Ana səhifə

Illolin Zina, Luwaxi Da Maxigo Ma’anar Zina Da Hukuncinta


Yüklə 83.5 Kb.
tarix26.06.2016
ölçüsü83.5 Kb.


Illolin Zina, Luwaxi Da Maxigo

Ma’anar Zina Da Hukuncinta : Lafazin Zina a shari'ance yana nufin saduwa da mace ba tare da an yi aure, ko an mallaketa a matsayin baiwa ba. Sai dai a kan yi amfani da lafazin zina akan abin da ba kai saduwa ba, kamar yadda ya zo a hadisin Abu Huraira – Allah ya yarda da shi – ya ce, Manzon Allah (S.A.W) ya ce : "An rubuta wa xan Adam rabonsa na zina, babu makawa sai ya same shi, zinar idanu ita ce gani, zinar kunnuwa ita ce ji, zinar harshe ita ce magana, zinar hannu ita ce damqa, zinar qafa ita ce taku, zuciya kuwa tana kwaxayi tana fata, farji kuma shi yake gasgata haka ko ya qaryata" Muslim.

A cikin wannan hadisi zamu ga yadda Manzon Allah (S.A.W) ya nuna cewa kowane xan Adam an rubuta masa rabonsa na zina, kuma zai sami wannan rabo babu makawa, sai dai ba za a kama shi da laifi ba har sai idan ya gasgata abin da idonsa ko kunnensa ko hannunsa ko qafarsa suka jiyar da shi, ta hanyar yin amfani da farjinsa don biyan buqatar waxannan gavvai, wannan shi ne ma'anar faxin Manzon Allah (S.A.W) a qarshen hadisin, "farji shi yake gasgata haka ko ya qarya ta" (Duba Sharhi Sahih Muslim Na Imam Nawawi J 16 sh 216).Hukuncin Zina : Zina haramun ce a addinin musulunci, Allah maxaukakin Sarki ya haramta ta in da yake cewa : "Kada ku kusanci zina, domin ita alfasha ce kuma tafarki ne mummuna" (Isra'i : 32).

Malamai suna cewa faxin Allah "kada ku kusanci zina", kai matuqa ne wajen hana ta, don ya fi a ce "kada ku yi zina".

Sheikh Abdur-Rahman Assa'idiy yana cewa : "Hani ga a kusanci zina ya fi kai matuqa akan hana yin ta, saboda cewa kada a kusance ta ya haxa hana dukkan yin abubuwan da suke gabatarta kuma suke kawo yin ta, domin kuwa duk wanda ya yi kiwo a gefen shinge to ko yana daf da faxawa cikinsa, musamman ma akan irin wannan lamari, wanda da yawa daga cikin zukata suna xauke da abin da yake sa wa a afka masa. Sannan Allah ya siffata zina da cewa alfasha ce, ma'ana zina wata aba ce da shari'a da hankali suke ganin muninta, saboda keta alfarmar Ubangiji ce, da shiga haqqin macen, da haqqin danginta, da mijinta, kuma vatawa miji shimfixarsa ne, da cakuxa dangantaka da makamancin haka". (Tafsirin Assa'idiy).

A wani wurin a cikin Alqur'ani mai tsarki Allah maxaukakin sarki ya siffata bayinsa muminai da cewa su ne waxanda ba sa zina, in da ya ce, "Waxanda ba sa kira, ko bautawa wani tare da Allah, ba sa kashe ran da Allah ya haramta sai da haqqi, kuma ba sa zina, duk wanda ya aikata haka sai gamu da azaba" (Alfurqan : 78).

Ya tabbata a cikin hadisi an tambayi Annabi (S.A.W) akan wanne zunubi ne ya fi girma, sai Manzon Allah (S.A.W) ya ce, "Shirka da Allah alhali shi ne ya halicce ka" sai aka ce sai wanne? Sai ya ce, "Sannan kashe xanka don kada ya ci tare da kai" sai aka ce "sannan sai wanne? Sai ya ce, "Ka yi zina da matar maqocinka" (Bukhari).

Allah maxaukakin sarki ya sanya hukuncin wanda duk ya yi zina kuma ya tava aure da jefe shi, namiji ko mace, idan kuwa bai tava aure ba, sai a yi masa bulala xari sannan a baquntar shi a wani gari daban tsawon shekara guda.

Duk wanda ya kalli hukuncin zina zai ga Allah ya kevance shi da wasu abubuwa masu yawa, saboda munin zina, ka kaxan daga cikin abubuwan da hukuncin ya qunsa:


 • Kausasawa wajen uqubar mazinaci, ta hanyar jefewa. Ko kuma bulala da baquntarwa shekara guda.

 • Hana jin tausayin mazinaci ko mazinaciya yayin da ake musu uquba. Allah ya ce :

"Mazinaciya da mazinaci ku yi kowane xaya daga cikinsu bulala xari, kada ku ji tausayinsu a cikin addinin Allah in dai kun yi imani da Allah da ranar qarshe" . (Annur : 2).

 • Yi musu uquba a gaban mutane, ba a yarda a yi musu a voye ba, Allah ya ce :

"Wasu vangare na muminai su halarci wajen yi musu uquba (haddi)" (Annur :2).

Duk waxannan abubuwa suna nuna mana munin zina da rashin kyanta a musulunci. Imamul Bukhari ya kawo a cikin ingantaccen littafinsa daga Maimun Al-audiy ya ce, "A lokacin jahiliyya na tava ganin wani biri da ya yi zina da wata biranya, sai sauran birran suka taro suka jefe su".Mafi munin zina ita ce wadda mutum zai yi da mahaifiyarsa, sai da muharramarsa, sai wadda zai yi da matar maqocinsa. Allah ya kare mu.

Illolin Zina : Babu ko shakka duk mai hankali ya san cewa zina tana tattare da illoli masu yawa, waxanda suke shafar mazinacin ko mazinaciyar, ko su shafi al'umma gaba xaya, ga wasu daga cikin illolinta :

 1. zubar da mutunci da jawo wa kai qasqanci : domin duk matar da ta yi zina to ta jawo wa kanta da danginta da mijinta qasqanci, ta kuma zubar musu da mutunci a idon duniya. Idan har ta sami ciki ta haihu, sannan ta kashe xan, to ta haxa laifi biyu, laifin zina da laifin kisan kai, in kuma ta bar shi to kuma ta shigar wa mijinta ko danginta wanda ba ya cikinsu. Idan kuwa mai zinar namiji ne to ya lalata mace, ya jawo mata lalacewa da tavewa, wanda hakan lalata duniya ne gaba xaya.

 2. Zina ta haxa dukkan sharri gaba xaya : saboda a cikin zina akwai, rashin tsoron Allah, rashin kunya, rashin tsantseni, rashin cika alqawari, qarya da butulci da sauransu. Duk kuwa waxannan munanan halaye a musulunci.

 3. Zina tana haifar da cututtuka, da mutuwar zuciya, da sanya zuciya ta zama baqiqqirin, da samun kai cikin damuwa da rashin kwanciyar hankali da nutsuwa a ko yaushe. Bincike ya tabbatar da cewa cutar qanjamau ta fi yaxuwa ta hanyar zina fiye da kowace hanya da ake iya xaukar cutar daga gareta, sannan ta hanyar cutar a kan kamu da muggan cututtuka masu mungun haxari.

 4. Zina tana haifar da talauci da musiba a bayan qasa, saboda da duk namijin da yake mazinaci to ba ya iya tattali, kullum kuxinsa suna wajen matan banza, duk abin da zai samu ba zai amfanu da shi ba yadda ya dace, a banza zai tafi. Hakanan duk matar da take mazinaciya ce, duk abin da ta samu yana qare wa ne wajen yadda zata janyo hankalin maza zuwa gare ta, Allah kuma zai zare wa dukiyarta albarka.

 5. Zina tana kawo qiyayya da gaba tsakanin masu yin ta da sauran mutane, Allah maxaukakin sarki yana cire kwarjininsu da girma daga idon mutane, saboda haka ne zaka ga qaramin yaro yana faxa da sa'an kakansa a wurin neman mata, saboda ba ya qaunarsa ballantana ya girmama shi.

 6. Zina tana jawo rashin amincewa da mai yin ta, kowa yana mai kallon maha'inci, mayaudari.

 7. Zina tana haifar da wari daga jikin mai yinta, ba wanda yake jin wannan wari sai mutanen qwarai

 8. Zina tana jawo azaba mai tsanani ga mai yin ta – idan bai tuba ba – a duniya da lahira. A duniya jefewa ko bulala da baquntarwa, a lahira kuwa makomarsa wuta. Allah ya kare mu.

 9. Zina tana kawo rugujewar gida da xaixacewar iyali, sannan tana kawo lalacewar tarbiyya.

 10. A cikin zina akwai toazartar da dangantaka, da sanya cin dukiyar mutane ba da haqqi ba, domin kuwa duk xan da aka samu ta hanyar zina abin da zai gada ba haqqinsa ba ne.

 11. Cikin zina akwai kamancecceniya da dabbobi, saboda mazinaci ba ya xaukan nauyin abin da zai biyo bayan lalatarsa, kamar yadda dabba ba ruwanta da abin da yake biyo bayan saduwarta da 'ya uwarta, na kula da mai cikin, da tufartar da ita, da renon abin da aka haifa, da yi masa tarbiyya. Ka ga kenan mazinata rayuwar dabbobi suke. Allah ya kiyaye mu.

 12. Zina tana kawo kisan kai a cikin al'umma, sau da dama faxa ya kan faru ga masu neman mata a wajen yawon banzansu, wani ya kashe wani, kamar yadda yawancin yaran da ake yar wa, ko a kashe 'ya 'yan zina ne, hakanan yawancin cikin da ake zubar wa cikin zina ne, wanda duk wannan kisan kai ne da Allah ba zai kyale wanda ya yi shi hakanan ba.

 13. Zina tana lalata al'umma, ta ruguza rayuwa gaba xaya, ta hanyar samar da 'ya 'yan da ba su da tarbiyya, ba sa ganin girman kowa, kai suna jin haushin al'umma duba da hanyar da suka zo, abin da dama ya kan sa su, su zama 'yan daba, da fashi, da sauran miyagun ayyuka, su vata rayuwarsu su vata rayuwar al'umma.

 14. Yawaitar zina alama ce ta tashin alqiyama, kamar yadda ya zo a hadisi Manzon Allah (S.A.W) ya ce, : "Ya al'ummar Muhammad (S.A.W) wallahi babu wani da ya fi Allah kishin a ce yau bawansa ya yi zina, ko kuma baiwarsa ta yi zina. Ya al'ummar Muhammad (S.A.W) da kun san abin da na sani, da kun yi dariya kaxan, kun yi kuka da yawa. Sannan sai Manzon Allah (S.A.W) ya xaga hannunsa sama ya ce, "Ya Ubangiji na isar". Bukhari ne ya rawaito.

 15. .Zina tana jawo fushin Allah da azabarsa ga al'umma. Abdullahi xan Mas'ud (R.A) yana cewa : "Zina baza ta bayyana a wata alqarya ba, face wannan alama ce ta Allah ya yi izinin halakar da ita".

Yan uwa waxannan kaxan kenan da abin da zina take haifarwa masu yin ta, da sauran al'umma. Allah Maxaukakin sarki ya kare mu.

Ma’anar Luwaxi Da Hukuncinsa

Luwaxi shi ne : Saduwa da namiji ko mace ta dubura. A kan haka luwaxi ya kasu kashi biyu, babban luwaxi wanda shi ne (Saduwa da namiji ta duburarsa) qaramin luwaxi shi ne (Saduwa da mace da dubura).

Hukuncin Luwaxi : Luwaxi da dukkan nau’o’insa guda biyu Haramun ne a musulunci, saboda baya cikin hanyoyin da Allah ya halatta wa bayinsa su biya buqatarsu daga gare su.

Allah Maxaukakin Sarki ya faxi irin azaba da bala’in da ya saukar a kan waxanda suke luwaxi a surori goma a cikin Alqur’ani, Suratul A’araf , daga aya ta 80. suratu Hud (aya 76 - ) Suratul Hijir, aya ta 58 - ) Al’anbiya, aya ta 73- . Alfurqan (28) Asshu’ara (160) Annamli (54). Al-ankabut (28) Assafat (133) Alqamar (33).

A cikin waxannan ayoyi zamu ga yadda Ubangiji ya haxa wa mutanen Annabi lux (A.S) azaba da bala’i iri iri, ya makantar da su, ya kisfe gidajensu, ya jefe su da duwatsu, ya jefa su cikin wuta.

Hakanan ya tabbata a cikin hadisin da Imam Abu Dawud, Titmizi, Ibnu Majah suka rawaito, Manzon Allah (S.A.W) ya ce, “Duk wanda kuka samu yana aikin mutane annabi Lux, ku kashe shi ku kashe wanda ake yi da shi”.

Sahabbai sun haxu akan hukuncin wanda duk ya yi luwaxi shi ne kisa, sai dai sun yi savanin yadda za a kashe shi,


 • Magana da farko : za a qone shi da wuta, wannan shi ne fahimtar Sayyidina Abubakar, Aliyu, Ibnu Zubair da sauransu. (Duba : Zadul Ma’ad, Adda’u waddawa’u. Sunan Al-kubra na Baihaq. ds).

 • Magana da biyu : za a jefe shi da duwatsu har ya mutu, ya tava aure ko bai tava ba. Wannan ita ce fahimtar Sayyidina Umar da Abdullahi xan Abbas da sauransu. (Duba : Raudatul Muhibeen na Ibnul qayyim).

 • Magana da uku : Za a samu ginin da ya fi kowane tsawo a jeho shi daga can, sannan a biyo shi da duwatsu. An rawaito wannan magana da Abubakar da Abdullahi xan Abbas. Sai ya zama suna da fahimta biyu kenan a mas’alar.

 • Magana ta huxu : Za a jeho masa katanga. An rawaito wannan magana daga Aliyu bin Abi Xalib.

 • Magana ta biyar : za a yi masa hukuncin mazinaci, idan yana da aure, ko ya tava yi sai a jefe shi, idan in kuma saurayi ne a yi masa bulala. Wannan shi ne fahimtar ibnu Zubair.

Waxannan sune maganganun sahabbai da Almajiransu akan hukuncin da za a yi wa mai luwaxi. Babu ko shakka idan muka dubi waxannan maganganu zamu gane cewa yin luwaxi ba qaramin laifi ba ne a addinin musulunci.

Illolin Luwaxi a cikin Al’umma

Ko tantama babu cewa luwaxi ya qunshi ximbin illoli da cutuwa ga mai yin sa da kuma al’ummar da yake rayuwa a cikinsu, ka kaxan daga cikinsu : 1. Luwaxi ya jawo wa mai yin shi da al’umma gaba xaya fushin Allah da azabarsa. Kamar yadda ya faru ga mutanen Annabi Lux (A.S).

 2. ‘Yan luwaxi mavarnata ne, azzalumai, mutanen banza, fasiqai, haka Allah ya siffata su a wasu ayoyi a cikin Alqur’ani mai girma.

 3. Cikin luwaxi akwai almubazzaranci, saboda mai luwaxi yana kashe dukiyarsa cikin abin Allah ya haramta, duk kuwa mai sanya dukiyarsa cikin haramun almubazzari ne, almubazzari kuwa xan uwan Shaixan ne kamar yadda Allah ya faxa.

 4. Cikin luwaxi akwa fita daga tsarin da Allah ya halicci mutum a kai, saboda Allah bai halicci namiji don ya sadu da xa namiji ba. Ya halicci maza da mata ne don su ji daxi da nutsuwa da juna, kamar yadda ya faxa.

 5. Mai yin luwaxi qazami ne, qazanta mai muni, domin ya sanya tsokarsa a cikin dubura wurin kashi da najasa.

 6. Luwaxi yana haifar da munanan cututtuka, irinsu rashin riqe bayan gida, kuraje, sanya zuciya ta yi baqi wuluk, vacewar basira da kyakkyawan tunani, rashin kunya, da sauransu.

 7. Luwaxi yana kawo qasqanci da wulaqanci da tozarta a duniya da lahira.

 8. Saduwa da mace ta dubura mummunan abu ne, wanda Ibnul Qayyim – Allah ya yi masa rahama – yake cewa “Ba a tava halatta saduwa da mace da dubura a harshen wani Annabi da Allah ya aiko ba”.

 9. Mai luwaxi bai kai darajar dabbobi ba, saboda dabba ma bata haka.

 10. Mai luwaxi – in bai tuba ba – ba ya rabuwa da duniya lafiya, ko dai Allah ya tozarta shi, kowa ya san aikinsa, ya wayi gari ba shi da mutunci a idon duniya gaba xaya, ko kuma Allah ya jefa masa wata mummunan cuta da za riqa fatan ya mutu kowa ya huta, saboda muninta. Allah ya kiyashe mu.

Maxigo Da Hukuncinsa

Maxigo shi ne Mace ta biya buqatarta da mace, ta hanyar rungumar juna da haxa gaba.

Maxigo haramun ne a addinin musulunci, malamai sun sanya shi daga cikin manya – manyan zunubai, sai dai shari’a ba ta ayyana wani hukunci zaunanne da za a yi wa masu maxigo ba, Alqali ne zai duba me ya dace ya yi musu na hukunci, bulala, xauri, kora, tozartawa, ko kuma a haxa musu duka, duk dai hukuncin da alqali ya yanke na razanarwa da tsoratarwa ya yi. (Duba Al-mausu’atul Fiqihiyyatul Kuwaitiyya. Da Almugni na Ibnu Qudama).

Illolin Maxigo

Maxigo kamar sauran abubuwan da suka gabata ne wajen haifar da cututtuka da bala’i da musiba ga mai yinsa. Ga kaxan daga cikinsu : 1. Maxigo fita ne daga xabi’ar da Allah ya halicci mace a kanta, ta jin daxi da xa namiji ba mace ‘yar uwarta ba.

 2. Cikin Maxigo akwai rashin kunya, da fitsara, alhali Manzon Allah (S.A.W) yana cewa : “Kunya alheri ce gaba xayanta” a wata riwaya : “Kunya ba ta kawo komai sai alheri”. Bukhari ne ya rawaito.

 3. Maxigo ya kan haifar da cutakan zamani, a wani bincike da aka gabatar ya tabbatar da za iya xaukan cutar qanjamau ta hanyar maxigo, idan aka yi da wadda take xauke da ita, kamar yadda za a iya samun ciki ta hanyar maxigo, idan mace ta yi wanda ba ta daxe da saduwa da xa namiji ba. Hakanan likitoci sun tabbatar da maxigo yana iya jawo rashin haihuwa.

 4. Ana iya rasa budurci ta hanyar maxigo, wanda hakan ba qaramin tozarta ba ne ga budurwa ta rasa budurcinta kafin ta yi aure.

 5. Mai maxigo ta kan rayu cikin quncin zuciya da qunarta, saboda Allah zai xebe mata nutsuwa a tare da ita, ya maye gurbinta da qunci da damuwa. Wata budurwa ‘yar shekara ashirin tana bada labarin irin yadda ta sami kanta cikin damuwa da bala’i bayan rabuwarta da abokiyar maxigonta, tana cewa : “Na kasance budurwa ‘yar shekara ashirin, ina son wata qawata sosai tsawon wasu shekaru masu yawa, har dai muka fara maxigo a tsakaninmu, ta shiga raina matuqa, na zama duk abin da take so shi nake yi, har ma ya zamana wani lokaci ana samun savani tsakanina da ita idan na ga wani ko wata suna qaunarta, saboda yadda nake kishinta. Wata rana sai wannan qawar tawa ta yi aure, abubuwa suka canza, tace dole ne mu rabu, haka muka rabu, ni kuma na shiga wani hali na jin zafi da raxaxi a jikina da zuciyata!!. Ciwon kai, ciwon idanu, ciwon jiki, na je wajen likitoci amma ban samu wata waraka ba, wayyo! Ni yanzu yaya zan yi, ga shi na tuba, amma fa ina so in koma wajenta, yaya zan yi!?. Wannan kaxan kenan daga illar maxigo.

 6. Maxigo ya kan hana ‘ya mace zaman aure, domin duk wadda ta saba da shi, to zai yi wahala kafin ta rabu da shi, wanda wannan zai sa ta kasa wadatuwa da mijinta, sai ta riqa fita tana yi, har idan Allah ya tonu asirinta, mijinta ya saketa, saki na wulaqanci, ko kuma ta nemi saki da kanta ta je ta ci gaba da maxigonta, don haka : “Maganin yaya za a yi kar a fara”.

 7. Mai maxigo bata qarewa da duniya lafiya, ko dai tozarta a duniya, ko kuma haxuwa da mummunar cuta da bala’in da ba a warkewa, sai dai qabari!.

 8. Maxigo dabanci ne, kai! Dabba ma ta fi ‘yar maxigo.

 9. Cikin maxigo akwai cin amanar Allah Mahalicci, saboda an aikata abin da ya hana, haka kuma akwai cin amanar iyaye ko miji.

 10. Haxuwa da azabar Allah A lahira, idan ba a tuba ba.

Wannan kaxan kenan daga cikin illolin da maxigo yake haifar wa masu yin sa. Allah Maxaukakin Sarki ya kare mu.

Hanyoyin Kare Kai Daga Zina, Luwaxi Da Maxigo

Saboda hikimar Ubangiji da rahamarsa duk abin da ya haramta wa bayi, to za ta buxe musu wata qofar da mutum zai biya buqatarsa ba tare da ya afka wa wancan abin da Allah ya hana xin ba. Wannan abu haka yake a nan ma, domin dai mun ji irin tarin illolin da suke tattare da yin zina, luwaxi, maxigo, to amma babu yadda namiji ko mace za su rayu ba tare da sun sami inda za su zubar da sha'awarsu idan ta taso ba, saboda haka sai musulunci ya hallatta waxannan abubuwa masu zuwa don kaucewa afka wa cikin zina : 1. Aure : Allah Maxaukakin Sarki ya halatta wa maza su auri mata, inda yake cewa :

"To ku auri abin da kuke so na mata, bibiyu, uku-uku, hurhuxu, idan kuwa kuna tsoron ba za ku iya adalci ba to ku auri xaya, ko kuma abin da damarku ta mallaka, wannan shi ne abin da zai sa ba za ku karkace ba" (Annisa'i : 3).

Manzon Allah (S.A.W) kuma yana cewa "Yaku taron samari, duk wanda ya sami iko (ma'ana zai iya riqe matar) to ya yi aure, domin shi ne mafi abin da yake sa runtse ido, kuma mafi sa wa a tsare farji, duk kuwa wanda bai samu iko ba, to ya yi azumi domin kariya ne a gare shi". Al-Bukhari Da Muslim.

Wannan aya da hadisi suna nuna mana halaccin mutum ya yi aure, kuma ya auri matar da yake so, wadda ta kwanta masa a rai, matuqar ba ta cikin waxanda Allah ya haramta masa ya aura. saboda haka, da mazinata, ‘yan luwaxi da masu maxigo za su yi tunani da sun ga yadda musulunci ya sauwaqe musu hanya, ta hanyar su yi aure, sai ya zama duk abin da za su yi halal ne, in ma sun yi niyya Allah ya ba su lada kamar yadda hadisi ya nuna.


 1. Mallakar bayi : musulunci ya halatta wa namijin da ya mallaki baiwa ya yi saxaka da ita, don kare mutuncinsa da mutuncinta. Ko kuma ya 'yanta ta ya aure ta.

 2. Azumi : kamar yadda hadisin da ya gabata ya nuna, saboda mai azumi an umarce shi da ya kare gavvansa daga barin haramun, kada ya yi aikin banza, ko maganar banza, ko kallon banza, wanda kuwa duk zai yi azumi ya kiyaye gavvansa daga waxannan abubuwa to babu ko shakka Allah zai ba shi tabbata a kan xa'arsa, ba zai kyale shi ga shaixan ba har ya kai shi zuwa ga haramun.

 3. Nisantar Abubuwan da suke motsa sha'awa : Ya zama mutum yana nisantar duk wani abin da zai motsa masa sha'awarsa har ya kai shi zuwa ga neman mata, ko luwaxi, ko maxigo, kamar kalle – kallen finafinan batsa, karanta mujallun banza, raye – raye tsakanin maza da mata, sauraran kixe – kixe, da sauransu. Hakanan da nisantar wuraren da ake sava wa Allah, in da yake haxa maza da mata, ana shexana da ayyukan banza.

 4. Shagalta da ayyukan alheri : Duk wanda zai shagaltar da kansa da ayyukan ibada da alheri, to ba zai sami lokacin da zai je zuwa ga zina ko luwaxi ko maxigo ba. Musulmi na haqiqa bai da wani lokaci da zai tafiyar da shi wajen sava wa Allah, duk lokutansa na ibada ne da tsoron Allah.

 5. Tsoron Allah a ko yaushe : Kamar yadda Manzon Allah (S.A.W) ya ce, "Ka ji tsoron Allah a duk inda kake".

Qofa A Buxe Take

Wani ko wata za iya tunanin cewa yanzu na ji wa’azi, to yaya zan yi in tuba in daina, kuma shin ma Allah zai karvi tuban nawa bayan dukkan waxannan abubuwa da na aikata?. Sai mu ce:

Babu wani zunubi a bayan qasa da Allah ba ya gafarta shi, matuqar dai mai yin sa ya tuba tuba ingantacce, saboda Allah yana cewa, : "Ka ce, yaku bayina waxanda suka yi wa kansu varna kada ku xebe qauna ga rahamar Allah, haqiqa Allah yana gafarta zunubai gaba xaya, lallai shi Allah mai gafara ne mai jin qai". (Azzumar : 53). Sannan Manzon Allah (S.A.W) ya ce : "Allah ya sanya wata qofa a wajen mafaxar rana, faxinta tafiyar shekara saba'in ce, saboda tuba, ba kuma za a rufe wannan qofar ba, matuqar dai rana ba ta vullo daga inda qofar take ba". Tirmizi ne ya rawaito wannan hadisi.

A wannan aya da hadisi zamu ga yadda Allah Maxaukakin sarki saboda rahamarsa da falalarsa ya buxe tangamemiyar qofar karvar tuba, har zuwa lokacin tashin alqiyama, don haka babu wani zunubi da mutum zai yi a faxin duniyar nan, face in ya tuba Allah zai karvi tubansa. Abin da dai ya wajaba a kiyaye yayin tuban shi ne : • Yin nadama akan abin da ya gabata, ya zama yana tunawa kuma yana damuwa, yana nadama, yana jin yaya ma aka yi ya aikata wannan laifin!.

 • Qudurcewa a zuciya yayin tuba, cewa ba zai qara koma wa wannan laifi ba, har qarshen rayuwarsa.

 • Barin wannan savon in yana cikin yi ne yayin da zai tuba, kada ya ce bari in qarasa sannan sai in tuba.

 • Yin tuban a lokacin da Allah yake karva, shi ne kafin tashin alqiyama, kuma ba lokacin da yake gargarar mutuwa ba. Haqiqa Allah ba ya karvar tuba a waxannan lokatai guda biyu, kamar yadda Alqur'ani da hadisi suka nuna.

 • Ya zama ya sauqe nauyin wani da ya hau kansa, idan kuxi ne ya biya shi, in cin mutunci ne ya nemi ya yafe masa.

Waxannan su ne abubuwan da mai tuba zai kiyaye da su yayin tubarsa. Allah Maxaukakin Sarki ya sa mu dace.
Ina So In Tuba Sai Dai…

Da yawa daga cikin mutane suna son su tuba su bar zunubin da suke yi, sai wasu abubuwa sukan zo su sha gabansu, su kange su ga barin tuba xin, har kuma su halaka suna kan wannan savon, to amma mutum musulmi wanda ya san abin da yake ya san babu wani abin da yake kare mutum daga tuba.

Anan zamu kawo kaxan daga cikin irin waxannan abubuwan da suke kange wasu daga tuba, mu yi bayanin yadda mutum zai yi :


 • Wata ta ce, ina so in tuba in bar yin zina, sai dai abokin varnata yana tsorata ni da cewa idan na qi yarda da shi, zai fallasa ni ya tona min asiri, domin kuwa yana da recordin xin wasu daga cikin abubuwan da muka yi tare da shi, to yaya zan yi?

 • Amsa : Ki sani cewa kunyar lahira ta fi ta duniya, kuma Allah Maxaukakin sarki ki ke sava wa ba wani xan adam ba, Allah kuma ya fi iko a kanki fiye da yadda wancan abokin baxalarki yake da iko a kanki, Allah zai iya tona miki asiri ke da shi a nan duniya, kuma ya qi rufa muku asiri a lahira. Don haka ki zavi kunyar duniya akan ta lahira, ki dogara ga Allah, babu abin da zai cutar dake, nawa ne cikin mutane da suka shahara da varna da fasadi a bayan qasa, amma Allah ya rufa musu asiri ya karvi tubansu, ya zamana ko da abokan baxalarsu a baya, sun faxi wani abu a kansu, baya wani ta'asiri, domin dukkan zukatan bayi suna a hannun Allah ne yana jujjuya su yadda ya ga dama. Don haka ki dogara ga Allah ki tuba, Allah mai ji ne mai gani. Shi kuma ki bar shi da Allah zai ishar miki sharrinsa.

 • Wani kuma ya ce, na yi lalata da yawa, na shigar da mutane masu ximbin yawa cikin wannan hanya, yanzu idan na tuba yaya zan yi da waxanda na rena, anya kuwa Allah zai gafarta min?

 • Amsa : ka sani sanya zuciyarka ta yi wannan tunani na tuba alama ce daga cikin alamomin Allah yana nufinka da alheri, kuma babu abin da ya wajaba a kanka face ka gaggauta tuba da barin wannan savo, waxanda kuwa ka sanya a wannan harka ka kira wo su zuwa ga tuba, kamar yadda ka kirawo su – a baya – zuwa ga halaka, wanda duk ya amsa kana da lada, wanda kuwa ya bijere maka, to Allah yana ji, yana gani, kai dai ka tsarkake niyyarka ka tuba, ka yawaita istigfari da neman tsari daga wurin Allah, ka yawaita alheri Allah mai gafarta zunubai ne gaba xaya.

 • Wata kuwa cewa ta yi : Yo in ma na tuba komawa nake, sau nawa ina tuba ina komawa, don haka gara kurum in ci gaba, nan gaba na tuba!

 • Amsa : A'a ya ‘yar uwa wannan ba dalili ba ne na qin tuba, wala'alla a baya baki tsarkake niyyarki ba, kina tuban ne a baki, amma zuciyarki tana tattare da abin. Kuma ki sani yawan tuba matuqar da niyya mai kyau kike yi, to ko da kin koma wa laifin daga baya, wannan ba zai hana ki sake duba ba. don haka ki gaggauta ki sake tuba, ki kuma tsarkake niyyarki Allah zai taimake ka.

Waxannan kaxan kenan daga cikin irin tunanin wasu dangane da tuba. A qarshe dai abin ya wajaba mu sani shi ne Allah yana karvar tuban bayinsa gaba xaya. Mai son qarin bayani ya duba littafin (Uridu An Atuba Walakin) Na sheikh Saleh Al-munajid, zai samu qarin bayani.

A qarshe ina roqon Allah da kyawawan sunayensa da siffofinsa maxaukaka ya kare mu daga faxa wa cikin wannan bala'i, da sauran abubuwan da ya hana, waxanda kuma aka jarraba da yi, to Allah ya shirye su, ya sanya su tuba su koma kan hanya madaidaiciya.

Xan Uwanku A Musulunci

Muhammad Rabi'u Umar R/lemoGatafa75@yahoo.com

Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət