanzu ka gane irin tunani ta rashin cin gaba na karya filla filla wanda magabci ke baka har kana tunani kullum akai? Ko ka soma ganin yanayin al’anuranka?

Ka dauki mataki yanzu, ko shiga haikalin Allah. Ka kwantar da zuciyarka, sa saurarar domin ka ji wannan murya ta sa’a as’a da wahayi na Yesu ka rubuta dukan tambayoyinka, da shakkarka, da fargabanka a cikin addu’a ga Allah. Ka tabbata ka sanrara domin ka ji amsarsa, ka kuma zura ido domin ka ga wahayinsa. Ka rubuta duk abin da ka gani da kuma ji. Ka yi farincili a cikin irin aikin nagarta na Allah!



1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət