Ana səhifə

Karban shawara daga wurin allah "Masu-albarka ne masu-tsabtan zuciya gama su za su ga Allah." Daga


Yüklə 361.5 Kb.
səhifə1/11
tarix25.06.2016
ölçüsü361.5 Kb.
  1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11


KARBAN SHAWARA
DAGA WURIN ALLAH

SAMUN LAFIYA TA ZUCIYATA WURIN JIN MURYAR ALLAH

KARBAN SHAWARA DAGA


WURIN ALLAH
"Masu-albarka ne masu-tsabtan zuciya gama su za su ga Allah."

DAGA
MARK da PATTI VIRKLER

© Mark and Patti Virkler

Published in Nigeria by


Christian Literature in Nigerian Languages Project

# 29 Shendam Street, P. O. Box 13377

Tel: 073 - 451139

Jos - Plateau State, Nigeria.


JERIN LITTAFIN


Babi Na Daya - Ka Bude Idamuna, Domin In Gani.....

Babi Na Uku - Ganawa Da Allah...

Baba Na Hudu - Mai Kara da Mai Lallasa...

Babi Na Biyar - Tunani a Kan Kristi Kadai...

Babi Na Biyar - Ganin Allah a Kwanakin baya...

Babi Na Shida - Daga Forgaba Zuwa Bangarkiya...

Babi Na Bakwai- Daga Alhaki Zuwa Bege...

Babi Na Takwas- Daga Fushi Zuwa Kauna...

Babi Na Tara - Daga Raina Kai Zuwa Daraja...

Babi Na Goma - Daga Damuwa Zuwa Farinaki...

Babi Na Goma Sha Daya- Nasara ta Wurin Mutuwa da Tashiwan Mattatu...

Babi na Goma Sha Biyu - Ganin Allah a Cikin Dukan Al'amura...
MIKAWA


Zuwa ga uban Patti, Lyle Hudson, mutum mai addu'a da kuma bangaskiya, wanda Ubangiji ya kira shi zuwa sama kafin a gama rubuta waman littafi, da kuma uwar patti, claire, mace mai cike da alheri da kuma mutunce, muna mika wanna littafi a garesu a cikin kauna.

GABATARWA

"Za a ce da sunansa...

Alajibi Mai-shawara (Ishaya 9:6). Abin godiya da albarka ce idea mun sani cewa za mu iya kowa karmu gaban mai bamu shawara mai alfarma kamar haka! kowace lokacin da fargaba da shakka ta cukume mu, abin godiya me ga ubangiji domin wanna mai ba da shawara mai alfarma! Mutanen chiniya za iya yin tuna da kasawarmy ta da, ta kuma ce ita ce ta jawo wachalun da ke rayuwamu to yanzu, amma begenmu ita ce muna da wannan mai ba da shawara mai alfarma!.

Ba nufin Ubanmu na sama ne mu yi raywuanmue da kanmu ba. Ya kafa mu a cikin alherinsa a iyali ta jama'a musa kamantaka da mu ya kuma umureemu mu karfafa juna, mu kuma kamaci juna. Idan mun ba juna shawara ko kuma mun ba ra'ayinmu, abin ba muke yi ita ce shawartan juna kenan ya kamata mu yi hankali ta harshamu domin ta fadi abin da wanna babban mai bada shawara wadda ke zuciyarmu zai fada ta bakinmu!

Kowane gawani a farnen bada shawara mai tausaiyi yana kokari ne ya sa mu mu ga damuwarmu a wata sabon farne. ya na nuna mana dokokin littafi mai tsarki, wanda muka kefare, wadda ta jawo mana wannan al'amari to damuwa. Ta wurin adua yana iya kwakulo ababa wadanda suka jawo mana raunuka masu tsanani a rayukanmu ko da a ce wadannan za su iya kwakulo fushen daliben damuwonmu, babu wani dan adam wanda zai iya bamu karfin mu ci nasara bisa halayenmu ta zunubi. Baba bil adama wanda zai iya zuba mama mai ta warkasuwa a zukatanmu mara lafiya. Masu bada shawara ta gaskiya sune wadanda sun san yadda za su kawo mutane zuwa gaban Yesu kristi wanda tabawarsa yana mayar da komai ta zama sabo.

Wannan yar littafin ba ta kumsli dukan amsa ta damuwarka ba. Bata nuna hunkan lisafin samun warkasuwa ba. Bata bada wata cikakkiyar dabara ta ceton koi ba.

Abin da aka nuna anan dai ita ne cewa duk matsalolin da ke aukuwa a rayuwarmu na tasowa ne domin rashin kulawa da abin da Ubangiji ke yi a rayuwarmu. Yesu ya ce,"

"Daga wanna mun gane cewa rashin tsabta a zukatanmu na iya hana mu ganin Allah, kuma ganin Allah tana tsabtace zukatanmu ta kuma warkar da ita. Ainitun sakon wannan littafi ita ce, a zyga ka domin ka hadu da wannan mai bada shawara mai alfarma domins ka dandana tansayinsa, ka kuma same dikaken warkasuwa. Ta wurin sachiwa da Ubangiji ne rayuwarmy ke samun canji ta har a bada Wanna ita ne addiata a gareka.


Babi Na 1


KA BUDE IDANUNA, DOMIN IN GANI

Ubangiji yana mika hannunsa domin ya taba zukatan yayansa yana son ya hada ruhunsa da nasu domin ta zama daya, domin ya hura masu numfashin ta sabon rayuwa daga wurin Ruhunsa Mai Tsarki "Masu-albarka ne masu-tsabtan zuchiya," ruhunsu a warke take, suna da yanci su yi dariya da rawa a dukan rayuwarsu, suna kuma jin dadin Ubangiji da dukar aikin halittarsa. Suna da yanci su kaunaci dukan yan'uwa. Suna kuma da yanci su kaunaci kansu." Masu albarka ne Masu-tsabtan Zuchiya gama su za su ga Allah! (Matta, 5:8)."

Idan samun zuciya mai tsabta, da lafiya, da kuma mai yanci ta kumshi ganin Allah, to me ake nufi da wannan? Ina zan zura ido domin in ganshi? Ina kuma zan iya samunsa? Littafi Mai Tsarki tana kumshe da amsoshi masu ban mamaki a game da wadannan tambayoyi.
A CIKIN WAHAYI

A wata safiya, bawan annabi Elisha ya tashe shi daga barci da wata labari mai ban tsoro cewa, "Ga wata babban askarawa masu dawakai da karusai sun kewayemu a cikin dare. Askarawan kuma sun san wurin da muke, mu kuma ba za mu kubuta ba daga hannunsu. Wayyo, me za mu yi?" Ga dai irin wata wayenwar gari ta masifa! A irin wannan rana ce yawancin mu za mu rasa ko ina ne Allah yake, ko ba haka ba? Kowa zai gane idan Elisha ya kasa ganin Allah a irin wannan aukuwa.

Amma menene wannan annabi (“mai duban") ya yi? "Ya Ubangiji ina rokonka, ka bude idanunsa domin shi gani' Hakika, dukan tudun ta ciku da dawakai da karusai ta wuta a kewaye da Elisha (Sarakuna II, 6:17)" A dan karaman lokaci ra'ayin wannan bawan ta canza. A nan da nan tsoro ta zama bangaskiya, shakka ta kuma zama bege, nauyin zuciya ta zama murna. Don me? Domin ya ga Allah!

Tuna da wannan kaunatacen manzo a cikin sufansa, an daure shi aka kai shi Patmos domin a hore shi. Yesu ya yi alkawari cewa zai dawo, amma bayan shekaru masu yawa sun rigaya sun wuce ba tare da an ga wata ceto ba. Yohanna ya ba da kansa domin ya bi Ubangijinsa, amma abin da dai ya samu shi ne zama shi kadai, da kuma nisa daga abokansa da kuma kurkuku. Idan kana cikin irin wannan hali ba za ka yi tunani cewa ko me kenan ke faruwa ba? Za ka soma shakka ko Allah na mulki?

Amma me Yohanna ya yi? "Bayan wannan na duba, ga kofa a bude chikin sama, murya kwa wadda na fara ji, murya kamar ta kafo yana zanche da ni, wani yana chewa, ka hau daganan, in nuna maka alamuran da za su faru dole gaban nan, Nan da nan ina chikin Ruhu: ga kursuyi a kafe chikin sama, da wani kuma a zamne bisa kursiyin (Ruya Ta Yohanna 4:1,2)" Da Yohanna ya duba, ya ga Allah a kan kursuyinsa, yana kan mulkinsa, shi ne kuma mai rikon komai, ko a cikin kurkuku, ko kora da kuma in kana nan kai kadai.

Ba shakka akwai wasu mutane wadanda suna zauna kusa da shi amma ba su iya ganin Allah ba. Ba shakka sauran firsinoni da masu gadi suna ganin su ankwa da kofofi da kuma bango mai kauri ce kurum. Me ta sa Yohanna ya iya gani amma sauransu sun kasa? Daya daga cikin amsar ita ce kalman nan mai cewa "Na duba".

Idan muna neman mu zama mutane masu ganin Allah, abin yi guda daya ita ne dole mu duba da idanunmu ta zuciya, a cikin bangaskiya da kuma begen ganin shi da irin aikin da ya ke yi a rayuwarmu da alamuran da ke kewaye da mu.

Wani almajirin da ya kamata ya yi fushi da Allah shi ne Istifanus. Istifanus ya ba da kansa ga aikin Kristi da kuma yan’uwa masu bi. Amma me ya samu daga wannan? Mutuwa ta hannun harbi da duwatsu. Ya kamata da ya daga hannu ta fushi ga Allah domin wannan "bala'in da ta faru da shi. Da ya ma bar shakka da razana su dauki hankalinsa. Ai wannan al'amari ta nuna cewa Allah ba ya mulki, domin in yana mulki ai da wannan bata faru da shi ba.

Amma, a maimakon haka Istifanus ya jimre da tsabtacen zuciya "amma shi, chike da Ruhu Mai-tsarki, ya zuba ido zuwa sama, ya ga darajar Allah, da Yesu a tsaye ga hannun dama na Allah, ya ce, 'ku duba, ina ganin sammai a bude, da Dan mutum a tsaye ga hannun dama na Allah' (Ayukan Manzanni 7:55,56)". Ubangiji Allah yana kan kursuyinsa. Yesu yana kaunarsa yana kuma marimarin ya karbe shi zuwa cikin darajarsa na ruhaniya.

A Tsohon Alkawari, wani sunan da a ke kiran annabi da ita shi ne "mai duba", domin irin baiwan da suke dashi na hangan abubuwa cikin duniya ta ruhaniya. A cikin sabon Alkawari kuwa, Kristi ya bude mana labule ta ruhu domin mu ga a cike abinda mutane kadan kurum ke iya gani a zamanin da. Mu yan hangan ruhu na yanzu za mu iya ganin abin da idanun nama ba za su iya gani ba a duniya ta ruhu. Mu kan gani da zurfi zuwa abin da idanu to jiki ba za ta iya gani ba zuwa can cikin yanayi ta ruhaniya wadda take mallakar komai na waje.


A CIKIN HALITTARSA

Ba ta cikin duniya ta ruhu kadai mu kan ga Allah ba, za mu iya ganinsa a sarari ta wurin aikinsa na halitta "Gama tun halittar duniya al'amura nasa da ba su ganuwa, watau ikonsa madawami da allahntakassa, a sarari a ke ganinsu ta wurin abubuwa da an halitta ana gane su; har kwa su rasa hujja (Romawa 1:20)"

Darajar Allah ta na bayana a hasken rana da a cikin ruwan sama, a itatuwa da kuma gajimare, a cikin ciyawa da fure, a cikin rani da kuma hunturu. Ba kowa ne ke ganin Allah a cikin haliltarsa ba. Wani zai iya duba waje ya ga ruwa na zubowa, sai ya yi gunaguni cewa, "Ina son rana ta yi haske yau. Me ya sa ana ruwa yau? Ni na ki jinin ruwa!" Ga wani kuma rana ta na zafi sosai kuma tana kara masa azaba a cikinsa.

Amma ga wadanda ke zura ido, ga wadanda ke so su ga Allah, "al'amura nasa da ba su ganuwa, watau ikonsa madawami da allahntakassa" na iya ganuwa a cikin dukan aikin halittarsa.


A CIKIN DUKAN ABUBUWA

Ba a cikin halittar Allah kadai a ke ganinsa ba, amma a cikin dukan gusurin kowane irin abu. "... a chikinsa kwa dukan abu suna harhade (Kolossiyawa 1:16,17)," Komai a duniya ta na da rai, domin tana kumshe da iko da rai ta Allah madawami shi ne ikon da ta harhada komai a wuri daya.

A yayin da na rike wannan littafi a hannu, na kan ji ikon Allah mai rikon komai a cikinta. Ba wai abu ita ne Allah ba. Wannan irin bangaskiya tsafi ne. A tabbace Allah ya yi wannan karamar littafi kwarai da gaskiye. Shi ya halicci komai da komai. Amma dukan abu na hade a wuri daya domin ikonsa na cikinsu.

Ka tuna abin Yesu ya fada wa Farisawa a yayin da yana hawan yar jaki zuwa Urishalima kuma Farisawa na faman su hana almajiransa yin masa yabo? “In fada maku, da a che wadannan za su yi shuru, ko duwatsu su a yi murya! (Luka 19:40).” Abubuwa marasa motsi kamar duwatsu na iya zama abin yabon wannan sarki.


A Cikin Girma Ta Ruhaniya

Ba wuya mu yi tunani cewa mune mu ke sa kan mu girma a cikin ruhaniya. Amma Allah ya ce “amma daga gareshi ku ke chikin Kristi Yesu wanda aka zamadda shi hikima garemu daga wurin Allah, da adilchi kuma da tsarkakewa, da pansa (Korinthiyawa I, 1:30)”. Girma cikin ruhaniya ita ce karuwa cikin aikata nagarta a rayuwarmu ta yau da kullum da kuma ware kanmu da hanyar rayuwa ta zunubi. Duk irin wanna aikata nagarta in ba tare da Yesu ba duk banza ne. Girma ta gaskiya a cikin ruhaniya ita ce girman Kristi a cikin zuciyar mai bi. Ina girma a cikin adilci idan na bar Kristi ya sami sakuwa a cikin rayuwana. Ba nawa aiki ne in wanke kaina ba, amma irin yarda ne wanda na nuna ga iyawansa domin ya wanke ni da kansa. Domin haka idan na dubi rayuwata sai in ga Allah a cikin aikinsa.


A CIKIN AL’AMURA

Idan kome tana faruwa yadda ka ke so, sai ta zama da sauki ka ga hannun Allah a rayuwarka. Idan maigidanka ya kara maka albashi, kuma motarka na aiki daidai, yara kuma suna cikin hankalinsu, kuma uwargida ta dafa maka abinci irin mai faranta maka rai, ba wuya aji ka kana cewa, “Lalle , Ubangiji Allah, Mai kirki ne! Albarkansa ta tabbata a rayuwata!” Amma idan an kore ka daga aiki, kuma mota ta lalace, ga yara na fada a rashin hankali, ko kuma abin ta fi wannan muni, a ce yaran su bar gida a yawon dandi mara ma’ana, har kuma a ce uwargidanka ta ware kanta wai domin ta “sami sakewa” komai dai ta zama a birkice a rayuwarka? Shin za ka iya ganin Allah? Allah mai kirki ne har yanzu? Hannunsa ta albarka tana a kanka? A cikin dukan bala’i ta rayuwa, za ka iya badagaskiya cewa Kristi yana yin komai “bisa ga ikon daukakarsa (Kolossiyawa 1:11)” da kuma shi ya kan sa “dukan al’amura suna aikatawa zuwa alheri (Romawa 8:28)”?

Ana cikin yaki a kasar. An kewaye babban birnin. Watanne masu yawa sun wuce ba tare da abinci ba. Yunwa ta mamaye kowa. Mata masu yaya sun rasa hankulansu saboda wannan al’amari har sun soma cin yayansu. Akwai wata yanayi wadda za ta fi wannan muni? Allah na kiyaye da wannan kasa wadda yake nema domin ya aura? Ko kuma zai iya mayar da munin wannan yaki ta zama hanya ta kawo masu alherinsa?.

Annabi Irmiya ya ce “I, haka ne”. I, hannun Allah na nan tare da kai. Ku ba da kanku ga abokin gabanku domin ta haka Allah zai yi amfani da abin da ke faruwa domin ya wanke dukan kasarmu. Akwai wadanda za su rage, kuma ta wurinsu ne ceto za ta zo wurin dukan duniya ko da a ce har yanzu muna ganin mugunta a ko’ina, amma ina ganin Allah a bisa kursiyinsa.A CIKIN DUKAN KOMAI

“Gama chikinsa mu ke rayuwa, mu ke motsi, mu ke zamanmu... (Ayukan Manzanni 17:28)”. Masu tsabtacen zuciya suna ganin Allah a cikin dukan numfashin da suke sheka. Suna jin karfinsa a kowane naman jikinsu. Kristi shi ne tushen komai “Kristi shi ne komi, yana chikin komi kuma... (Kolossiyawa 3:11).” Shi ne “wanda ya cika dukan abu sarai... (Afisawa 1:23).”

Amma ta yaya ne za mu iya ganin Allah a dukan irin wadannan hanyoyi? Idan zuciyata ta birkice, bangaskiyata ta rushe, karfina ta guje ni, ta yaya zan gani? Ta hanyar wahayi ne kurum.

Ta alherin Allah ne kurum za mu iya ganin kamun kai a cikin hauka, kauna cikin rasana, murna cikin makoki. Dole ne mu zo gabansa ba tare da ko kadan daga cikin iyawanmu ba, mu kuma zo da addu’a cewa bari a kunna hasken zuciyarmu domin mu sani (Afisawa 1:17,18). Wannan ta zama addu’armu ta kullum, domin mu gani dabam da irin ta ganin duniya ko jikinmu, mu kuma gani da idanun zuciyarmu abubuwa na ainihi wadda ke duniya ta ruhaniya.

Dauda ya yi addu’a cewa, “Ka bude mani idanuna, domin in duba... (Zabura 119:18) “Dauda ba makaho ba ne a cikin jiki. Ya iya karatun kalmomin Littafin Allah. Amma ba shi iya gani. Shakka ko tsoro ko kuma zunubi sun rufe masa idanunsa ta ruhaniya. Iko ta ruhu ce kadai za ta iya wanke masa zuciya ta kuma bude masa idanunsa ta ruhaniya.

A yayin da almajiran nan ke tafiya a hanya zuwa garin nan mai suna Imwasu (Luka 24:13-35), rayuwa ta zama abin banza gaba ki daya. Bala’i ta faru. An giciye Yesu, mugunta ta ci nasara, duk warkasuwa ta kauna ta tsaya daga zubarta, rayuwa ta zama abu mara ma’ana, sun daina ganin Allah gaba daya.

“A ware ku ke daga Kristi rababbu daga yangaranchi na Israila, baki ga wa’adodin alkawali, marasa-bege marasa-Allah chikin duniya (Afisawa 2:12).” A yayin da suna takawa zuwa gida, suna ta tattaunawa game da wannan zance ta bala’i wadda ta fara da su. Watakila sun yi magana game da yadda zukatansu ta baci game da abin da ta faru. Ai sun yi zato cewa Almasihu ya zo domin ya cecesu daga mulkin danniya. Sun bar iyalisu da gidajensu domin su bi shi. Tunaninsu ta nasara ta koma ciki don wannan aukuwar. Babu mai ceto, duk shekarun da suka bata na bin wannan zato ta bi ruwa.

Nan da nan sai “Yesu da kansa ya kusanche su ya tafi tare da su. Amma idanunsu a kame su ke da ba za su sansanche shi ba”. Sau nawa irin wannan take faru da mu. Yesu yana nan kusa da mu domin ya kwantar mana da hankali ya kuma warkar da mu, amma idanunmu suna a makance daga bacin rai. Sai Yesu ya ce wa almajuran nan biyu, “Me ku ke magana akai?” Yesu kuwa ya dai san duk abin da su ke magana akai. Ya san komai duka. Amma don me ya yi wannan tambaya? Domin yana so ya jawo su domin su furta tushen ainihin tunaninsu. Haka a kullum Yesu na yi da mu a yayin da muna ganawa da shi. Zai yi mana tambaya, mu kuma za mu amsa masa cewa, “Amma kai ka san amsar wannan tambaya. Me ya sa ka ke tambayana?” Amma farkon warkasuwarmu tana zuwa ne idan mun furta zukatanmu a gaban Allah. Kada ka ji tsoro ko kunya in ta zo na furta dukan tambayoyinka da fushinka da shakkarka da tsoronka ba za ka bata masa rai ba. Yana so ya ga ka kawo duk abin damuwanka masu sa ka ja baya na cikin zuciyarka domin ya canza su zuwa abubuwa ta daukaka masu kawo cin gaba.

Amma almajiran nan basu dago cewa Yesu ne ke tambayarsu ko mene ne su ke magana a kai ba, har sun amsa masa cewa “kai kadai kana bakonta chikin Urushalima, ba ka san al’amuran da suka faru a nan chikin wadannan kwanaki ba?” shi kadai ne ya SAN abin da ta faru! Kowa ya ga abin da ta faru cikin jiki, amma Yesu ya san yadda abu ta jiki, ta hadu da ta ruhaniya, shi ya san yadda abu ta ruhaniya ke canza yanayi ta duniya. Yesu ne kadai ya yi murna da abin “Bala’i” wadda ta faru a giciyarsa.

Wadannan almajirai sun furta zukatarasu a gaban wannan Bako wanda ya amsa masu cewa wahala tana bude hanya wa daukaka, ya kuma bayana masu ta wurin binciken Littafi Mai Tsarki yadda nufin Allah ke cikawa, a cikin abin da mu muke gani kamar bala’i ne kurum. Yesu yana marimarin ya yi haka a gareka! Yana marimarin ya bude idanunka ka gane shi a cikin lokacin da yanayi, ta yi maka duhu. Yana so ya sa zuciyarka ta komo a cikinka domin ya canza tsoronka, da alhakinka da fushinka zuwa bangaskiya, da bege, da kauna mai daukaka.

Allah ne kadai mai canza zuciyar mutum. Sai ta wurin zuwa garesa ne kadai akan iya sami tsabtacewa ta rai. Sai idan mun yi abin da wadannan almajirai na Imwasu suka yi ne tukuna za mu sami warkasuwa. Ba furta zuciyarmu kadai garesa zamu yi ba amma ya kamata mu yi tsit domin mu ji abin da zaya fada mana. Idan yanayi ta juya mana ta kuma zama baki kuma muna shakka domin abubuwa sun birkice, ya na cewa, “Ku kwantar da hankulanku, har wa yau Ina bisa kursiyina.” Abin da mu ke gani kamar bala’i ce a garemu, a wurinsa ba haka ba ne. A gare shi giciye ba bala’i ba ne. Ba mugayen mutane ba ne marasa hankali, ko da a ce muna ganinsu kamar haka a idanu ta nama da jini. Wannan ne al’amari mai ban mamaki na halin Allahnmu yana da girma sosai har domin haka yana iya juya muguntan mutane zuwa abin alheri wadda zai daukaka nufinsa a garemi. Ko da mene ne mutum zai yi a garemu, ba za ta hana cikawar nufin Allah ba. Ni ban san yadda Allah ke aikata wannan ba amma ina yabonsa da sujada a gareshi domin haka ta ke.

Ka tuna Yesufu da irin azabar da ya sha, duk wadannan azaban kuwa daga hannun maza da mata wadda ke kusa da shi. Me ya fada game da harkar rayuwarsa?” Ku dai, kuka nufe ni da mugunta; amma Allah ya nufi alheri (Farawa 50:20).” Yan’uwan Yusufu sun ciku da bakin ciki, amma Allah ya juya muguntansu domin ta cika nufinsa. Ka ga Allah shi ne kauna. Kauna ita ce ke mulkin duka duniya da sararin samaniya. Kauna kuma ta fi dukan irin makamai wanda za a taro a bisa kanta.


TAKAITAWA

“Masu - albarka ne masu-tsabtan zuciya, gama su za su ga Allah” Idan mun ga Allah a idanun zukatanmu a halitta, a kuma yadda ya ke a cikin dukan abubuwa, a cikin girman mu ta ruhaniya, a cikin al’amura (“Masu kyau” da “mara kyau”) kai, ko a cikin komai, zukatanmu na samun tsabtacewa da warkasuwa. Amma muna iya ganin Allah ta wurin wahayi ne kurum. Domin haka dole mu yi addu’a domin Allah ya bude idanunmu ta ruhaniya domin mu sami haskensa. Dole mu furta dukan zukatanmu a gareshi, mu kuma zama tsit domin mu ji amsarsa zuwa garemu. A cikin babi ta biyu za mu sami koyasuwa akan kaidodi wanda za su taimake mu mu gane muryarsa a sarari a cikin zukatanmu.


  1   2   3   4   5   6   7   8   9   10   11


Verilənlər bazası müəlliflik hüququ ilə müdafiə olunur ©atelim.com 2016
rəhbərliyinə müraciət